Search This Blog

Wednesday, 5 April 2023

Kujerar Dan Majalisa: Ban Gamsu Da Nasarar NNPP Ba, Zan Tafi Kotu – Dan Ganduje


 Umar Abdullahi Gandujedan Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, wanda ya tsaya takarar dan Majalisar Wakilai a jam’iyyar APC, ya ce bai yarda da sakamakon zaben da ya ba NNPP nasara ba.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) dai ta ayyana Injiniya Tijjani Abdulkadir Jobe a matsayin wanda ya lashe kujerar dan majalisar a mazabar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado, a jam’iyyar NNPP.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa, Tuni dai Umar, wanda aka fi sani da Abba Ganduje ya maka Tijjani Jobe a gaban kotun sauraron kararrakin zabe.

Abba, ta bakin lauyansa, Barista A.T Falola, ya kuma kalubalanci INEC kan ayyana Jobe a matsayin dan takarar da ya samu rinjayen kuri’un da aka kada a lokacin zaben.

Da ya ke gabatar da kara a gaban kotun, Falola ya roki kotun da ta gudanar da shari’ar a kan Jobe da kuma jam’iyarsa ta NNPP mai sakatariya a unguwar Sharada a Kano

Bukukuwan Easter: Gwamnati Ta Ayyana Juma’a Da Litinin A Matsayin Ranakun Hutu

 


Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Juma’a da Litinin, 7 da 10 ga watan Afrilu a matsayin hutu albarkacin bukukuwan Easter da Kiristoci za su yi a fadin Najeriya.

Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren ma’aikatar, Shuaib Belgore, ya fitar a Abuja ranar Laraba.

Ya bukaci mabiya addinin na Kirista da su yi amfani da lokacin wajen kwaikwayon halayen sadaukarwa, kaunar juna, yafiya, soyayya, hakuri da zaman lafiya da Annabi Isah (A.S) ya koyar.

Ministan ya kuma bukace su da su yi amfani da lokacin wajen yi wa Najeriya addu’o’i na musamman saboda kalubalen tsaron da take fama da su.

“Tsaro sha’ani ne da ya shafi kowa. Saboda haka, nake kira ga ’yan Najeriya da ma ’yan kasar waje mazauna kasarmu da su ci gaba da nuna halin kishin kasa ta hanyar taimaka wa jami’an tsaro wajen dawo da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan kasa,” in ji shi.

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnati na yin duk kokarinta wajen ganin an mika mulki lami lafiya bayan kammala zaben sabuwar gwamnati.

AMINIYA

Tuesday, 4 April 2023

An Kama Donald Trump Kan Zargin Aikata Laifuka

An kama Tsohon Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump kan zargin aikata laifuka.

An kama shi ne ranar Talata yayin da aka gurfanar da shi a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta Manhattan.

An tsare ‘yan sandan da suka yi sanadin mutuwar matashi a Filato
’Yan bindiga sun yi garkuwa da matar Dagaci da danta a Kano
Ana zargin tsohon shugaban ne da biyan wata mai fina-finan batsa, Stormy Daniels toshiyar baki don kada ta yi bayani game da alakar nema a tsakaninsu lokacin da yake takarar shugaban kasa a zaben 2016.

Shi ne tsohon shugaban Amurka na farko da aka taba kamawa a tarihin kasar.

To sai dai, a lokuta da dama Trump ya musanta zargin.

Sai dai Trump ya ce duk wadanan tuhume-tuhumen da ake masa ba komai ba ne face yi wa takararsa ta neman wa’adi na biyu zagon kasa.
AMINIYA 

Yadda masu son muƙamin shugaban majalisa ke sayen ƙuri'un sanatoci - Ndume

 


A Najeriya bayan kammala zaɓukan ƙasar a yanzu hankali ya karkata kan shugabancin zaurukan majalisun dokoki.

Tuni dai wasu 'yan majalisun da ke son ɗarewa kujerun shugabancin majalisun suka fara bayyana sha'awarsu ta hanyar kamun ƙafa a wajen masu ruwa da tsaki na jam'iyyunsu da kuma zaɓaɓɓun 'yan majalisar.

Sai a watan Yuni mai zuwa ne za a ƙaddamar da majalisar dokokin ta goma, daga nan kuma a fara shirye-shiryen zaɓen shugabannin majalisun.

To sai dai wasu 'yan majalisun sun fara zargin cewa ana amfani da kuɗi wajen sayen bakin 'yan majalisun domin zaɓen wasu a matsayin shugabannin majalisun.

Sanata Ali Ndume ɗan majalisar dattawa ne daga jihar Borno ya kuma shaida wa BBC cewa akwai zargin da ake yi na cewa wasu na amfani da kuɗi wajen ganin sun samu ɗarewar kujerar shugaban majalisar dattawa.

Ya ce a yanzu siyasar ƙasar masu hannu da shuni, ko masu kuɗi su ne ke juya ɓangaren siyasar ƙasar.

''Dandalin siyasarmu ya cika da irin waɗannan mutanen da suke ganin za su iya sayen komai suke so da kuɗi'' in ji Sanata Ndume.

Dan majalisar dattawan ya ce a baya ana maganar cewa ana sayen ƙuri'ar talaka, matakin har ya kai ga talakawan ƙasar suna ganin komai nasu na sayarwa ne a ɓangaren zaɓen ƙasar.

'A yanzu har ƙuri'ar sanata ake saya'

Majalisar Dattawa

ASALIN HOTON,NIGERIAN SENATE

Dan majalisar dattawan ya ce matakin ya kai a yanzu har ƙuri'ar sanata ma ana so a saya.

Ya yi zargin cewa a yanzu masu son ɗarewa kujerar shugabancin majalisar dattawan sun fara sayen ƙuri'un sanatoci.

''Akwai sanatocin da suke bai wa 'yan majalisar dattawa kuɗi a kan suna so su nemi shugabancin majalisar'' In ji Ali Ndume.

Ali Ndume ya ce bayan kwarewa a majalisar, idan mutum yana da kuɗi to damar da yake da ita ta zama shugaban majalisar ta fi yawa.

Sanatan ya kuma yi zargin cewa a yanzu akwai sanatocin da ba su da kwarewa a aikin majalisar, amma suna son mukamin shugaban majalisar dattijai.

''Amma saboda suna da kuɗi, amma yanzu suna son ɗarewa shugabancin majalisar, kawai saboda suna da kuɗi''.

'Kamun ƙafa da kuɗi a maimakon cancanta'

Ali Ndume

ASALIN HOTON,SANATA ALI NDUME/FACEBOOK

Dan majalisar ya kuma yi zargin cewa ba kawai sanatocin masu muradin shugabancin majalisar ke saya ba, har da sauran hukumomi.

''A yanzu duk abinda kuɗi bai baka ba a Najeriya to sai in kuɗin ne ya gaza, kuma idan ka ƙara za ka samu'', in ji Ndume.

Dan majalisar ya ce abu biyu ne a yanzu suke yin tasiri wajen samun shugabancin majlisar wato da kamun ƙafa da kuma kuɗi, maimakon cancanta.

Sanata Ndume ya kuma yi ƙorafin cewar a yanzu maimakon ya mayar da hankali kan cancanta domin zaɓen shugaban majalisar, an mayar da hankali wajen kamun ƙafa da kuma bayar da kuɗi.

'Ya kamata a bi cancanta maimakon tsarin shiyya-shiyya'

Sanata Ali Ndume ya kuma ce bai ga dalilin da zai sa a bi tsarin shiyya-shiyya a shugabancin majalisar dattawan ƙasar ba, a cewarsa kamata ya yi a bi cancanta.

''A lokacin babban zaɓe na yadda da batun shiyya-shiyya, amma a zaɓen da za a yi tsakanin waɗanda sun riga sun ci zaɓe ban goyi bayan shiyya ba'', in ji shi.

A cewar ɗan majalisar bin tsarin shiyya-shiyya zai haifar da samun shugabannin majalisar waɗanda ba su cancanta ba.

''Akwai wasu fa a majalisar nan waɗanda suna da tabo na laifi, sannan a matayinmu na dattawa, kuma a ce an sa mana shugaba wanda ba dattijo ba''?, a cewarsa.

Ya ce kamata ya yi a bar mambobin majalisar da kansu, su zaɓi wanda suke ganin ya cancanta.

Kujerun shugaban majalisar dattawa da ta kakakin majalisar wakilan Najeriya na da matuƙar muhimmanci da tasiri a siyasar Najeriya.

BBC

Gwamnatin Najeriya Na Zargin Peter Obi Da Cin Amanar Kasa

 


Gwamnatin Tarayya ta shawarci dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar LP a zaben da ya gabata, Peter Obi, da ya guji tunzura jama’a su tayar da zaune tsaye kan sakamakon zaben da ya gabata.

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayar da shawarar yayin wata tattaunawarsa da kafafen yada labarai a birnin Washington DC na Amurka.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Ministan ya je Amurka ne don tattaunawa da kafofin kan abubuwan da suka wakana yayin zaben da ya gabata a Najeriya.

NAN ya ce ya zuwa yanzu, Ministan ya tattauna da jaridar Washington Post da Muryar Amurka da mujallar Foreign Policy da kuma kamfanin dillancin labarai na AP.

Lai Mohammed ya kuma gargadi Peter Obi da cewa ba daidai ba ne ya rika neman hakkinsa a kotu, sannan kuma ya rika kokarin tayar da zaune tsaye a daya bangaren.

“Obi da Mataimakinsa Datti, bai kamata su rika yi wa zababben Shugaban Najeriya, Bola Tinubu na APC barazana cewa muddin aka rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa, Dimokuradiyya ta kare a Najeriya.

“Wannan cin amanar kasa ne. Neman tayar da zaune tsaye ne. Kuma abin da suke kokarin yi ke nan.

“Kalaman Obi dan ko a mutu ko a yi rai ne, bai mai son Dimokuradiyyar da yake ikirari ba ne shi, saboda mai sonta bai kamata ya yi amanna da ita kawai lokacin da ya lashe zabe ba,” in ji Ministan.

Monday, 3 April 2023

Gwamnatin Kano ta nada Oba Balogun Da Farfesa Jega, Shugaba Da Uban Jami’ar Sa’adatu Rimi

Majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da nadin Oba Dr. Sanata Moshood Olalekan Ishola Balogun Aliiwo da Farfesa Attahiru Jega, tsohon mataimakin shugaban jami’ar Bayero kuma tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa a matsayin Shugaban da Uban majalisar gudanarwar Jami'ar Ilimi ta Sa'adatu

Hakan ya biyo bayan samun amincewa ne daga Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa (NUC), wacce ta amince da ita a matsayin jami’ar Jiha ta 61 daga cikin jami'o'in guda 222 a tsarin jami’o’in Najeriya.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya bayyana haka bayan taron majalisar da aka gudanar a zauren majalisar da ke gidan gwamnatin Kano ya bayyana sauran mambobin majalisar da suka hada da Dr. Muhammad Adamu Kwankwaso, Hajiya Zulaiha UM Ahmed, Dr. Ibrahim Yakubu Wunti, Dr. Halima Muhammad da Alhaji Sabi'u Bako.
 
Ya ce nadin ya zo daidai da sashe na uku na 22 na dokar Jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi ta Kumbotso wadda ta ce “za a yi majalisar da za ta zama hukumar gudanarwar jami’ar”, yayin da sashi na 1, 2 da 3. A cikin jadawalin na biyu na dokar ya tanadi cewa “bako, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai nada Chancellor, Pro Chancellor/Chairman of the Council da kuma na waje na majalisar.”
 
Malam Garba ya kara da cewa kamar yadda sashe na 3(2) na jaddawali na biyu, Pro Chancellor da sauran Yan majalisar gudanarwar Jami'ar za su ci gaba da rike mukaman na tsawon shekaru 4, wanda za a sabunta su na biyu kuma na karshe na wasu shekaru hudu.

A halin da ake ciki, bisa tsarin doka sashi na 5 da na biyu, majalisar ta baiwa maziyartan, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin sabuwar jami’a a karon farko, amincewar nada manyan jami’ai da masu ziyarar Jami'ar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya nada. Ganduje, wanda shi ne zai jagoranci tafiyar da jami’ar.

Ya ce wadanda aka nada sune Farfesa Isa Yahaya Bunkure, Provost Sa’adatu Rimi College of Education (SRCOE), Kumbotso, mataimakin shugaban jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi; Dr. Kabiru Ahmad Gwarzo, mataimakin shugaban mai lura da harkokin koyarwa,  mataimakin shugaban jami’ar mai lura da harkokin mulki ; Dr. Miswaru Bello,  Saminu Bello Zubairu, a matsayin Maga takarda, Ibrahim Muhammad Yahaya, Bursar, SRCOE, Kumbotso, Mai Lura Da Harkokin kudi da kuma Mabruka Abubakar Abba a matsayin shugabar sashen lura da dakin karatu na jami'ar 

Kwamishinan ya bayyana cewa, yayin da nadin mataimakin shugaban jami’ar, magatakarda, mai kula da harkokin kudi da kuma mai lura da dakin karatu na tsawon shekaru biyar ne, mataimakin mataimakin shugaban jami’ar a fannin koyarwa, da na fannin mulki tsawon shekaru hudu kowannensu

Sunday, 2 April 2023

Zababben Gwamnan Kano Ya Nada Mai Lura Da Harkokin Karbar Bakinsa

Zababben Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Abdullahi Ibrahim Rogo a matsayin babban mai lura da harkokin Karbar bakin sa na lokacin mika mulki.

Wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin mika mulki na jihar Kano 2023 NNPP Sanata Dr. Abdullahi Baffa Bichi ta nuna cewa nadin zai fara aiki nan take har zuwa ranar 29 ga watan Mayu 2023.

Sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na Zababben Gwamnan Jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce nadin nasa ya samo asali ne a bisa tarihi da jajircewarsa da kuma biyayyarsa daga 2019 zuwa 2023.

Hon. Rogo ya kammala karatun kimiyyar siyasa a jami'ar Abuja. Ya yi wasu guraben karatu da suka hada da karatun Difuloma daban-daban 

Sabon mai jami'in kula da harkokin Karbar bakin da aka nada ya rike mukaman siyasa da dama kamar Sakatare, Kwamitin riko na rusasshiyar jam’iyyar ANPP na karamar hukumar Dawakin Kudu, mai ba shugaban karamar hukumar shawara ta musamman kan harkokin filaye, sakataren karamar hukumar Rogo, shugaban kwamitin riko, karamar hukumar Rogo da kuma shugaban karamar hukumar Rogo. Dan Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Har zuwa nadin nasa, Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo shi ne Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar NNPP reshen Jihar Kano.

Yanzu-Yanzu : Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Mika Mulki Mai Dauke Da Mutum 17

Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da kafa kwamitin mika mulki mai mambobi 17 domin mika mulki ga gwamnati mai jiran gado a jihar.

Majalisar ta kuma amince da wani karamin kwamiti mai mutum 100 wanda za a fitar da kundin tsarin kunshinsa daga ma’aikatu da ma’aikatu da hukumomi daban-daban (MDAs).

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya tabbatar da wannan batu a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan sakamakon taron majalisar na mako-mako da aka gudanar a zauren majalisar da ke gidan gwamnatin jihar Kano, ya ce ana sa ran zababben gwamnan zai ba da wakilai uku a babban kwamitin.

Ya ce kwamitin wanda ke karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jiha Alhaji Usman Alhaji yana da wadannan mambobi a matsayin shugaban ma’aikatan gwamnati, babban lauya/kwamishanan shari’a, kwamishinan yada labarai, kwamishinan muhalli, kwamishinan kasuwanci. , Masana'antu da Haɗin kai.

Sauran sun hada da kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi, kwamishinan kananan hukumomi, kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa, kwamishinan kudi, kwamishinan ilimi, darakta-janar, ofishin kula da filaye, darakta-janar, bincike da takardu, Manajan Darakta na hukumar tsara Birane da sauransu. Hukumar Raya Kasa, yayin da Babban Sakatare, Binciken Bincike da Harkokin Siyasa, REPA za ta zama sakatariyar kwamitin.

Malam Garba ya bayyana cewa, babban kwamatin zai yi aiki cikin jituwa da nufin rubutawa tare da mika rahoton mika mulki na karshe cikin makonni uku.

Kwamishinan ya bayyana cewa an ba wa babban kwamitin rikon kwarya umarnin fara shirin mika mulki tare da rubuta nasarorin da aka samu a cikin wa’adin mulki biyu na gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Ya ce kwamitin zai kuma samu tare da tantance rahotanni daga ma'aikatu da sassan gwamnati ta fuskar manyan ayyuka

Saturday, 1 April 2023

Lawan Majakura: Mai Sayar Da Kifi Da Ya Kada Shugaban Majalisar Yobe

 


A zaben Gwamna da na ’yan majalisar jiha da aka gudanar a ranar Asabar 18 ga Maris ne Lawan Musa Majakura mai shekara 33, ya kayar da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Alhaji Ahmed Mirwa Lawan da kuri’a 182 don wakiltar Mazabar Nguru II a Karamar Hukumar Nguru a Jihar Yobe.

Majiyarmu ta tattauna da zababben dan majalisar na Jam’iyyar PDP ta waya, inda ya yi bayani kan takaitaccen tarihi da harkokin siyasarsa da yadda ya samu nasarar da ta yi waje da Shugaban Majalisar:

Mene ne takaitaccen tarihinka?

