Search This Blog

Friday, 25 August 2023

Hukumar Kula Da Lafiya A Matakin Farko Ta Kano, Ta Ce Za Ta Yi Amfani Da Fasahar Sadarwa Wajen Bibiyar Kashe Kudadenta

Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Kano ta bayyana yin amfani da na’urorin fasahar sadarwa na zamani wajen bin diddigin ayyukan hukumar a kowane mataki.

Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Kano Dr. Muhammad Nasir Mahmoud ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wata manhaja mai suna Code Name Harmonized Finacial Tracking Tool wanda sashin fasahar sadarwa na hukumar ya samar.

A sanarwar da jami’in yada labarai na hukumar, Maikudi Muhammed Marafa ya sanyawa hannu, Dokta Nasir ya bayyana fatansa cewa, manhajar za ta samar da hanyar da za ta taimaka wa hukumar wajen bin diddigin duk wani tsarin tafiyar da harkokin kudi na hukumar.

Ya yabawa sashin fasahar sadarwar na hukumar bisa aikin  tare da bada tabbacin goyon bayansa kan sabbin abubuwa da zasu inganta ayyukan hukumar.

A nasa jawabin daraktan kudi na hukumar Malam Abubakar ya bayyana makasudin samar da manhajojin da ke da manufar tattarawa, tantancewa da kuma duba duk wata hada-hadar kudi daga duk hanyoyin samun kudade a matakin hukumar lafiya.

Daraktan ya ci gaba da bayanin cewa, manhajar za ta tabbatar da bin diddigin gaskiya da gaskiya a duk matakin da ake bukata, da kawo karshen ganin duk wata mu’amalar kudi ta cibiyoyin kiwon lafiya tare da inganta ritayar duk wani kashe kudi.

Hakazalika a cewar Darakta an tsara wannan manhaja ne domin sa ido da kuma yin armashin hada-hadar kudi na ’yan asusu, ’yan asusu na shiyyar, alkalan kananan hukumomi da kuma jami’in kula da cibiyoyin lafiya a karkashin hukumar kula da lafiya a matakin farko.


An Kawo Karshen Rashin Fahimtar Juna Tsakanin Ma'aikatar Al'adu Da Hukumar Tace Finafinai Ta Kano

A ranar Juma'a ne kwamishinan shari'a na Jahar Kano,  Barista Haruna Isah Dederi ya shirya wani taro irinsa na farko tsakanin kwamishinan raya al'adu da yawon rude ido ta Jahar Kano Hajiya ladidi Garko da Kuma Manajin Darakta na hukumar kula da masu yawon Bude ido Alh. Tukur Bala Sagagi tare da Shugaban Hukumar tace Fina-finai da Dab'i ta Jahar Kano Alh. Abba El-mustapha

Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Dab'i ta Jahar Kano, Abba El-Mustapha, Shi ne ya walllafa labarin a shafinsa na #Facebook 

El-Mustapha ya ce an shirya taron ne  domin nemo bakin zaren rashin fahimtar dake faruwa wajen gudanar da aiyukan daya rataya a tsakanin hukumomin biyu akan masu sana'ar gidajen kallo tare da masu gidajen shirya tarur-ruka (event centers). 

Tunda farko dai kwamishinan shari'ar na Jahar Kano Barista Haruna Isah Dederi yayi dogon jawabi dangane da hakki tare da aiyukan da rataya a kan dukkannin hukumomin biyu inda bayan doguwar tattaunawa tsakankanin shuwagabannin Hukumomin biyu aka sami daidaito dangane da shawarar da Shugaban Hukumar tace Fina-finai ta Jahar Kano Alh. Abba El-mustapha ya kawo na araba aiyukan gida biyu inda kowacce hukuma zata dauki daya danta maida hankali akan sa.

Hajiya Ladidi Garko ita ce kwamishiyar hukumar lura da al'adu tare da yawon bude ido ta Jahar kano a inda a madadin hukumar tayi na'am da hakan la'akari da hakan kwamishina shari'a na Jahar Kano Barista Haruna Isah Dederi ya tabbatar da bawa ko wacce hukumar aiki daya dan ta maida hankali akai domin cimma nasarar da gobnati tasa agaba

A yanzu haka dai, Hukumar tace Fina-finan da Dab'i ta Jahar Kano ita ce keda alhakin kula da aiyukan masu sana'ar gidajen kallo(Viewing Centers), Inda Hukumar kula da al'adu tare da masu yawon buda ido keda alhakin kula da aiyukan masu gidajen shirya tarur-ruka (Event centers).

Ana su jawabansu Daban-daban,  shuwagabannin sun nuna farin cikin su dangane da yadda ma'aikatar shari'ar ta kawo karshen takaddamar tare da samun nasarar da taron yayi na cimma matsaya 


Rashin Aikin Yi Ya Ragu Da Kaso 4.1 A Najeriya – Hukumar Kididdiga

Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce matsalar rashin aikin yi ta ragu da kaso 4.1 cikin 100 a watanni uku na farkon 2023.

Alkaluman rashin aikin yi dai sun kai kaso 33.3 cikin 100 a rahoton karshe da hukumar ta fitar ya zuwa karshen shekara ta 2020.
A cewar Babban Mai Kididdiga na Kasa, Semiyu Adediran, sun yi amfani da tsarin ICLS ne wajen yin kididdigar ta karshe. Taron masu kididdigar kwadago ta duniya ne ya kirkiro sikelin da aka yi amfani da shi a shekara ta 1982.

A baya dai hukumar ta ce za ta yi amfani da sabuwar hanya wajen kididdige ainihin yawan masu aikin yi da masu zaman kashe wando domin samun sahihan alkaluma a Najeriya.


A yayin da yake jawabi yayin kaddamar da sabuwar hanyar kididdigar a Abuja ranar Alhamis, Semiyu ya ce sabbin alkaluman sun sa kididdigar ta Najeriya ta zama iri daya da ta sauran ƙasashen duniya.

Ya ce an gudanar da ita ne da hadin gwiwar Bankin Duniya da Kungiyar Kwadago ta Duniya (ILO), kuma tuni ƙasashe 26 suka rungume ta a nahiyar Afirka.


Shugaban ya ce alkaluman, ya zuwa karshen shekarar da ta gabata sun tsaya ne a kan kaso 5.3 cikin 100, kafin su sauka a farkon wannan shekarar.
(AMINIYA)

Thursday, 24 August 2023

Gwamnan Kano Zai Biya Wa Daliban BUK 7,000 Kudin Makaranta

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin biya wa daliban da ke karatu a Jami’ar Bayero (BUK) kimanin su 7,000 ’yan asalin Jihar kudin makaranta.

Babban mai taimaka wa Gwamnan a kan harkokin kafafen sadarwa na zamani, Salisu Yahaya Hotoro, ne ya tabbatar da haka a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook da maraicen Laraba.


“Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin biya wa ɗaliban jihar Kano da ke karatu a BUK su kimanin dubu bakwai kuɗin makaranta,” kamar yadda ya wallafa.

Hakan na zuwa ne dai a daidai lokacin da daliban jami’ar ke ci gaba da kokawa da karin kudin da jami’ar ta yi.


A sakamakon karin, dalibai da dama sun rika neman gwamnati da masu hannu da shuni da su tallafa musu.

Hatta jami’ar ta Bayero sai da ta tsawaita wa’adin lokacin yin rajistar dalibai, kasancewar da dama daga cikinsu ba su iya kammalawa ba, saboda tsadar.

(AMINIYA)

Wednesday, 23 August 2023

Sunayen Unguwannin Da Wike Zai Yi Rusau A Abuja

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya amince a rusa gine-gine sama da 6,000 a yankunan Garki da Jabi da wasu unguwanni 28 da suka saɓa da tsarin birnin tarayyan ba.

Hukumar kula da birnin tarayyar (FCTA) ta fitar da jerin sunayen unguwannin, inda ta bayyana cewa gine-ginen ta riga aka sanya wa alama ne rusau din zai shafa, a shirin gwamnati na kawar da gine-ginen da aka yi ba bisa ƙa’ida ba a birnin.

Ga jerin unguwannin da abin zai shafa:

Apo Mechanic Village
Byanzhin.
Dawaki.
Dai Dai.
Durumi.
Dutse.
Garki.
Garki Village.
Gishiri.
Gwagwalada.
Idu.
Jabi.
Kauyen Kado.
Karmo.
Karshi.
Karu.
Katampe.
Kauyen Ketti.
Kpaduma.
Kabusa.
Kauyen Kpana.
Kubwa.
Lokogoma.
Lugbe.
Mabushi.
Mpape.
Nyanya.
Piya Kasa.
Jikwoyi
Galadima
Tun ranar Litinin da aka rantsar da tsohon gwamnan na jihar Ribas a matsayin Minista, ya sha alwashin dawo da birnin kan ainihin taswirarsa, ruguza gine-ginen aka yi ba bisa tsaru ba, da kuma kawo karshen badaƙalar filaye a babban birnin.

Wike wanda ya ce ya zaga birnin Abuja a cikin dare domin ya ga al’amura da kansa, ya koka bisa yadda aka yi gine-gine a filayen da gwamnati ta kebe ba don ginawa ba.

Ya ce: “Za mu kwace duk filayen da masu su ba su gina ba, don haka dole masu su su ci gaba da aiki nan take.

Sai dai daraktan sashen kula da ci gaban FCTA, Muktar Galadima ya ce za a gudanar da wani sabon bincike.

(AMINIYA) 



Hukumar Tace Finafinai Ta Rufe Sutudiyon Mawaki Ɗanzaki

Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa ita ce ta garƙame sutudiyon mawakin siyasar nan Idris Ɗanzaki tare da yin awon gaba da kayan aikinsa.

Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Abdullahi Lawan Sulaiman ya shaida wa ’yan jarida a Kano cewa hukumar ta ɗauki matakin ne bayan mawaƙin ya yi biris da gayyatar da ta yi mana na bayyana a ofisoshint

Ya ce tun ranar Asabar Hukumar ta nemi mawakin ya bayyana a ofisoshinta, amma har zuwa lokacin da muke kawo muku wannan labari bai amsa gayyatar ba.

“Kasancewar a yanzu zamani ya sawwake abubuwa mun yi amfani da waya inda muka kira wannan mawaki Idris Ɗanzaki inda kuma muka nemi ya zo wannan hukuma.

“Bayan sun kira ni a waya sun ce suna gayyata ta, na tura lauyana hukumar don ya wakilce ni.

“Amma me zai faru sai aka kira ni cewa wai hukumar ta rufe sutudiyona haka kuma ta kwashe wasu kayayyakin aikina.”

Abdullahi Lawan ya kara da cewa hakan ya sa Hukumar ta sa aka kulle sutudiyon tare da kwashe kayayyakin aikinsa.

Sai dai yayin da majiyarmu ta tuntubi mawaƙin ya tabbatar mata cewa hukumar ta gayyace shi amma ya tura lauyansa ya wakilce shi.

Mawakin ya yi iƙirarin cewa Hukumar ba ta sanar da shi laifin da take zargin sa da aikatawa ba.

Duk da cewa hukumar ba ta bayyana dalilin gayyatar mawakin ba, amma rahotanni sun nuna cewa ana zargin sa ne da yin munanan kalamai ga jagoran darikar Kwankwasiyya Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso a cikin wata waka da ya yi a kwanan baya.
(AMINIYA)





Birtaniya Ta Gurfanar Da Diezani A Gaban Kotu Kan Zargin Almundahana

Kasar Birtaniya ta gurfanar da tsohuwar Ministar Man Fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke a gaban kotu kan zargin rashawa lokacin da take Minista.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa ’yan sandar kasar sun ce sun maka ta a kotun ne saboda suna zargin ta karbi cin hanci a wasu kwangilolin man fetur da iskar gas.

Diezani, mai shekara 63 a duniya, na daya daga cikin kusoshi a gwamnatin tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan.

A zamanin mulkin tsohon Shugaban, Diezani ta rike mukamin Ministar Mai ta Najeriya daga 2010 zuwa 2015, sannan ta rike matsayin shugabar Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur ta Duniya (OPEC).


A cewar Shugaban Hukumar Yaki da Laifuffuka ta Birtaniya (NCA), Andy Kelly, “gurfanarwar da aka yi wa Diezani wata somin-tabi ce na wani zuzzurfan bincike na kasa da kasa da aka dade ana yi.”

Hukumar dai ta ce ana zargin Diezani da karbar akalla tsabar kudi har Fam din Ingila 100,000 da wasu motoci da hawa jirgin da ba na ’yan kasuwa ba, yin hutun kece raini ita da iyalanta da kuma yin amfani da gidaje masu yawa a birnin Landan.

An kuma zarge ta da nuku-nuku kan wasu kadarori masu tsada da ta mallaka da suka hada da kayan ɗaki da biyan kudin makarantar ‘ya’yanta da kuma wasu sarkoki da kayan ado.
(AMINIYA)

Monday, 21 August 2023

Cancanta Muka Duba Wajen Zaɓo Ministoci — Tinubu

Shugaban Bola Ahmed Tinubu ya ce cancanta ce ta yi tasiri wajen zaɓo ministocinsa da aka rantsar a yau domin su taimaka wajen tafiyar da lamurran ƙasar.

Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne a lokacin da ya yi jawabi bayan rantsar da sabbin ministoci a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

“Ƴan Najeriya na sa ran za ku yi aiki mai inganci kuma za ku sauke nauyin da aka ɗora muku,” in ji Tinubu.

