Search This Blog

Thursday, 11 January 2024

Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Bukatar INEC Da Gwamnan Ogun A Shari’ar Zabe


Kotun koli ta karbi karar da Jam’iyyar PDP da dan takararta a zaben gwamnan Ogun, Ladi Adebutu, suka daukaka domin kalubalanar nasarar Gwamna Dapo Abiodun.

Kwamitin alkalai biyar na kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Inyang Okoro ya kuma ki sauraron karan da Jam’iyyar APC ta Gwamna Dapo Abiodun da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) suka daukaka daga bisani a kan lamarin.

A yayin zaman na ranar Alhamis, kwamitin alkalan ya sanar da lauyan APC, Wole Olanipekun (SAN) cewa babban karar da aka daukaka a gaban kotun koli ya hade bukatarsu.

Adebutu da PDP suna neman Kotun Koli ta kwace kujerar Gwamna Abiodun, a bisa dalilin saba dokar zabe, magudi da kuma rashin cancantarsa.

Da yake gabatar da jawabinsa, lauyan Adebutu da PDP, Chris Uche (SAN) ya ce ya kamata INEC ta sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 99 da aka soke zabensu.

PDP da Adebutu suna kuma son Kotun Koli ta soke hukuncin kotun daukaka kara na ranar 23 ga watan Nuwamba, da ya tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe da ke tabbatar da nasarar Gwamna Adiodun.

Amma a martaninsa, lauyan INEC, Abiodun Owonikoko ya bukaci Kotun Kolin ta yi watsi da daukaka PDP da Adebutu.

A hukuncin kotun baya, alkalai biyu sun yi watsi da karar Adebutu da PDP saboda rashin dalili, amma Mai Shari’a Jane Esienanwan Inyang na ganin sabanin haka, inda ta umarci INEC da ta janye takardar shaidar cin zaben da ta ba wa Abiodun, ta da gudanar da sabon zabe a rumfunan 99 da ake takaddama akansu.

(AMINIYA)

Abin da Shekarau ya ce kan dakatar da Betta Edu


 Jagororin adawa a Najeriya na ci gaba da mayar da martani kan matakin shugaban kasar na dakatar da ministar ma'aikatar jin-kai da ake zargi da rashawa.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibahim Shekarau na cikin wadanda suka yaba wa shugaba Bola Tinubu duk da cewa wasu 'yan hamayyar na ganin matakin dakatar da ministar ya makara, ya kamata tun kafin naɗata mukamin a tantance halinta.

Sai dai Malam Shekarau ya ce sun jinjinawa shugaba Tinubu, da yi wa gwamnatinsa fatan alkhairi. Saboda a ra'ayinsu duk wanda ya yi daidai ya kamata a yaba ma sa da karfafa masa gwiwa da bashi shawarar ci gaba da aikata hakan.

''Mun ga abubuwan da suka faru a baya, misali lokacin da ake zargin sakataren gwamnatin tarayya da aikata ba daidai ba, da cuwa-cuwar kudi da ayyuka, sai da aka yi watanni shida ba tare da an dakatar da shi ba, kuma har yanzu ba mu sake jin duriyar maganar ba. Dan haka wannan mataki da Tinubu ya dauka a bisa adalci abin da ya kamata ya yi kenan,'' in ji Shekarau.

Ya kara da cewa daman su 'yan adawa ne, amma bisa tarbiyyar addini ko ma wa ke shugabanci indai ya yi daidai to a fito a yaba masa kuma abin da suka yi kenan.

Shekarau ya ce; ''Mu na yi wa wannan gwamnatin kyakkyawan zato, domin ba ma yi wa shugaba fatan sharri, idan ka yi masa mummunan fata ya kasa to jama'a ne za su cutu.

Daman shi horo, ana yinsa domin ya tunatar da kuma nunawa masu niyyar yi kada su aikata, wannan matakin da aka dauka ba ga ministoci ba har duk wanda ke cikin gwamnati zai shiga taitayinsa, idan aka ce kyas ba za a kyale ba sai an bincika an kuma hukunta mai laifi.''

An dakatar da ministar ma'aikatar ayyukan jin kai ta Najeriya, Betta Edu bayan wata takaddama kan zargin ta ba da umarnin biyan sama da naira miliyan 585 cikin asusun ajiyar wani mutum, lamarin da ya saɓa da ƙa'idar aiki.

A cikin wata wasiƙa da aka yi zargin ministar ta sanya hannu, Betta ta umarci babbar akantar Najeriya, Oluwatoyin Madein ta zuba kuɗi cikin asusun wata mai suna Oniyelu Bridget, a matsayin tallafi ga ƙungiyoyin mutane masu rauni a jihohin Akwa Ibom da Cross River da Lagos da kuma Ogun.

Sai dai babbar akantar ta yi bayanin cewa, ko da yake ofishinta ya karɓi wannan buƙata daga ma'aikatar jin ƙai, amma bai yi abin da aka nema ba.

Tun daga lokacin ake ta kiraye-kirayen shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da ita daga aiki tare da bincike kan zargin almundahanar da dukiyar al'umma.

A kuma ranar 8 ga watan Junairun 2024 ne shugaban ya bada kai bori ya hau inda ya dakatar da Betta, ta kuma gurfana gaban hukumar EFCC domin amsa tambayoyi.

(BBC HAUSA)

CBN Ya Nada Sabbin Shugabannin Bankunan Union, Keystone Da Polaris

Sabbnin nada-naden sun fara aiki ne nan take


Babban Bankin Najeriya (CBN) ya nada sabbin shugabannin bankunan Union da Keystone da Polaris.

CBN ya nada sabbin shugabanni da manyan daraktocin bakunan ne sa’o’i kadan bayan ya sanar da rushe majalisar daraktoci da kwimitin gudanarwan bankunan.

Da take sanar da hakan a safiyar Alhamis, Daraktar yada labaran CBN, Hakama Sidi Ali, ta ce sabbin nade-naden sun fara aiki ne nan take.

Hakama Sidi Ali ta ce CBN ya nada Yetunde Oni a matsayin sabuwar Manajan Darakta kuma Shugabar Bankin Union, Mannir Ubali Ringim kuma Babban Daraktan Gudunarwa na bankin.

Bankin Keystone kuma, Hassan Imam shi ne sabon Manajan Darakta kuma Shugaba, tare da Chioma Mang a matsayin Babban Daraktan Gudunarwa.

A Bakin Polaris kuma, Lawal Mudathir Omokayode Akintola ne sabon shugaba kuma Manajan Darakta, Daraktan Gudunarwansa kuma Chris Ofikulu.

Babban Bankin ya sanar da sabbin nade-naden a ranar Alhamis ne washegarin da ya rushe kwamitocin daraktocin bankunan kasuwancin.
(AMINIYA)

Bom Ya Kashe Mutane 8, Wasu Dama Sun Jikkata A Borno

 


Akalla mutane takwas ne ake fargabar sun mutu sakamakon fashewar wasu bama-bamai a kan hanyar Ngala zuwa Dikwa a Karamar Hukumar Ngala a Jihar Borno.

Rahotannin sun nuna cewar, mutane da dama sun samu raunuka a sakamakon tashin bom din a kauyen Kinewba a ranar Talata.

Wata majiyar tsaro ta ce “Akalla Mutane  8 ne ake fargabar sun mutu, ciki har da yara biyu, sannan wasu da dama sun samu munanan raunuka sakamakon fashewar nakiyoyin.”

Majiyar ta ce fashewar bom din ya yi kaca-kaca da wasu motocin biyu yaddda ba za a iya gyara su ba.

Wata babbar majiya ta jami’an farin kaya na  JTF ta ce motocin biyu kirar Isuzu da wata babbar mota ce suka taka bom din kuma ana fargabar kashe kusan dukkan fasinjojin ciki.

“Wadannan motocin dai sun bar garin Ngala da misalin karfe 9 na safe, yayin da lamarin ya faru a nisan kilomita 15,” in ji majiyar.

Majiyarmu ya ruwaito cewa, tashin bama-baman ya faru ne a tazarar kilomita 15 daga Maiduguri, babban birnin jihar.

(AMINIYA)

Wednesday, 10 January 2024

Yanzu-Yanzu: Shugaba Bola Ahmed Tinubu Ya Nada Sababbin Shugabannin Hukumar NAHCON

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin sababbin 'yan hukumar gudanarwa na hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), har sai majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da hakan.


