Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa majalisar dattawan Kano

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa majalisar dattawan Kano (KEC) domin ta kasance mai ba da shawara ga gwamnatin jihar Kano.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Asabar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa Allah SWT ya albarkaci Kano da dimbin dattijai da tsofaffin shugabanni da suka kai ga kololuwar sana’o’insu kuma suka ci gaba da kasancewa cikin koshin lafiya.

Majalisar Dattawa ta kunshi tsofaffin Gwamnoni, Mataimakan Gwamnoni, Shugabannin Majalisar Dattawa, Shugabannin Majalisar Wakilai, Shugabannin Majalisar Jiha, Mataimakan Shugaban Majalisar, Alkalan Kotun Koli da suka yi ritaya, Alkalan Kotun daukaka kara da suka yi ritaya, tsofaffin alkalan jihar, tsofaffin alkalai. Sakatarorin Gwamnatin Jiha, da Tsoffin Shugabannin Ma’aikatan Jiha, wadanda dukkansu ‘yan asalin jihar ne.

Bugu da kari, majalisar ta hada da shugabannin Malamai, ‘yan kasuwa, sarakunan gargajiya, tsofaffin shugabannin hukumomin tsaro na jihar Kano, da sauran manyan dattawan da gwamnati za ta tantance tare da nada su.

Gwamnan ya jaddada cewa wadannan dattijai suna da tarin ilimi da hikima da gogewa, kuma da gangan gwamnatinsa za ta nemi yin amfani da kwarewarsu.

Haka kuma gwamnan ya ce nan ba da jimawa ba za a tantance ranar da za a kaddamar da majalisar.



Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki