Search This Blog

Saturday, 13 January 2024

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa majalisar dattawan Kano

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa majalisar dattawan Kano (KEC) domin ta kasance mai ba da shawara ga gwamnatin jihar Kano.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Asabar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa Allah SWT ya albarkaci Kano da dimbin dattijai da tsofaffin shugabanni da suka kai ga kololuwar sana’o’insu kuma suka ci gaba da kasancewa cikin koshin lafiya.

Majalisar Dattawa ta kunshi tsofaffin Gwamnoni, Mataimakan Gwamnoni, Shugabannin Majalisar Dattawa, Shugabannin Majalisar Wakilai, Shugabannin Majalisar Jiha, Mataimakan Shugaban Majalisar, Alkalan Kotun Koli da suka yi ritaya, Alkalan Kotun daukaka kara da suka yi ritaya, tsofaffin alkalan jihar, tsofaffin alkalai. Sakatarorin Gwamnatin Jiha, da Tsoffin Shugabannin Ma’aikatan Jiha, wadanda dukkansu ‘yan asalin jihar ne.

Bugu da kari, majalisar ta hada da shugabannin Malamai, ‘yan kasuwa, sarakunan gargajiya, tsofaffin shugabannin hukumomin tsaro na jihar Kano, da sauran manyan dattawan da gwamnati za ta tantance tare da nada su.

Gwamnan ya jaddada cewa wadannan dattijai suna da tarin ilimi da hikima da gogewa, kuma da gangan gwamnatinsa za ta nemi yin amfani da kwarewarsu.

Haka kuma gwamnan ya ce nan ba da jimawa ba za a tantance ranar da za a kaddamar da majalisar.



Friday, 12 January 2024

GAME DA SHARI’AR ZABEN JIHAR KANO: ABINDA YAI SAURA - Saidu Ahmad Dukawa

Bismillahir Rahmanir Raheem
Yau, Juma’a 12/1/2024, Allah ya kawo karshen dakon da aka sha wajen sanin wanene halartaccen Gwamna a Jihar Kano. 

Ina zaton an dade al’umar Kano, da wadanda suka damu da halin da Kano take ciki a fadin Duniya, ba su shiga zulumi (tension) da fargaba (anxiety) kamar a wadannan watannin da aka gudanar da shari’u a mataki daban daban ba. Alhamdu lillah, Allah ya nunawa wadanda suke raye karshen dambarwar. Muna fatan kada Allah ya sake jarrabar Bayinsa da irin wannan halin.

Yanzu abu uku ne suka saurar mana. Abu na farko shine kowa ya karbi hukuncin da zuciya daya. Wandanda suka yi nasara kada su dauka iyawarsu ce, wadanda ba su samu yadda suke so ba kada su dauka wani ne ya janyo musu. Wannan ne zai taimaka wajen kaucewa irin wannan jarrabawar anan gaba.

Abu na biyu shine gawmanati da dukufa wajen samar da shugabanci nagari, ba tare da tunanin ramuwar gayya ba, ko wariya, ko wani abu mai kama da haka. Ya kamata a sani cewar gwargwadon yadda al’umma take da hadin kai gwargwadon yadda shugabanci zai yi sauki ya yi inganci. 

Abu na karshe shine yana da kyau ‘Yansiyasa su taimaki kansu da sauran al’umma su ragewa mutane shari’un zabe. Idan za a iya tunawa su kan hadu su saka hannu na alkawarin ba za su janyo tashin hankaili ba wajen yin zabe. To su kara da wasu alkawuran guda hudu, kamar haka:

1. Ba za su yi duk wani nau’i na magudi ba a harkar zabe

2. Ba za su yi amfani da ‘Yan Daba ba wajen tsorata mutane zuwa wajen zabe

3. Duk wanda aka ce ya fadi zabe ba zai je kotu neman a yi musu shari’a da wanda ya ci zabe ba; sannan

4. Wanda ya ci zabe ba zai tozarta wanda ya fadi ba, ta kowace hanya.

Ina kyautata zaton idan aka yi haka za a daina shari’un zabe, zai zama al’umma ne alkalai na koli a harkar zabe, kuma za su rika yanke hukunci ne a gindin akwatin zabe.

Amman fa na san fadar daban, aikatuwar daban. Don babu mamaki idan mafarki kawai nake yi.

Ko ma dai menene, Allah ya sa mu dace da shugabanci nagari.