An haife ni a garin Majakura da ke Karamar Hukumar Nguru a watan Janairun 1990. Na yi karatun firamare a Majakura.

Daga nan na wuce Kwalejin Gwamnati da ke Nguru, inda na samu karamar Diploma a Nazarin Addinin Musulunci.

Daga nan na tafi Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Tarayya da ke Damaturu, inda na kammala a shekarar 2009 tare da samun takardar Babbar Diploma (HND) a fannin kasuwanci da Gudanarwa a 2020.

To amma ban samu damar yi wa kasa hidima ba (NYSC) saboda shekaruna sun zarta shi ya sa na samu takardar shaidar yawaitar shekaru kamar yadda tsarin hakan ya nuna.

Daga nan ne na tsunduma cikin harkar sayar da kifi da sauran abubuwan da za su ba ni wani abu don ci gaba da bukata ta.

A halin yanzu ina da mata daya da ’ya’ya hudu.

An zabe ka dan Majalisar Dokokin Jiha, ko ka taba tsayawa takarar wani mukami?

Eh, lallai na taba tsayawa takarar kansila a 2021 lokacin ina Jam’iyyar APC kafin in koma PDP, amma ban samu ba.

Mutanenmu musamman matasa, sun ce in yi takara, domin suna ganin zan iya yin abin da ya fi haka, amma Allah bai Sa na dace ba a wancan lokaci, daga bisani muka yi addu’ar Allah Ya ba mu matsayi mafi alheri da za mu taimaki al’umma.

Alhamdulillah Allah kuwa Ya karbi addu’armu da na manyanmu ga shi yanzu na zama dan majalisar dokoki.

Kamar yadda muka samu labari a baya an ce akwai lokacin da wasu jami’an tsaro suka kama ka, kuma suka tsare har sau uku saboda sukar shugaban majalisar da wasu ’yan siyasa a Facebook. Mece ce gaskiyar hakan?

A gaskiya an kama ni sau biyu. Daya daga cikinsu ya fito daga wani dan siyasa a Jam’iyyar APC kafin in bar jam’iyyar, bayan na yi masa suka a Facebook, sai ’yan sanda su kama ni suka tsare ni na tsawon kwana biyar.

Na biyu shi ne na Shugaban Majalisar wanda na yi suka a kan rashin wakilci nagari da yake mana mu al’ummar Mazabar Nguru 11.

An kama ni aka tsare na tsawon awa 48 wato a bara a cikin watan Ramadan wato kamar yanzu.

Kuma abin da ke jawo min irin wannan kamu bai wuce duk lokacin da na ji cewa gwamnatin jiha ta amince da aikin mazabu ga ’yan majalisar jiha, nakan tabbatar da inda aka kashe namu kudaden, idan yana da wani tasiri a cikin al’ummarmu, inda nakan bi diddiginsu don ganin an yi aikin.

Don haka matukar na ga ya gaza yin abin da ya dace nakan soke shi a duk lokacin da na gano cewa muna da matsalar da zai iya magancewa amma ya kasa yin haka, kuma nakan yi suka ce ta gaskiya babu son zuciya a ciki hakan ke haifar min da kamu da tsarewa.

Me ya jawo hankalin ka, ka tsaya takara da Shugaban Majalisar wanda ya shafe shekara 20 a majalisar har ya kai matsayin da yake kai a yanzu?

Hakikanin gaskiya abubuwa da yawa sun yi tasiri kan tsayawa takararta.

Abu na farko, fannin ilimi, muna da komawa baya a kauyenmu na Majakura kuma mukan ga yadda abubuwa suke faruwa kowace rana inda ajujuwanmu sun lalace ga kuma karancin ayyukan yi ga matasanmu masu yawa haka nan a bangaren lafiya nan ma haka lamarin yake don haka na gane cewa rashin wakilci mai kyau ya haddasa mana shiga cikin wannan yanayi.

Don haka don magance wadannan kalubale ne, ya sa mutanenmu suka ce in tsaya takara watakila suna tunanin zan yi abubuwa daban da za su taimaka musu.

Ka ce mutanenka suka ce ka fito takara, ko sun ba ka wani tallafi don yakin neman zabe?

Eh, sun saya min fom din takara. Sun kuma ba da gudunmawar kudi don yakin neman zabe kuma ba su tuntube ni ba ko ina da sha’awa ko a’a.

Sai kawai suka sayi fom suka ce suna so in tsaya takara, ni kuma ban tambaye su nawa suka sayi fom din ba, nan take na cika na mayar musu da shi.