Ya ƙara da cewa “Dole ne ku yi aikin da zai sanya ƴan Najeriya su sake amincewa da gwamnati.”


Ya bayyana cewa akwai babban nauyi a kan sabbin ministoci ganin irin manyan alƙawurran da gwamnatinsa ta ɗauka.

Shugaban ya kuma buƙaci sabbin ministocin da su yi aiki ba tare da nuna banbanci ba, inda ya ce: ”An ba ku wannan matsayi ne ba domin ɓangaren da kuka fito ku jihonhinku ba, sai dai domin ƙasa baki ɗaya.”
(AMINIYA)

Hukumar 'yan Sanda Ta Kano Ta Haramta Dukkanin Wata Zanga-zanga A Titina

SANARWA

SANARWA TA GAGGAWA GA JAMA'A DAGA HUKUMAR YAN SANDA NA JIHAR KANO!! HANA ZANGA-ZANGAR KAN TITI A JIHAR KANO

 

Bisa la'akari da samfuran bayanan sirri da ke hannun wannan rundunar 'yan sanda, an haramta duk wani nau'i na zanga-zangar tituna a duk sassan jihar.

Don haka jama’a ku lura cewa ya zo mana da cewa a halin yanzu jam’iyyar APC da NNPP suna ta tara jama’a na haya da sunan jam’iyyar Civil Society Coalition, ba tare da izini daga shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya ba, ba tare da amincewar su ba. daga hukumomin tsaro a jihar. Dukkan masu shirya taron, da na kungiyar, ya kamata su lura cewa duk wani yunkuri na rashin mutunta NLC da Hukumomin tsaro a jihar, ta hanyar yin wasa da tabarbarewar yanayin tsaro, wanda hadin gwiwar hukumomin tsaro ke gudanarwa, ba wai kawai rashin wayewa ba ne, laifi ne kawai. 

Har ila yau, wani laifi da ya shafi Tsaron Kasa 3. Ya zuwa yanzu dai wannan jami’an ‘yan sanda na gudanar da bincike kuma ya nuna cewa wasu ‘yan jam’iyyun biyu da ke jan hankalin ‘ya’yan kungiyoyin farar hula da su shiga wannan matakin na su ne kawai sakamakon kama su. da kuma yin watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe.
 

A karshe, wannan rundunar ‘yan sanda tana godiya da dimbin goyon baya da hadin kai da take samu daga mutanen kirki.

Jihar don zaman lafiya, tsaro, kwanciyar hankali, da muradun duk mazauna.


Na gode muku
SANARWA: CP MOHAMMED USAINI GUMEL, FIPMA, pse KWAMISHINAN YAN SANDA NA JAHAR KANO. 21 GA AGUSTA, 2023.

Sunday, 20 August 2023

Sai Nan Da Shekara 3 Za Mu Sauka Daga Mulki – Gwamnatin Sojin Nijar


Shugaban mulkin soji na Jamhuriyar Nijar, Janar Abdulrahmane Tchiani, ya ce za su ci gaba da tafiyar da gwamnatin rikon kwarya har sai nan da shekara uku kafin su mika mulki ga farar hula. 

 Ya kuma gargadin cewa duk wanda ya kuskura ya kaddamar da kai wa kasarsa hari sai ya yi da-na-sani. 

A cikin wani jawabinsa da aka watsa ta kafar talabijin din kasar a ranar Asabar, Tchi ani ya ce, 

 “Babban burinmu shi ne mu kwace mulki, kuma duk wanda ya sake ya kai mana hari zai gane shayi ruwa ne.” Gargadin nasa na zuwa ne kwana ɗaya bayan dakarun Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), sun ce a shirye suke su kutsa kai Nijar domin su dawo da mulkin Dimokuraɗiyya a Nijar. 

 A cikin jawabin mai tsawon minti 12, Tchiani ya kuma ce, “Muna sanar da kafa wani kwamitin tattaunawa na kasa da zai fito da nagartattun hanyoyin samar da sabon Kundin Tsarin Mulki.” 

 Kazalika, ya yi jawabin ne jim kadan bayan tawagar ECOWAS karkashin tsohon Shugaban Najeriya, Abdulsalami Abubakar, ta gudanar da tattaunawa domin warware rikicin siyasar kasar a birnin Yamai. Tawagar ta kuma sami ganawa da hambararren Shugaban na Nijar, Mohammed Bazoum.

AMINIYA

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

SAPZ Kano partners ABCOAD to organize FFS Training for Youth and Women.

The Special Agro-Industrial Processing Zones (SAPZ) Programme, Kano State, in collaboration with Audu Bako College of Agricultur...