Abin da Shekarau ya ce kan dakatar da Betta Edu


 Jagororin adawa a Najeriya na ci gaba da mayar da martani kan matakin shugaban kasar na dakatar da ministar ma'aikatar jin-kai da ake zargi da rashawa.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibahim Shekarau na cikin wadanda suka yaba wa shugaba Bola Tinubu duk da cewa wasu 'yan hamayyar na ganin matakin dakatar da ministar ya makara, ya kamata tun kafin naÉ—ata mukamin a tantance halinta.

Sai dai Malam Shekarau ya ce sun jinjinawa shugaba Tinubu, da yi wa gwamnatinsa fatan alkhairi. Saboda a ra'ayinsu duk wanda ya yi daidai ya kamata a yaba ma sa da karfafa masa gwiwa da bashi shawarar ci gaba da aikata hakan.

''Mun ga abubuwan da suka faru a baya, misali lokacin da ake zargin sakataren gwamnatin tarayya da aikata ba daidai ba, da cuwa-cuwar kudi da ayyuka, sai da aka yi watanni shida ba tare da an dakatar da shi ba, kuma har yanzu ba mu sake jin duriyar maganar ba. Dan haka wannan mataki da Tinubu ya dauka a bisa adalci abin da ya kamata ya yi kenan,'' in ji Shekarau.

Ya kara da cewa daman su 'yan adawa ne, amma bisa tarbiyyar addini ko ma wa ke shugabanci indai ya yi daidai to a fito a yaba masa kuma abin da suka yi kenan.

Shekarau ya ce; ''Mu na yi wa wannan gwamnatin kyakkyawan zato, domin ba ma yi wa shugaba fatan sharri, idan ka yi masa mummunan fata ya kasa to jama'a ne za su cutu.

Daman shi horo, ana yinsa domin ya tunatar da kuma nunawa masu niyyar yi kada su aikata, wannan matakin da aka dauka ba ga ministoci ba har duk wanda ke cikin gwamnati zai shiga taitayinsa, idan aka ce kyas ba za a kyale ba sai an bincika an kuma hukunta mai laifi.''

An dakatar da ministar ma'aikatar ayyukan jin kai ta Najeriya, Betta Edu bayan wata takaddama kan zargin ta ba da umarnin biyan sama da naira miliyan 585 cikin asusun ajiyar wani mutum, lamarin da ya saɓa da ƙa'idar aiki.

A cikin wata wasiƙa da aka yi zargin ministar ta sanya hannu, Betta ta umarci babbar akantar Najeriya, Oluwatoyin Madein ta zuba kuɗi cikin asusun wata mai suna Oniyelu Bridget, a matsayin tallafi ga ƙungiyoyin mutane masu rauni a jihohin Akwa Ibom da Cross River da Lagos da kuma Ogun.

Sai dai babbar akantar ta yi bayanin cewa, ko da yake ofishinta ya karɓi wannan buƙata daga ma'aikatar jin ƙai, amma bai yi abin da aka nema ba.

Tun daga lokacin ake ta kiraye-kirayen shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da ita daga aiki tare da bincike kan zargin almundahanar da dukiyar al'umma.

A kuma ranar 8 ga watan Junairun 2024 ne shugaban ya bada kai bori ya hau inda ya dakatar da Betta, ta kuma gurfana gaban hukumar EFCC domin amsa tambayoyi.

(BBC HAUSA)

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki