Search This Blog

Saturday, 29 April 2023

’Yan Bindiga Sun Sako 70 Daga Cikin Yara 85 Da Suka Sace A Zamfara

 


’Yan ta’adda da suka yi garkuwa da yara sama da 85 a Jihar Zamfara sun sako 70 daga cikin yaran, amma sun kashe biyu.

A ranar Juma’a ’yan ta’addan suka sako yaran, kimanin mako uku bayan sun sace su daga kauyen Wanzamai na Karamar Hukumar Tsafe ta jihar.

Wani mazaunin yankin Sani Aliyu ya ce, “Yara biyu da ’yan bindigar suka kashe sun yi kokarin tserewa ne, wadanda aka sako din kuma sun galabaita saboda tsananin yunwa, kuma yanzu ana duba lafiyarsu.”

Ya ce ganin irin galabaitan da yaran suka yi ya sa iyayensu koke-koke, kuma “An sako su ne bayan an biya kudin fansa Naira miliyan shida; da farko miliyan uku aka ba su, amma suka ki sako su, sai an kara musu da sabbin babura guda biyu.”

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bangaren Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, amma hakarsa ta yin magana da kakakin rundunar, CSP Muhammad Shehu, ba ta cim ma ruwa ba.

Kimanin makonni uku da suka gabata ne ’yan bindiga suka  ritsa wasu yara da suka je neman icen girki da wasu manya a gonaki suka yi awon gaba da su a yankin Tsafe na Jihar Zamfara.

Daga cikin manyan da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su har da mata.

AMINIYA

Ba Ma Yi Wa Shirin Mika Mulki Zagon Kasa - Ganduje

Gwamnatin jihar Kano  ta ce a shirye take domin miƙa mulki ga sabuwar gwamnati cikin ruwan sanyi ba tare da tayar da ƙura ba.

Cikin wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sa hannun kwamishinan yaɗa labarai Muhammad Garba, gwamnatin ta ce tuni aka samar da babban kwamiti da kuma ƙanana da za su taimaka domin ganin an miƙa mulkin salin alin.

Ya musanta iƙirarin jam’iyyar NNPP da ta ke jiran karɓar mulki na cewa gwamnatin Ganduje na yi wa shirin miƙa mulki zagon ƙasa.

Kwamishinan ya ƙara da cewa kwamitin miƙa mulki na ɓangaren gwamnatin Ganduje na rubuta rahoton ƙarshe kafin miƙa mulki. Ya bayyana cewa kamata ya yi kwamitin karɓa na gwamnati mai jiran gado shi ma ya shirya domin karɓar rahoton, wanda ya yi alƙawarin miƙawa a kan lokaci.

Muhammad Garba ya ƙara da cewa manufar miƙa mulki shi ne gwamnati mai sauka ta miƙa duk wasu abubuwa na tafiyar da shugabanci cikin ruwan sanyi. Ba yunkurin yaɗa wani tunani ko wata aƙida ba.

Ya kuma ce kamata ya yi gwamnati mai jiran gado ta mayar da hankali game da shirin da take yi na karɓar mulki, ta kuma kiyaye duk wani abu da zai iya janyo fitina a yayin miƙawar.

Ƙorafin da NNPP ta yi a jiya shi ne gwamnatin ta ba ta gurbi uku kawai a cikin kwamitin da aka kafa don miƙa mulki hannun sabuwar gwamnati.

BBC 

Labari da dumiduminsa : Shugaba Buhari Ya Dage Kidayar 2023

A wata ganawa da ya yi da mambobin majalisar zartaswa ta tarayya da kuma shugaban hukumar kidaya ta kasa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dage kidayar yawan jama’a da gidaje na shekarar 2023, wadda aka shirya gudanarwa tun daga ranar 3-7 ga watan Mayun 2023. Za a tantance sabon ranar ne ta hanyar gwamnati mai shigowa.


