GAME DA SHARI’AR ZABEN JIHAR KANO: ABINDA YAI SAURA - Saidu Ahmad Dukawa
Bismillahir Rahmanir Raheem
Yau, Juma’a 12/1/2024, Allah ya kawo karshen dakon da aka sha wajen sanin wanene halartaccen Gwamna a Jihar Kano.
Ina zaton an dade al’umar Kano, da wadanda suka damu da halin da Kano take ciki a fadin Duniya, ba su shiga zulumi (tension) da fargaba (anxiety) kamar a wadannan watannin da aka gudanar da shari’u a mataki daban daban ba. Alhamdu lillah, Allah ya nunawa wadanda suke raye karshen dambarwar. Muna fatan kada Allah ya sake jarrabar Bayinsa da irin wannan halin.
Yanzu abu uku ne suka saurar mana. Abu na farko shine kowa ya karbi hukuncin da zuciya daya. Wandanda suka yi nasara kada su dauka iyawarsu ce, wadanda ba su samu yadda suke so ba kada su dauka wani ne ya janyo musu. Wannan ne zai taimaka wajen kaucewa irin wannan jarrabawar anan gaba.
Abu na biyu shine gawmanati da dukufa wajen samar da shugabanci nagari, ba tare da tunanin ramuwar gayya ba, ko wariya, ko wani abu mai kama da haka. Ya kamata a sani cewar gwargwadon yadda al’umma take da hadin kai gwargwadon yadda shugabanci zai yi sauki ya yi inganci.
Abu na karshe shine yana da kyau ‘Yansiyasa su taimaki kansu da sauran al’umma su ragewa mutane shari’un zabe. Idan za a iya tunawa su kan hadu su saka hannu na alkawarin ba za su janyo tashin hankaili ba wajen yin zabe. To su kara da wasu alkawuran guda hudu, kamar haka:
1. Ba za su yi duk wani nau’i na magudi ba a harkar zabe
2. Ba za su yi amfani da ‘Yan Daba ba wajen tsorata mutane zuwa wajen zabe
3. Duk wanda aka ce ya fadi zabe ba zai je kotu neman a yi musu shari’a da wanda ya ci zabe ba; sannan
4. Wanda ya ci zabe ba zai tozarta wanda ya fadi ba, ta kowace hanya.
Ina kyautata zaton idan aka yi haka za a daina shari’un zabe, zai zama al’umma ne alkalai na koli a harkar zabe, kuma za su rika yanke hukunci ne a gindin akwatin zabe.
Amman fa na san fadar daban, aikatuwar daban. Don babu mamaki idan mafarki kawai nake yi.
Ko ma dai menene, Allah ya sa mu dace da shugabanci nagari.