Labari Da Dumiduminsa: Kotun Koli ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamnan Kano

Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Cikakken labarin zai zo muku nan gaba kadan 

Thursday, 11 January 2024

Mai Magana Da Yawun Gwamna Zulum Ya Rasu

Isa Gusau, mashawarci na musamman ga gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya rasu.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai ya rasu ranar Alhamis a kasar Indiya bayan rashin lafiya.

Mista Gusau, wanda tsohon dan jaridar Daily Trust ne, ya taba rike mukamin mai baiwa gwamnan jihar Borno Kashim Shettima shawara kan harkokin yada labarai na tsawon shekaru 8, kuma magajinsa ya sake nada shi a wannan mukamin.


Marigayin dan jaridar ya samu digirin digirgir a fannin yada labarai da hulda da jama'a  a jami'ar Leicester da ke Burtaniya.

Marigayin mai magana da yawun a cikin 2020 ya nemi izinin karatu na shekara guda don komawa Burtaniya don yin karatu, daga nan ne ya sa ido kan ayyukan watsa labarai na gwamnan.

Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Bukatar INEC Da Gwamnan Ogun A Shari’ar Zabe


Kotun koli ta karbi karar da Jam’iyyar PDP da dan takararta a zaben gwamnan Ogun, Ladi Adebutu, suka daukaka domin kalubalanar nasarar Gwamna Dapo Abiodun.

Kwamitin alkalai biyar na kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Inyang Okoro ya kuma ki sauraron karan da Jam’iyyar APC ta Gwamna Dapo Abiodun da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) suka daukaka daga bisani a kan lamarin.

yayin zaman na ranar Alhamis, kwamitin alkalan ya sanar da lauyan APC, Wole Olanipekun (SAN) cewa babban karar da aka daukaka a gaban kotun koli ya hade bukatarsu.

Adebutu da PDP suna neman Kotun Koli ta kwace kujerar Gwamna Abiodun, a bisa dalilin saba dokar zabe, magudi da kuma rashin cancantarsa.

Da yake gabatar da jawabinsa, lauyan Adebutu da PDP, Chris Uche (SAN) ya ce ya kamata INEC ta sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 99 da aka soke zabensu.

PDP da Adebutu suna kuma son Kotun Koli ta soke hukuncin kotun daukaka kara na ranar 23 ga watan Nuwamba, da ya tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe da ke tabbatar da nasarar Gwamna Adiodun.

Amma a martaninsa, lauyan INEC, Abiodun Owonikoko ya bukaci Kotun Kolin ta yi watsi da daukaka PDP da Adebutu.

A hukuncin kotun baya, alkalai biyu sun yi watsi da karar Adebutu da PDP saboda rashin dalili, amma Mai Shari’a Jane Esienanwan Inyang na ganin sabanin haka, inda ta umarci INEC da ta janye takardar shaidar cin zaben da ta ba wa Abiodun, ta da gudanar da sabon zabe a rumfunan 99 da ake takaddama akansu.

(AMINIYA)

Abin da Shekarau ya ce kan dakatar da Betta Edu


 Jagororin adawa a Najeriya na ci gaba da mayar da martani kan matakin shugaban kasar na dakatar da ministar ma'aikatar jin-kai da ake zargi da rashawa.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibahim Shekarau na cikin wadanda suka yaba wa shugaba Bola Tinubu duk da cewa wasu 'yan hamayyar na ganin matakin dakatar da ministar ya makara, ya kamata tun kafin naÉ—ata mukamin a tantance halinta.

Sai dai Malam Shekarau ya ce sun jinjinawa shugaba Tinubu, da yi wa gwamnatinsa fatan alkhairi. Saboda a ra'ayinsu duk wanda ya yi daidai ya kamata a yaba ma sa da karfafa masa gwiwa da bashi shawarar ci gaba da aikata hakan.

''Mun ga abubuwan da suka faru a baya, misali lokacin da ake zargin sakataren gwamnatin tarayya da aikata ba daidai ba, da cuwa-cuwar kudi da ayyuka, sai da aka yi watanni shida ba tare da an dakatar da shi ba, kuma har yanzu ba mu sake jin duriyar maganar ba. Dan haka wannan mataki da Tinubu ya dauka a bisa adalci abin da ya kamata ya yi kenan,'' in ji Shekarau.

Ya kara da cewa daman su 'yan adawa ne, amma bisa tarbiyyar addini ko ma wa ke shugabanci indai ya yi daidai to a fito a yaba masa kuma abin da suka yi kenan.

Shekarau ya ce; ''Mu na yi wa wannan gwamnatin kyakkyawan zato, domin ba ma yi wa shugaba fatan sharri, idan ka yi masa mummunan fata ya kasa to jama'a ne za su cutu.