An cimma matsayar ne bayan taron ya jaddada muhimmancin da ke akwai na kidayar jama’a, wanda ba a yi ta tsawon shekaru 17 ba, na tattara sabbin bayanai domin inganta rayuwar ‘yan Nijeriya, da kuma fitar da manufofin ci gaban kasar. Duk da irin gagarumin ci gaban da aka samu da suka hada da kammala aikin tantance yankin da kuma daukar ma'aikata da horar da ma'aikata, shugaban ya bayyana cewa kamata ya yi gwamnati mai jiran gado ta samu damar karfafa wadannan nasarori.

Shugaba Buhari ya yaba wa tsarin hukumar kidaya ta kasa, musamman yadda ake tura na’urorin zamani domin tabbatar da kidayar jama’a mai inganci kuma abin dogaro. An umurci hukumar da ta ci gaba da shirye-shiryen kidayar jama’a don dorewar nasarorin da aka samu.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da suka hada da babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami; ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Mrs Zainab Ahmed; ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed; Karamin Ministan Kasafi da Tsare-Tsare na Kasa, Mista Clem Agba da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Boss Mustapha.


A wata sanarwa da ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya fitar a ranar 29 ga Afrilu, 2023, an sanar da jama’a shawarar dage kidayar.
NIGERIAN TRACKER 

Friday, 28 April 2023

PDP Ta Bukaci Sanyawa Buhari Takunkumi

Babbar jam’iyyar adawar Najeriya ta PDP ta bukaci kasashen duniya da su hana shugaban kasa Muhammadu Buhari bizar tafiye tafiye da zaran ya mika mulki ranar 29 ga watan gobe, saboda abinda ta kira kalamansa dangane da zaben shugaban kasar da akayi ranar 25 ga watan Fabarairu. 


Yayin tsokaci akan zaben, Buhari ya bayyana ‘yan adawar Najeriya a matsayin wadanda suka shantake akan cewar zasu samu nasara ba tare da neman goyan bayan jama’a kamar yadda jam’iyarsa ta APC tayi ba. 

Sakataren hulda da jama’a na jam’iyyar Debo Ologunagba yace kalaman shugaban na iya tinzira jama’a da kuma haifar da illa ga zaman lafiyar kasar. 

Ologunagba ya kuma ce kalaman na iya karfafawa alkalai gwuiwa wajen yanke hukunci akan karar da suka shigar a gaban kotu domin kalubalantar sakamakon zaben wanda yace tuni wasu a ciki da wajen kasar ke bayyana shi a matsayin mafi muni a tarihin Najeriya. 

Jam’iyyar PDP tace zaben da akayi bana ya gamu da matsalolin da suka sabawa kundin tsarin mulkin kasa da kuma dokar zabe ta shekarar 1999 da kuma 2022 musamman abinda ya shafi wallafa sakamako daga tashoshin zabe da kuma aikewa da su kai tsaye zuwa cibiyar hukumar ta kasa. 

Kakakin jam’iyyar ya jaddada cewar suna da yakinin cewar basu fadi zabe ba, kamar yadda shugaba Buhari ke fadi, kuma ba zasu bada kai bori ya hau ba duk da barazanar da gwamnatin APC ke musu. 

Jam’iyyar tace ganin yadda Buhari ya yiwa dimokiradiya illa a Najeriya, suna bukatar kasashen duniya da su kakaba masa takunkumi da kuma hana shi da iyalansa tafiye tafiye da zaran ya mika mulki ranar 29 ga wata. 

Ologunagba yace wannan bukatar tasu tayi dai dai da bukatar da shugaba Buhari ya gabatarwa kungiyar kasashen Turai a ranar 17 ga watan Fabarairun shekarar 2022 lokacin da ya ziyarci kungiyar EU a Brussels. 

RFI

Ci-da-zucin 'yan adawa ne ya kayar da su zaɓe - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya yi imani ci-da-zuci ne babban abin da ya janyo taron 'yan adawar Najeriya suka sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa da ya wuce.

Ya bayyana haka lokacin da ya karɓi gwamnonin jam'iyyarsa ta APC a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi.

Yana cewa a daidai lokacin da jam'iyya mai mulki take aiki tuƙuru don ci gaba da mulki a zaɓukan da aka yi a baya-bayan nan, 'yan adawa suna can sun cika da ci-da-zuci.