A sanarwar da mai taimakwa Shugaban kasar kan harkokin kafafen yada labarai, Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu, yace Shugaban a cikin kudurinsa na tabbatar da gudanar da aikin Hajji na shekarar 2024 ba tare da matsala ba, ya nada wadannan mutane a Hukumar NAHCON:

Jalal Arabi - Shgaba 

Aliu Abdulrazaq - Kwamishinan tsare-tsare, Ma'aikata, da Harkokin Kudi

Prince Anofi Elegushi - Kwamishinan Ayyuka

Professor Abubakar A. Yagawal - Kwamishinan Tsare-tsare & Bincike

Wakilan shiyya: 

Dr. Muhammad Umaru Ndagi — Arewa ta tsakiya

Abba Jato Kala — Arewa maso gabas 

Sheikh Muhammad Bin Othman - Arewa maso Yamma

Tajudeen Oladejo Abefe - Kudu maso Yamma

Aishat Obi Ahmed — Kudu maso Gabas

Zainab Musa – South South

Professor Musa Inuwa Fodio — Jama’atul Nasril Islam

Farfesa Adedimiji Mahfouz Adebola — Majalisar Koli kan Harkokin Musulunci

Shugaban ya umurci wadanda aka nada su sadaukar da kansu wajen ganin cewa ayyukan hukumar alhazai ta kasa sun kasance masu inganci da gaskiya da kuma biyan bukatun ‘yan Najeriya.


Shugaban NAHCON Ya Nemi A Sake Inganta Ayyukan Da Ake Yi Wa Alhazan Najeriya

A ziyarar da ya kai a jiya, 9 ga watan Janairu, 2024, a bankin ci gaban Musulunci, Shugaban Hukumar Hajji ta kasa, Malam Jalal Ahmad Arabi, ya nemi a karfafa alaka da bankin ci gaban Musulunci. 

A sanarwar da mataimakiyar daraktar harkokin hulda da jama'a da dab'i ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, tace shugaban ya mika godiyarsa ga Mataimakin Shugaban Ayyuka Dr Mansur Mukhtar, bisa tallafin fasaha da NAHCON ta samu a shekarar 2019 wanda ya taimaka wa dalibai da kafa tsarin ceton Alhazai da Cibiyar Hajji ta Najeriya. ( Karin bayani kan ziyarar bankin raya Musulunci za ta biyo baya).
 
Shugaban ya gabatar da bukatar daukar nauyin kwararrun ma’aikatan Najeriya irin su Likitocin dabbobi, ma’aikatan don bayar da ayyuka a lokacin aikin Hajji musamman a karkashin Hadaya. 

Haka kuma ya bukaci Bankin ya bude wa Najeriya kasuwa don fitar da dabbobin hadaya da sauransu.

Malam Jalal Ahmad Arabi a yau 10 ga watan Junairu 2024 ya ci gaba da leko tare da tantance wasu masu gudanar da ayyuka don shiga hidimar alhazan Najeriya a inda ya dace. Ya ziyarci sauran mahajjata’ Muttawif Establishments don nazarin ayyukan da ke cikin tsarinsu. 

Ma'aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta samar da dama ga kasashe don zabar Kamfanonin Mutawwif na Alhazai da suke so a matsayin hanyar karfafa hidimar Alhazai da ta dace. 
 
A baya shugaban ya tuntubi Dr Abdulrahman Bejawi, mataimakin ministan aikin hajji mai kula da aikin umrah da ziyara a Madina. A can, ya nemi jajircewa kan batutuwan da suka shafi jin dadin alhazan Najeriya da kare dukiyoyinsu. 

Haka kuma Malam Arabi ya yi na'am da aikin hanyar Makkah da mataimakin ministan ya bayar, Najeriya na daya daga cikin kasashe bakwai da suka bayar da ayyukan. A cewar Dr Bejawi, sama da kasashe 30 ne suka nuna sha'awar wannan shirin.
 
Malam Jalal Arabi ya rattaba hannu kan yarjejeniyoyin da aka kulla da Janar Car Syndicate, Ofishin Jakadancin United Agents da kuma Adillah Establishment of Madinah.

Gwamna Umar Namadi Ya Nada Sabon Darakta Janar Na Hukumar Alhazai Ta Jigawa

Gwamna Malam Umar A. Namadi ya amince da nadin Ahmed Umar Labbo a matsayin Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa na tsawon shekaru hudu.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Jigawa Malam Bala Ibrahim.