Ka san cewa lokacin da kake neman kujera a kowace jam’iyya akwai zaben fid-da gwani, amma na yi nasara ba tare da hamayya ba a jam’iyyata ta PDP.

Mutanen kauyena wadanda galibi manoma ne da masu sayar da kifi, su ma sun tara min kudi don yakin neman zabe cikinsu akwai wadanda sukan kira ni ta waya suna yi min fatar samun nasara, wasu kuma su tura Naira dubu 20 zuwa dubu 50 a asusun bankina, duk don suna ganin zan iya yin abubuwan da suka dace matukar na kai ga nasara.

A lokacin yakin neman zabenmu, an yi ta tursasa wa mutane saboda bambancin jam’iyya, amma alhamdulillahi duk da kalubalen da aka fuskanta mun samu nasarar cin zabe, amma dai ba abu ne mai sauki ba kayar da Shugaban Majalisar Dokoki ta Jiha.

Ko Shugaban Majalisar ya tuntube ka kafin zabe a kan ka janye masa?

Maganar gaskiya bai tuntube ni don in janye takararta shi da kansa ba. Amma wani jami’in gwamnati da wasu da nake tunanin wakilansa ne sun zo min sau biyu suna cewa in janye.

Sun yi alkawarin ba ni Naira miliyan 18, amma na ki, daga baya suka dawo suka yi min tayin Naira miliyan100, amma na ki.

Na ce da su mutanen kauyenmu ne suka sayo min fom don tsayawa takara saboda sun yi imanin cewa zan yi abubuwan da suka kamata in na samu nasara.

Don haka ban ga dalilin da zai sa in janye daga takara ba. Da na ga sun matsa sai na ce su je su hadu da mutanena idan da gaske suna son in janye takarata ga duk wanda ya aiko su gare ni.

Daga bisani na gaya wa jama’ata abin da muka tattauna amma duk mun yarda cewa ba zan janye ba, sai muka ci gaba da yakin neman zabe ba tare da sake saurararsu ba.

Wane abu za ka sa gaba in ka shiga majalisa domin al’ummar mazabarka?

A koyaushe muna yin abubuwa daban misali, kamar yadda nake magana da ku, ina da ’yan mata sama da 25 da maza 30 da suka samu karatun sakandare ta hanyar tallafi da horarwa.

Shugaban Majalisar ba zai iya gaya muku adadin mutanen da ya taimaka wajen cimma wannan buri ba kasancewar ban yi tsammani yana da abin fada ba kan haka.

Dangane da kyakkyawan wakilci, zan ba da fiffiko ga ilimi ta hanyar gyara azuzuwanmu tare da tabbatar da mun dauki kwararrun malamai da samar da kayan koyo da koyarwa.

Na biyu, cibiyoyin kula da kiwon lafiyarmu suna bukatar kulawa sosai ta hanyar samar da magunguna da ma’aikatan lafiya kwararru lura da cewa muna da al’ummomi masu yawa.

Har ila yau zan kokarta wajen samar da ruwa da kuma sauran kayan more rayuwa.

Haka nan zan matsa ta wajen rokon gwamnati ta yi wa mutanenmu abubuwan da suka dace na ci gaban su, kuma zan yi duk mai yiwuwa wajen gabatar da kudiri don tabbatar da cewa an sake gina hanyoyinmu da suka lalace a mazabata in Allah Ya so.

Akwai mutane da dama da suka kammala karatu amma ba su da aikin yi kuma makarantunmu na bukatarsu, don haka zan tabbatar da cewa gwamnati ta dauki irin wadannan mutanen aiki, walau aiki na wucin-gadi ko na dindindin.

Zan tabbatar cewa ina tare da mutanena a kowane karshen mako don jin matsalolinsu da abin da zan iya yi don magance su.

Idan ba zan iya magance matsalolin ba zan kai su ga bangarorin da suka dace don daukar mataki a kai.

Gwamna Buni ko Shugaban Majalisar akwai wanda ya kira ka don taya ka murnar lashe zabe?

Gaskiya babu daya daga cikinsu da ya kira ni ya taya ni murna, amma na samu sakonnin taya murna daga ma’aikatan gwamnati da ’yan siyasa da ’yan jarida da kuma kungiyoyin farar hula.

Sakonnin wadannan mutane sun karfafa ni, don haka ban damu da sakon Shugaban Majalisar ba.