"Sun je suna ta faɗa wa masu goya musu baya a ƙasashen waje cewa, sai sun kayar da APC.

Yayin zaɓen na 25 ga watan Fabrairu, ɗan takarar jam'iyyar APC mai mulki Bola Ahmed Tinubu ya smau ƙuri'a 8,794,726.

Sai Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban ƙasar da ya samu ƙuri'a miliyan 6,984,520.

Ɗan takarar jam'iyyar Labour, Peter Obi yana da ƙuri'a miliyan 6,101,533, yayin da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya zo na hudu da ƙuri'a miliyan 1,496,687.


Shugaba Buhari ya ce jam'iyyarsu ta yi nasara ne saboda ta haɗa ƙwarin gwiwar da take shi da taka-tsantsan kuma ta yi aiki tuƙuru har ya kai ta ga nasara.

Ya ce yanzu ma ga shi ci-da-zucin yana haifar wa 'yan adawan ƙarin matsaloli fiye da kowa.

"Abin na yi musu wahala su yi wa masu goyon bayansu na ƙasashen waje gamsasshen bayani a kan abin da ya sa suka gaza kayar da mu," in ji Buhari.

A cewarsa, sun haɗa ci-da-zuci da ji-ji-da-kai da bahagon lissafi, kuma su ne suka ja musu faɗuwa a zaɓukan bana. "Wannan ya sake haifar da ƙarin matsaloli a cikinsu. ta kai har ana tambaya. Me ya sa suka kasa kayar da mu?"

Shugaba Buhari ya ce babban dalilin da ya sa shi taya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu murna kan nasarar da ya samu, shi ne 'yan adawa sun samu goyon baya, kuma masu goyo musu bayan daga ƙasashen waje sun lasa musu zuma a baki.

"Hakan ta sa sun tafi da burin cewa za su ci zaɓe, za su kayar da mu.

Wanne irin kuskure ne wannan?" shugaban ya sake tambaya.

'Kaduna zan koma bayan na huta a Daura'
Shugaba Buhari ya kuma yi bayani game da burinsa na rayuwa bayan sauka daga mulki, inda ya ce ya yi niyyar komawa gidansa na Daura, inda zai zauna tsawon wata shida kafin ya koma Kaduna.

Sanarwar Mallam Garba Shehu mai magana da yawun shugaban ƙasar, ta ambato Buhari yana yaba wa "Gwamna Nasir El-Rufa'i na Kaduna saboda ƙoƙarin da ya yi wajen samar da ababen more rayuwa da za su kyautata rayuwarsa da ta al'ummar jihar bayan ya kammala mulki".


Tun bayan sanar da sakamakon zaɓen 25 ga watan Fabrairu, masu sharhi kan al'amuran siyasa a Najeriya, suka yi ta tsokaci game da sakamakonsa.

Idan da 'yan adawan ƙasar sun haɗa ƙarfi wuri ɗaya, mai yiwuwa da cikin sauƙi, sun cinye zaɓen shugaban ƙasa.

Ana dai ɗora alhakin faɗuwar jam'iyyun adawar na Najeriya ne a kan matsalar rarrabuwar kai, da shiga zaɓe a lokacin da suke fama da ɓaraka.

'Yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen watan Fabrairu guda biyu, Peter Obi da Rabi'u Musa Kwankwaso, duk sun ɓalle ne daga babbar jam'iyyar adawa ta PDP, wadda ta shiga zaɓen kuma tana fama da ɓaraka da rikicin cikin gida.

Idan an haɗa lissafin ƙuri'un da 'yan takarar biyu suka samu da na jagoran adawar Najeriya, Atiku Abubakar jimillar ƙuri'un za su kai 14,582,740.

Adadin dai ya kusa ninka abin da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya samu, har suka ba shi nasara
 BBC 

Kwamitin Karbar Mulki Na NNPP Na Kano Ya Zargi Gwamna Ganduje da gurgunta Tsarin Karbar mulki

Kwamitin Karbar Mulki na jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano, ya zargi gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje mai barin gado da yin zagon kasa ga tsarin mika mulki ga gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf mai jiran gado.


A cewar shugaban kwamitin mika mulki na jam’iyyar NNPP, Farfesa Abdullahi Baffa Bichi, gwamnatin Ganduje ta nuna turjiya da rashin hadin kai tun bayan kafa kwamitin mika mulki na NNPP da zababben gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.

Jaridar Nigerian Tracker ta rawaito Bichi yana bayyana cewa kwamitin mika mulki na NNPP ya kafa kananan kwamitoci 33, amma babu daya daga cikin kwamitocin da ya samu hadin kai daga gwamnatin Ganduje. Duk da yunkurin kwamitin mika mulki na jam’iyyar NNPP na shirya taron hadin gwiwa da kwamitin mika mulki na gwamnati mai barin gado, gwamnatin Ganduje ta bukaci su zabi mutane uku ne kawai a taron wanda jam’iyyar NNPP ba ta amince da shi ba.

Bichi ya zargi Gwamna Ganduje da mayar da dukkan sakatarorin dindindin na jihar a wani bangare na kokarinsa na kawo cikas ga tsarin mika mulki a Kano.

Kwamitin rikon kwarya na NNPP ya yi kira ga dukkanin hukumomin  da su ba kwamitin mika mulki tare da mutunta zabin mutanen Kano da suka zabi Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Kwamitin Karbar mulkin na NNPP zai gudanar da taron hadin gwiwa tare da dukkanin sakatarorin dindindin, shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnati, da daraktocin gudanarwa na dukkanin kananan hukumomi 44 daga ranar Talata 2 ga watan Mayu, domin tabbatar da samun saukin aikin. 

"Muna kira ga Gwamna Ganduje da ya mutunta zabin mutanen Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya ba da mulki ga wanda Ya so"

Kotu ta sake umartar Ganduje da ya amince da Muhuyi Magaji a matsayin Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa

Kotun ma'aikata ta kasa da ke zamanta a Kano ta yi watsi da karar farko da gwamnatin jihar Kano ta shigar kan wata doka da ta hana gwamnatin jihar nada kowane mutum a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar.

Idan dai za a iya tunawa, a kwanakin baya ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya mika sunan mukaddashin shugaban hukumar Mahmud Balarabe ga majalisar dokokin jihar domin tabbatar da shi a matsayin kwararren shugaba.

Majalisar ta tsara tantance shugaban riko a ranar 2 ga Mayu, 2023.

SOLACEBASE ya bayar da rahoton a wani hukuncin da kotu ta yanke a baya a cikin wani umarni na musamman cewa dakataccen shugaban hukumar korafe-korafen al’umma da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimigado ya ci gaba da kasancewa a matsayin shugaban hukumar.

Biyan kuɗi zuwa wasiƙarmu
Shigar da adireshin imel ɗin ku
Yi rijista
Karanta kuma:Kwarai Muhuyi a matsayin Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kano- Kotu ta umarci Ganduje

A zaman kotun a ranar Juma’a, Mai shari’a E.D. Isele ta yi watsi da karar farko da gwamnatin jihar Kano ta shigar kan lamarin yayin da ta amince da bukatar Muhuyi Magaji Rimingado ta amince da shi a matsayin shugaban hukumar.


Kotun ta kuma gargadi Lauyan Gwamnatin Jihar Kano da ya gargadi wanda yake karewa da ya daina duk wani tsari na tabbatar da wani mutum a matsayin Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano.

HAJJIN 2023: Rikicin Sudan Ka Iya Kawo Matsala Ga Jigilar Ahazan Najeriya - Kungiyar Fararen Hula

Rikicin da ake fama da shi a kasar Sudan na iya kawo cikas ga jigilar maniyyatan Najeriya zuwa kasar Saudiyya cikin sauki, domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2023, in ji kungiyar daukar rahotannin aikin hajji mai zaman kanta.
 
Kungiyar farar hula a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma'a mai dauke da sa hannun shugabanta na kasa Ibrahim Muhammad, ta ce tuni yakin ya kai ga rufe sararin samaniyar Sudan ba zato ba tsammani.
 
Kungiyar ta ce Najeriya "dole ne ta hanyar NAHCON ta yi gaggawar sake duba kalubalen da ke gabanta sannan ta fito da wasu zabin da za a yi a matsayin ma'auni."
 
Kamar yadda jadawalin NAHCON ya nuna, za a fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa kasa mai tsarki a ranar 21 ga Mayu, 2023.
 
Jiragen saman jigilar alhazan Najeriya na tafiya ta sararin samaniyar Sudan a lokacin da suke tafiya Saudiyya, kuma ana daukar matsakaicin sa'o'i hudu zuwa biyar kafin su isa kasar.
 
Sai dai kuma rufe sararin samaniyar kasar Sudan ba zai tilastawa masu jigilar jigilar Alhazan jiragen sama na zirga-zirga ta wasu hanyoyi daban-daban da za su dauki sama da sa'o'i bakwai daga Najeriya ba, ta yadda za a kara wa'adin aikin jigilar jiragen.
 
Kungiyar ta ce wani ma’aikacin canjin hanyoyin mota baya ga lokacin, shi ne farashin tikiti wanda wani karin nauyi ne kan mahajjata.
 
Sanarwar ta ce, "Muna cikin fargabar cewa za a iya tilasta wa maniyyatan mu su tashi ta kasashen Kamaru, Afirka ta Tsakiya, Eritrea, Habasha, Kenya, Uganda, ko DRC don isa Saudiyya."
 
Kungiyar  ta damu da cewa tuni rufe sararin samaniyar Sudan ya tilastawa wasu manyan kamfanonin jiragen sama irin su Qatar Airways, Turkish Airlines, Etihad Airways, Emirates da Saudi Airlines fara jigilar jiragensu zuwa wasu kasashen Afirka da Kudancin Amurka.
 
Ta ce, kamfanin jiragen saman kasar Habasha wanda ke kan gaba wajen gudanar da aikin Hajji a Najeriya, tuni ya sake karkata hanyoyin sadarwa har guda 38.
 
“Muna kira ga Gwamnatin Tarayya, da ta gaggauta duba lamarin, ta samar da hanyar da ta dace ga masu jigilar alhazai kafin a fara jigilar maniyyatan Najeriya. Yin dinki a cikin lokaci yana ceton tara," in ji sanarwar.

Firaministan Pakistan ya tsallake rijiya da baya

 


Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya tsallake rijiya da baya, bayan da ‘yan majalisar kasar suka kada kuri’ar yanke kauna, yayin da sauran kungiyoyin fararen hula suka matsa kan a fara shirin gudanar da babban zaben kasar. 

Sharif ya sami kuri’un amincewa guda 180, yayin da ‘yan majalisa 172 suka nuna rashin amincewa da salon shugabancin sa, abinda ya bashi damar ci gaba da rike mukamin sa da kyar. 

Ko da yake jawabi, kakakin majalisar dokokin kasar Raja Pervais Asharf, yace a yanzu abinda majalisar zata mayar da hankakli shine batun babban zaben da ke tafe. 

Sharif wanda ya gaji Imran Khan ya yabawa mambobin jam’iyyyar sa da ke majalisar bayan da suka amince da salón mulkin sa, tare da yanke hukuncin sake bashi dama, ta hanyar kada kuri’ar amincewa da shi. 

rfi

An tilasta wa 'ya'yanmu ba da fasfo kafin a kai su Masar - Iyayen ɗaliban Sudan

 


Hausawa kan ce tsuguno ba ta ƙare ba a kan lamarin ɗaliban Najeriya da ke karatu a Sudan, waɗanda gwamnatin Najeriyar ta ce za ta kwaso su zuwa gida.

Yayin da ake kukan cewa har yanzu akwai tarin ɗalibai da aka bari a ƙasa - a gefe ɗaya kuma iyayensu na kukan lokaci na ƙurewa, ko da yake an tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da ƙarin sa'a 72.

Iyayen ɗalibai da dama da BBC ta tattauna da su, sun ce yanzu haka halin da yaransu ke ciki ya fi wanda suka baro a Khartoum.

Asma'u Yarima Muhammad, sakatariyar ƙungiyar iyayen ɗaliban Najeriya da ke karatu a Sudan, ta ce 'ya'yanta biyu "na cikin tsakiyar sahara ba tare da sanin inda suka dosa ba".

Asma'u Yarima na da yara biyu 'yan shekara 18, wato 'yan tagwaye ne duka maza.

Daya na karantar fannin zane, sai kuma ɗayan da ke nazarin aikin likita.

Ta ce yawancin dare sukan yi waya da yaranta irin ta iyaye da 'ya'ya wadda rabinta nishaɗi ne, ɗaya rabin maganar karatu.

Amma tun daga 15 ga watan Afrilun da muke ciki rayuwa ta sauya.

Ta ce "ƙasa da awa biyu da muke magana da kai na yi magana da su, kuma suna shaida min cewa motoci 7 cikin 13 da suka taso daga Khartoum sun tsaya a sahara, suna neman a ba su (cikon) kuɗin aikinsu.

"Ganin cewa yaran ba su da kuɗin da za su ba su, sai suka ce to su bayar da fasfo ɗinsu, kafin su ƙarasa da su Aswan da ke cikin ƙasar Masar, kamar yadda suka cimma yarjejeniya da gwamnatin Najeriya", in ji Hajiya Asamau.

Wata mahaifiya da BBC ta tattauna da ita ko da yake ta nemi a sakaya sunanta, ta ce sai da yarinyarta ta shiga mota a cikin motocin da aka kawo, amma daga baya aka fitar da ita.

"Kimanin sa'a biyu suka kwashe a cikin motar, duk murna ta ishe mu, ni da yan uwanta muna ganin ta tsira, amma daga baya aka fitar da ita.

Ta yi zargin cewa mutanen gari ne suka riƙa biyan kuɗi ana maye gurbinsu da ɗaliban da aka aika motacin su kwaso.

Yarjejeniya da ke tsakin gwamnati da masu kwaso ɗalibai

Asma'u Yarima Muhammad ta ce yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin jigilar motocin da zai kwashi ɗaliban Najeriya shi ne za a biya su dalar Amurka miliyan1.2.

"Gwamnati ta bai wa kamfanin dalar 400,000, saura dubu 800,000. A kan wannan sauran kuɗin ne suka tsayar da yaranmu a tsakiyar sahara, suka ce sai an cika musu kuɗinsu.

"Kuma kuɗin nan garinsu aka yi magana za a biya ba wai a aika musu ta asusunsu na banki ba,'' in ji ta.

Sai dai Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce daga safiyar yau Juma'a ne za a fara kwaso ɗaliban.

Kuma jirgin saman Air Peace da zai yi aikin kwashe ɗaliban da sauran 'yan Najeriya, zai tashi da ƙarfe 6 na yamma zuwa Aswan, cewar shugaban hukumar ba da agajin gaggawar.

Mustapha Habib Ahmed ya ce tuni motoci guda biyu ɗauke da ɗaliban da aka kwaso daga Khartoum suka isa bakin iyakar Masar.

Ya amsa cewa ba shakka sun samu matsala da wasu direbobi da suka zubar da ɗalibai a cikin Sahara kusa da Dongola, wani wuri mai nisan kilomita 411 daga Khartoum.

Mustapha Habib ya ce suna aikin shirya takardu tare da ofishin jakadancin Najeriya a Masar don ganin jirgin Air Peace ya samu damar jigilar 'yan Najeriyan daga birnin Aswan.

Ya ce tuni suka daidaita da kamfanin sufurin da ya zubar da ɗalibai a Sahara, har ma sun shiga motocinsu guda bakwai sun ci gaba da tafiya.

BBC

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Gimba Kakanda Celebrates Abdulmumin Jibrin at 50

Public affairs commentator and writer, Gimba Kakanda, has described Hon. Abdulmumin Jibrin as an archetype of a young Nigerian w...