Daman shi horo, ana yinsa domin ya tunatar da kuma nunawa masu niyyar yi kada su aikata, wannan matakin da aka dauka ba ga ministoci ba har duk wanda ke cikin gwamnati zai shiga taitayinsa, idan aka ce kyas ba za a kyale ba sai an bincika an kuma hukunta mai laifi.''

An dakatar da ministar ma'aikatar ayyukan jin kai ta Najeriya, Betta Edu bayan wata takaddama kan zargin ta ba da umarnin biyan sama da naira miliyan 585 cikin asusun ajiyar wani mutum, lamarin da ya saɓa da ƙa'idar aiki.

A cikin wata wasiƙa da aka yi zargin ministar ta sanya hannu, Betta ta umarci babbar akantar Najeriya, Oluwatoyin Madein ta zuba kuɗi cikin asusun wata mai suna Oniyelu Bridget, a matsayin tallafi ga ƙungiyoyin mutane masu rauni a jihohin Akwa Ibom da Cross River da Lagos da kuma Ogun.

Sai dai babbar akantar ta yi bayanin cewa, ko da yake ofishinta ya karɓi wannan buƙata daga ma'aikatar jin ƙai, amma bai yi abin da aka nema ba.

Tun daga lokacin ake ta kiraye-kirayen shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da ita daga aiki tare da bincike kan zargin almundahanar da dukiyar al'umma.

A kuma ranar 8 ga watan Junairun 2024 ne shugaban ya bada kai bori ya hau inda ya dakatar da Betta, ta kuma gurfana gaban hukumar EFCC domin amsa tambayoyi.

(BBC HAUSA)

CBN Ya Nada Sabbin Shugabannin Bankunan Union, Keystone Da Polaris

Sabbnin nada-naden sun fara aiki ne nan take


Babban Bankin Najeriya (CBN) ya nada sabbin shugabannin bankunan Union da Keystone da Polaris.

CBN ya nada sabbin shugabanni da manyan daraktocin bakunan ne sa’o’i kadan bayan ya sanar da rushe majalisar daraktoci da kwimitin gudanarwan bankunan.

Da take sanar da hakan a safiyar Alhamis, Daraktar yada labaran CBN, Hakama Sidi Ali, ta ce sabbin nade-naden sun fara aiki ne nan take.

Hakama Sidi Ali ta ce CBN ya nada Yetunde Oni a matsayin sabuwar Manajan Darakta kuma Shugabar Bankin Union, Mannir Ubali Ringim kuma Babban Daraktan Gudunarwa na bankin.

Bankin Keystone kuma, Hassan Imam shi ne sabon Manajan Darakta kuma Shugaba, tare da Chioma Mang a matsayin Babban Daraktan Gudunarwa.

A Bakin Polaris kuma, Lawal Mudathir Omokayode Akintola ne sabon shugaba kuma Manajan Darakta, Daraktan Gudunarwansa kuma Chris Ofikulu.

Babban Bankin ya sanar da sabbin nade-naden a ranar Alhamis ne washegarin da ya rushe kwamitocin daraktocin bankunan kasuwancin.
(AMINIYA)

Bom Ya Kashe Mutane 8, Wasu Dama Sun Jikkata A Borno

 


Akalla mutane takwas ne ake fargabar sun mutu sakamakon fashewar wasu bama-bamai a kan hanyar Ngala zuwa Dikwa a Karamar Hukumar Ngala a Jihar Borno.

Rahotannin sun nuna cewar, mutane da dama sun samu raunuka a sakamakon tashin bom din a kauyen Kinewba a ranar Talata.

Wata majiyar tsaro ta ce “Akalla Mutane  8 ne ake fargabar sun mutu, ciki har da yara biyu, sannan wasu da dama sun samu munanan raunuka sakamakon fashewar nakiyoyin.”

Majiyar ta ce fashewar bom din ya yi kaca-kaca da wasu motocin biyu yaddda ba za a iya gyara su ba.

Wata babbar majiya ta jami’an farin kaya na  JTF ta ce motocin biyu kirar Isuzu da wata babbar mota ce suka taka bom din kuma ana fargabar kashe kusan dukkan fasinjojin ciki.

“Wadannan motocin dai sun bar garin Ngala da misalin karfe 9 na safe, yayin da lamarin ya faru a nisan kilomita 15,” in ji majiyar.

Majiyarmu ya ruwaito cewa, tashin bama-baman ya faru ne a tazarar kilomita 15 daga Maiduguri, babban birnin jihar.