Sakamakon zaben ya nuna Jam’iyyar APC na da kujerun ’yan majalisa 22 yayin da jam’iyyarku ta PDP ke da biyu, ku ’yan tsiraru ne da hakan na iya shafar aikinku, ko akwai yiwuwar ku sauya sheka zuwa APC?

A gaskiya ba zan ce komai ba domin Allah ne kadai Ya san abin da zai faru yau ko gobe, Na san cewa Gwamna Buni mutum ne mai tawali’u mai basirar shugabanci, don haka bisa fahimtata da shi ba zai bari bambancin jam’iyya ya yi tasiri ga ci gaban Nguru ko Jihar Yobe ba.

Abin da zan iya cewa shi ne, zan yi duk mai yiwuwa don ganin na isar da sako da matsalolin al’ummar mazabata wadanda aka bari a baya ga gwamnatin jiha da bin duk hanyoyin da suka dace, tare da fatar magance su.

Insha Allahu ba zan taba bata musu rai ba dangane da bukatunsu.

AMINIYA


Friday, 31 March 2023

Gobara Ta Barke A Gidan PDP

 


Ga dukkan alamu gobara ta sake barkewa a gidan babbar jam’iyyar adawa ta kasar nan wato PDP, wadda ta sake shiga rudu, makonni kadan da faduwarta a zaben Shugaban Kasa.

A ranar Talata da ta gabata ce, Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar na Kasa (NWC), ya ayyana Ambasada Iliya Umar Damagum a matsayin Shugaban Riko na jam’iyar ta kasa.

Kafin nadinsa, Alhaji Iliya Damagum shi ne Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Shiyyar Arewa.

Kakakin Jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba ne ya bayyana nada Damagun a ranar Talata a wani taron manema labarai a Abuja.

A sanarwar da PDP ta fitar, ta ce ya zame mata dole ta yi biyayya ga umarnin wata kotu da ta bukaci Shugaban Jam’iyyar na Kasa Dokta Ayu Iyorchia ya daina bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan kararsa da aka kai gabanta.

Wata Babbar Kotu a Jihar Benuwai ce ta dakatar da Dokta Iyorchia Ayu daga shugabancin Jam’iyyar PDP ta Kasa.

Alkalin Kotun, Mai Shari’a W.I Kpochi ne ya bayar da umarnin a ranar Litinin bayan sauraron kunshin karar da aka shigar Mai lamba MHC/85/2023.

Tun a ranar Juma’ar da gabata Jam’iyyar PDP ta ce ta dakatar da Shugabanta na Kasa, Iyorchia Ayu bisa zarginsa da wasu ayyuka na cin amanar jam’iyyar.


Shugabannin jam’iyyar a matakin gundumarsa da ke Karamar Hukumar Gboko, a Jihar Benuwe ne suka dauki matakin.

Sun ce sun dakatar da shi ne bayan kada kuri’ar rashin kwarin gwiwa kan ayyukansa.

A lokacin da ya karanta matsayar da shugabannin suka cim ma, Sakataren Jam’iyyar a Gundumar Igyorob, Mista Banger Dooyum ya ce zagonkasa da Ayu da na kusa da shi suka yi wa PDP ne ya janyo mata shan kaye a gundumar da kuma jihar baki daya a zaben Gwamnan da aka yi a jihar.

Sun kuma zargi Ayu da rashin biyan kudaden da ake karba na shekara-shekara daga ’ya’yan jam’iyyar, kamar yadda dokokinta suka tanada.

hugaban Kungiyar, Terzungwe Atser ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, inda a ciki ya ce ba zai taba yiwuwa jagororin jam’iyyar su dauki wannan mataki ba a yanzu ba tare da an tursasa su yin hakan ba.

Yanzu aka fara rigimar —Wike

A bangaren Gwamnan Jihar Ribas, Nyesome Wike ya ce yanzu aka fara rigimar siyasa a tsakaninsa da dakataccen shugaban na PDP, Dokta Ayu.

Ya ce hankali ba zai dauka ba a ce wanda ya kasa kawo mazabarsa a zabubbukan da suka gabata ya ci gaba da jagorantar PDP a matsayin Shugabanta na kasa.

Wike ya bayyana haka ne lokacin da yake kaddamar da makarantar Okoro-nu-Odo da ke Karamar Hukumar ObioAkpor da ya sabunta.

Ya ce, Allah ne kadai Ya san dalilin da Ayu ya kekeshe zuciyarsa ya ki sauka daga mukaminsa a lokacin da Gwamnoni 5 da ake kira G5 suka bukaci hakan bayan Atiku Abubakar ya zama dan takarar Shugaban Kasa a PDP.