Sanarwar ta ce nadin Labbo a matsayin Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa an yi shi ne bisa cancanta

Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa, Ahmed Umar Labbo ya yi aiki a matsayin Darakta aiyuka na hukumar kuma an daukaka shi zuwa matsayin babban sakataren hukumar a ranar 20 ga Maris, 2023 bisa la’akari da kwarewarsa da kuma tarihin aikinsa.

“Saboda haka, muna fatan wanda aka nada zai tabbatar da amincewar da aka yi masa, ya kuma yi iya kokarinsa wajen ci gaban jihar Jigawa,” in ji SSG.

Sanarwar ta bayyana cewa, nadin zai fara aiki daga ranar 11 ga watan Janairu, 2024

Bakuwa Ta Sace Jariri Awa 3 Da Haihuwarsa A Asibiti

 Ana zargin bakuwa ta sace jaririn ne da hadin bakin ’yar uwar mai jegon


Wata mata ta sace jariri awa uku bayan haihuwarsa a Asibitin Kwararru na Dalhatu Arafat (DASH) da ke garin Lafia, Jihar Nasarawa.

Ana zargin bakuwar ta sace jaririn ne da hadin bakin ’yar uwar mai jegon sa’o’i kadan da haihuwarsa ta hanyar yi wa mahifiyarsa tiyata.

Aminiya ta gano bayan haihuwarsa da misalin karfe 3 na asubahin ranar Talata ne jami’an asibiti suka mika jaririn da mai jegon ga wata ’yar uwarta domin ta ci gaba da kula da su.

Wani ganau da ya nemi a boye sunasa ya ce, bayan sun dawo dakin masu jego ne ’yar uwar mai jegon ta kawo mata da wata bakuwa, wadda ake zargin sun hada baki wajen sace jaririn.

‘Kamar Layar Zana’

A cewarsa, “’yar uwar mai jegon ce ta ce mata za ta koma gida ta dauko cajar wayarta da ta manta; shi ne ta hada ta da wata mata da za ta zauna da su kafin ta dawo ,” wadda ake zargin ita ce ta sace jaririn.

Sace jaririn daga dakin masu jegon da misalin karfe 6 na safe,  awa uku da haihuwarsa ya jefa daukacin jami’ai da sauran mutanen asibitin cikin al’ajabi.

Wata ’yar uwar mai jegon da ta nemi a boye sunanta, ta tabbatar cewa, ’yar uwarsu ce kawo wa mai jegon wata bakuwa, ta kuma damka mata jaririn.

A cewarta, ba su yi aune ba, sai dai aka nemi jaririn da bakuwar — wadda ya yi zargin matsafiya ce — suka rasa, sun yi layar zana.

Ta ce, “Ba mu ga barauniyar jaririn ba, wannan wane irin rashin imani ne, mace ta shiga asibiti ta yaudari duk ’yan dakin da masu tsaron kofa cewa za ta yi masa wanka, amma ta tsere da jariri. Duniya ta zama abin tsoro!”

Yadda Aka Sace Jaririna —Mai Jego

Mai jegon, Malama Wasira Suleiman, wadda ke zubar da hawaye, ta ce “wadda aka kawo domin ta taimaka wajen kula da jaririn, ita ce ta sace jaririn da na dauka a cikina wata tara.”

Malama Wasira ta roki Gwamnatin Jihar Nasara da hukumar gudanarwar Asibitin DASH da hukumomin tsaro su taimaka su ceto jaririn nata ba tare da komai ya same shi ba.

Mahaifiyar jaririn ta bayyana cewa, “saboda ba ni da karfin da zan iya yi wa kaina komai” aka kawo matar a matsayin ’yar aike — idan mai jegon tana bukatar wani abu, ko sayen magunguan idan an bukaci hakan.

mma duk da haka matar ta nace cewa tana da kayan da za a lullube shi idan aka yi wankan, a karshe da mai jegon ta amince matar ta yi masa wanka, sai daga baya aka ce mata a sace jaririn nata.

“Wahalar da na sha na wata tara ba shi da misali, don haka babu abin da za a fada min da zan hakura; karfe biyun dare aka yi mini tiyata fa,” in ji mai jegon.

Bai Taba Faruwa Ba  —Hukumar Asibiti

Mukaddashin Shugaban Sashen Kula da Masu Juna Biyu na Asibitin DASH, Dalhatu Arafat ya bayyana takaicinsa kan lamarin yana mai cewa haka bai taba faruwa a asibitin ba.