(AMINIYA)

Wednesday, 10 January 2024

Yanzu-Yanzu: Shugaba Bola Ahmed Tinubu Ya Nada Sababbin Shugabannin Hukumar NAHCON

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin sababbin 'yan hukumar gudanarwa na hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), har sai majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da hakan.


A sanarwar da mai taimakwa Shugaban kasar kan harkokin kafafen yada labarai, Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu, yace Shugaban a cikin kudurinsa na tabbatar da gudanar da aikin Hajji na shekarar 2024 ba tare da matsala ba, ya nada wadannan mutane a Hukumar NAHCON:

Jalal Arabi - Shgaba 

Aliu Abdulrazaq - Kwamishinan tsare-tsare, Ma'aikata, da Harkokin Kudi

Prince Anofi Elegushi - Kwamishinan Ayyuka

Professor Abubakar A. Yagawal - Kwamishinan Tsare-tsare & Bincike

Wakilan shiyya: 

Dr. Muhammad Umaru Ndagi — Arewa ta tsakiya

Abba Jato Kala — Arewa maso gabas 

Sheikh Muhammad Bin Othman - Arewa maso Yamma

Tajudeen Oladejo Abefe - Kudu maso Yamma

Aishat Obi Ahmed — Kudu maso Gabas

Zainab Musa – South South

Professor Musa Inuwa Fodio — Jama’atul Nasril Islam

Farfesa Adedimiji Mahfouz Adebola — Majalisar Koli kan Harkokin Musulunci

Shugaban ya umurci wadanda aka nada su sadaukar da kansu wajen ganin cewa ayyukan hukumar alhazai ta kasa sun kasance masu inganci da gaskiya da kuma biyan bukatun ‘yan Najeriya.


Shugaban NAHCON Ya Nemi A Sake Inganta Ayyukan Da Ake Yi Wa Alhazan Najeriya

A ziyarar da ya kai a jiya, 9 ga watan Janairu, 2024, a bankin ci gaban Musulunci, Shugaban Hukumar Hajji ta kasa, Malam Jalal Ahmad Arabi, ya nemi a karfafa alaka da bankin ci gaban Musulunci. 

A sanarwar da mataimakiyar daraktar harkokin hulda da jama'a da dab'i ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, tace shugaban ya mika godiyarsa ga Mataimakin Shugaban Ayyuka Dr Mansur Mukhtar, bisa tallafin fasaha da NAHCON ta samu a shekarar 2019 wanda ya taimaka wa dalibai da kafa tsarin ceton Alhazai da Cibiyar Hajji ta Najeriya. ( Karin bayani kan ziyarar bankin raya Musulunci za ta biyo baya).
 
Shugaban ya gabatar da bukatar daukar nauyin kwararrun ma’aikatan Najeriya irin su Likitocin dabbobi, ma’aikatan don bayar da ayyuka a lokacin aikin Hajji musamman a karkashin Hadaya. 

Haka kuma ya bukaci Bankin ya bude wa Najeriya kasuwa don fitar da dabbobin hadaya da sauransu.

Malam Jalal Ahmad Arabi a yau 10 ga watan Junairu 2024 ya ci gaba da leko tare da tantance wasu masu gudanar da ayyuka don shiga hidimar alhazan Najeriya a inda ya dace. Ya ziyarci sauran mahajjata’ Muttawif Establishments don nazarin ayyukan da ke cikin tsarinsu. 

Ma'aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta samar da dama ga kasashe don zabar Kamfanonin Mutawwif na Alhazai da suke so a matsayin hanyar karfafa hidimar Alhazai da ta dace. 
 
A baya shugaban ya tuntubi Dr Abdulrahman Bejawi, mataimakin ministan aikin hajji mai kula da aikin umrah da ziyara a Madina. A can, ya nemi jajircewa kan batutuwan da suka shafi jin dadin alhazan Najeriya da kare dukiyoyinsu. 

Haka kuma Malam Arabi ya yi na'am da aikin hanyar Makkah da mataimakin ministan ya bayar, Najeriya na daya daga cikin kasashe bakwai da suka bayar da ayyukan. A cewar Dr Bejawi, sama da kasashe 30 ne suka nuna sha'awar wannan shirin.
 
Malam Jalal Arabi ya rattaba hannu kan yarjejeniyoyin da aka kulla da Janar Car Syndicate, Ofishin Jakadancin United Agents da kuma Adillah Establishment of Madinah.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

SAPZ Kano partners ABCOAD to organize FFS Training for Youth and Women.

The Special Agro-Industrial Processing Zones (SAPZ) Programme, Kano State, in collaboration with Audu Bako College of Agricultur...