Gwamna Wike ya ce da a ce lokacin da suka bukaci haka, Dokta Ayu ya amince ya sauka, da irin su da suka yi kokarin ganin an mayar da mulki Kudu sun yi amfani da wannan wajen samun sulhu, wanda a cewarsa watakila da hakan ya sa Jam’iyyar PDP ta samu nasara.

“Ku wadanda kuke cewa kun dakatar da Ayu, ba ku ma ga komai ba.

“Ayu, yanzu aka fara rigimar nan. Wadanda suke kusa da shi su fada masa cewa yanzu aka fara,” in ji Wike.

Duk da cewa ba yanzu aka fara yunkurin cire Ayu daga Shugaban PDP na Kasa ba, wannan karon lamarin ya yi karfi matuka domin a cikin shugabannin jam’iyyar da masu ruwa-da-tsaki an samu rabuwar kai kan cire shi.

Aminiya ta samu labarin cewa an fara yunkurin ganin bayansa ne kwanaki kadan bayan zaben Shugaban Kasa, inda Jam’iyyar PDP ta sha kaye a hannun Jam’iyyar APC, rashin nasarar da wasu suka alakanta da kin amincewa ya sauka daga mukaminsa.

Aminiya ta ruwaito yadda hayaki ya fara tashi a jam’iyyar bayan Atiku Abubakar ya doke Gwamna Wike na Ribas a zaben fid-da-gwan na takarar Shugaban Kasa.

Gwamna Wike da wasu gwamnoni hudu sun ware, inda suka kafa Kungiyar G5, wadda daga cikin bukatunta akwai batun cire Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar.

A cewarsu, ba zai yiwu ba dan takarar Shugaban Kasa da Shugaban Jam’iyya su fito daga yanki daya, wanda hakan ya sa suka bukaci Ayu ya sauka, a musanya shi da wani daga Kudu.

Hakan ya sa PDP ta shiga zaben Shugaban Kasa ba tare da gwamnonin biyar tare da ita ba, ciki har da Wikem, Gwamnan Jihar Ribas wadda take kan gaba wajen ba PDP kuri’u a zabubbukan baya.

Aminiya ta samu labarin cewa wannan yunkurin ya kara zafi ne kasancewar shugaban ya kasa hada kan jam’iyyar kafin zabe da kuma gazawarsa wajen kawo wa PDP jiharsa a zaben Shugaban Kasa da na gwamnoni, duk da cewa ba sa ga maciji da Gwamnan jiharsa ta Binuwai daya daga cikin gwamnonin G5.

Wasu abubuwan da suka kara ta’azzara rikicin shi ne batun dakatar da wasu jiga-jigan Jam’iyyar PDP da suka hada da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Anyim Pius Anyim da tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose da tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema kuma ta bukaci Kwamitin Ladabtarwa na Jam’iyyar da ya binciki Gwamna Ortom na Binuwai.

Jim kadan bayan dakatar da Shema ne ya fitar da sanarwa, inda a ciki ya bukaci ko dai a janye dakatarwa, ko ta zama takardar sallamarsa daga jam’iyyar, domin a cewarsa ba zai yiwu a dakatar da shi ba, inda kuma aka ce dole za a dakatar da shi, to zai bar jam’iyyar.

Daga cikin wadanda suke gaba-gaba wajen ganin an cire Ayu, akwai gwamnonin G5, wato Gwamna Nyesom Wike na Ribas da Samuel Ortom na Binuwei da Seyi Makinde na Oyo da Okezie Ikpeazu na Abiya da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.

Akwai kuma wasu jigajigan jam’iyyar, ciki har da tsofaffin gwamnoni da suka hada da Ibrahim Shema da Cif Bode George da Ayo Fayose da sauransu.

Haka a cikin jagororin jam’iyyar, Aminiya ta samu labarin cewa an samu rarrabuwar kai a tsakaninsu, inda wasu suka amince a cire shi, wasu kuma suke tare da shi.

Akwai bayanan da suke cewa mai yiwuwa Dokta Ayu ya kalubalanci dakatar da shi da Kwamitin NWC ya yi a kotu, lamarin da ake jin zai kara rura wutar rikicin da ke cin jam’iyyar.

AMINIYA

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

SAPZ Kano partners ABCOAD to organize FFS Training for Youth and Women.

The Special Agro-Industrial Processing Zones (SAPZ) Programme, Kano State, in collaboration with Audu Bako College of Agricultur...