A cewarsa, bayan an yi wa mai jegon aiki ta haihu da misalin karfe 3 na asubahin Talata aka kai ta dakin masu jego tare da mai kula da it.

Ita kuma ta kawo wata bakuwar da ba ta sani ba domin kula da su, za ta  je gida ta dauko wani bu.

“Abin takaici, bakuwar ta dauki jaririn da cewa za ta yi masa wanka, daga nan ta yi layar zana da shi, abin da mu a asibitin muka sani ke na,” in ji shi.

Amma ya ce duk wadanda ke da alaka da sace jaririn sun hannun ’yan sanda ana bincike domin gano bakuwar da ta sace jaririn.

Dalhayu Arafa ya ce, “sai da muka kira kowa, saboda wannan ne karo farko a haka ya faru a nan” kuma wadanda aka kama sun hada da ’yar uwar mai jegon da ta kawo bakuwar da wasu ma’aikatan asibitin da ke aiki a lokacin da abin ya faru.

Duk wanda aka samu da hannu za mu sallame shi mu mika shi ga hukuma, domin zama darasi ga masu irin wannan hali.

“Za kuma mu kara amfani da kyamarorin CCTV domin daukar duk wani motsi a cikin dakunan marasa lafiya,” in ji shi.

(AMINIYA)

EFCC Ta Kwace Fasfon Sadiya Da Betta Edu


Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ta kwace fasfo din tsohuwar Ministar aJin-kai, Betta Edu da magabaciyarta, Sadiya Umar-Farouq, kan binciken badakalar da ake yi a ma’aikatar.

Wata majiya mai tushe daga EFCC ta ce an kwace fasfo din Edu da da Sadiya ne domin hana su fita daga Najeriya yayin da ake ci gaba da binciken.

“Hukumar ta kwace fasfo din tsofaffin ministocin biyu, Sadiya Umar-Farouq da Betta Edu.

“Mun kuma kwace fasfo din Halima Shehu har sai an kammala bincike. Hukumar ba ta son yin kasadar ganin ko daya daga cikinsu ya fice daga Najeriya alhalin ana bincike a kan su,” in ji majiyar.

Dangane da binciken Edu da Sadiya Umar-Farouq, EFCC ta gayyaci shugabannin bankunan Zenith, Providus da Jaiz ofishinta a ranar Talata.

Ita ma Halima Shehu, wacce aka dakatar daga hukumar kula da harkokin zuba jari ta kasa, EFCC na bincike a kan ta.

Aminiya ta ruwaito cewa Edu ta isa hedikwatar EFCC da misalin karfe 10 na safiyar ranar Talata domin amsa tambayoyi kan zargin almundahanar kudi da ake mata.

Wannan na zuwa ne bayan fitar wata takarda da ta nuna cewa Edu ta bukaci babban Akanta-Janar na Tarayya ya biya Naira miliyan 585 da aka ware wa marasa galihu zuwa wani asusun banki na daban.

A nata bangaren kuma, Sadiya Umar-Farouq, tsohuwar minista a lokacin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ita ma EFCC ta gayyace ta domin amsa tambayoyi kam zargin da ake mata na sama da fadi da sama da biliyan 37.

(AMINIYA)



Monday, 8 January 2024

Labari Da Dumiduminsa: Shugaba Bola Ahmed Tinubu Ya Dakatar Da Ministar Harkokin Walwala Betta Edu

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya dakatar da ministar jin ƙai, Betta Edu nan take.

Kakakin shugaban Najeriyar, Ajuri Ngelale ne ya sanar da matakin dakatar da ministar cikin wata sanarwa da aka fitar a yau.

Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin ne domin ba da dama ga hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gudanar da bincike a kanta.

Tun farko al'ummar Najeriya sun yi ta matsa lamba inda suke kiraye-kiraye gwamnati ta dakatar da ita daga mukaminta domin a gudanar da cikakken bincike a kanta game da zarge-zargen da ake mata.

Ana zargin ta da bayar da umarnin tura kuɗi kimanin naira miliyan 585 zuwa asusun bankin wata mata.

(BBC HAUSA)

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Kano Business Community Endorses Gov. Yusuf for Second Term

The leadership of the Kano business community, comprising representatives of 25 major markets across the state, has endorsed Gov...