Search This Blog

Friday, 10 February 2023

Labari da dumiduminsa : Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Sadiq Wali A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Kano Na PDP

A ranar Juma’a ne wata kotun daukaka kara ta jihar Kano ta tabbatar da Sadiq Aminu Wali a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Kano.


A wani hukunci na bai daya da ta yanke a ranar Juma’a, kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da karamar kotun ta yanke na tabbatar da Muhammad Abacha a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano na PDP.

Cikakkun labarin zai zo muku nan ba da jimawa ba…

Thursday, 9 February 2023

Hukumar NAHCON Ta Bude Cibiyar Bayar Da Horo Kan Ayyukan Hajji

Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta kaddamar da cibiyar bayar horo kan ayyukan Hajji da alhazai

Cibiyar za ta horas da duk ma’aikatan da ke aikin Hajji da Umrah ta Najeriya tare da ba su takardar shaida. Haka kuma za ta samar da hanyoyin koyon sana'o'i, bunkasa sana'o'in Matasa da kuma zama wurin tuntuba a duk duniya wajen horar da aikin Hajji da Umrah.

An kuma gabatar da kason farko na daliban cibiyar. Daliban sun hada da Shugaban Hukumar, da daukacin kwamishinonin zartaswa na Hukumar, mambobin hukumar da zababbun Sakatarorin gudanarwa na hukumar jin dadin Alhazai na Jahohi. 

Manyan baki da dama ne suka halarci bikin, ciki har da Ministan babban birnin tarayya Abuja, Malam Muhammad Musa Bello CON; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha CFR; Jakadan Saudiyya a Najeriya,  Faisal Ibn Ibrahim Al-Ghamdy; Shugaban NAHCON, Alh. Zikrullah Kunle Hassan da Babban Sakataren Hukumar NBTE, Farfesa Idris Bugaje.
(Nura Hassan Yakasai) 

Wednesday, 8 February 2023

Kotun Ƙolin Ta Dakatar Da Gwamnatin Najeriya Dga Aiwatar Da Wa'adin Amfani Da Tsofaffin Kudi

Kotun Ƙolin Najeriya ta dakatar da gwamnatin tarayya daga aiwatar da wa'adin amfani da tsofaffin takardun kuɗin kasar.

A baya dai CBN ya saka 10 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za a daina amfani da tsofaffin takardun naira 1,000 da 500 da kuma 200 da aka sauya wa fasali.

Jihohin arewacin ƙasar uku, waɗanda suka haɗa da Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka shigar da ƙarar a gaban Kotun Ƙolin ƙasar suna buƙatar kotun da ta hana Babban Bankin ƙasar aiwatar da wa'adin.

A hukuncin wucin-gadin da suka yanke, alƙalan kotun bakwai ƙarƙashin jagorancin mai shari'a John Okoro, sun dakatar da gwamnatin tarayya da Babban bankin ƙasar da sauran bankunan kasuwanci na ƙasar daga aiwatar da wa'adin 10 ga watan Fabrairu na amfani da tsofaffin takardun kuɗin ƙasar.

Kotun ta kuma ce dole ne gwamnatin tarayya da CBN da kuma sauran bankunan ƙasar su jingine batun aiwatar da wa'adin har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukunci game da lamarin a ranar 15 ga watan Fabrairu.

Wannan hukunci na nufin a halin yanzu al'ummar Najeriya za su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin ƙasar har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukuncin ƙarshe.

Batun wa'adin amfani da tsofaffin kuɗin ƙasar dai ya zama wani batu da ya ɗauki hankula a 'yan kwanakin nan.

Tuesday, 7 February 2023

Buhari ya gana da Emefiele da EFCC kan karancin Naira

 


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri  da Gwamnan Babban Bankin Kasar, CBN, Godwin Emefiele da shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa , EFCC, AbdulRasheed Bawa da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari  game da halin da kasar ke cikin na karancin takardar kudin Naira

Kazalika gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da takwaransa na Kebbi, Atiku Bagudu, su ma sun halarci zaman na yau Talata.

An gudanar da wannan zaman ne a daidai lokacin da  ake fama fa matsanancin karancin takardar kudin Naira wanda ya haddasa zanga-zanga a wasu sassan Najeriya tare da kaddamar da hari kan wasu bankuna da jami’an tsaro.

A Juma’ar da ta gabata  ne, shugaba Buhari ya roki ‘yan kasarr da su ba shi wa’adin kwanaki bakwai domin magance matsalar karancin takadar Nairar wadda ta samo asali sakamakon shirin Babban Bankin CBN na sauya fasalin Naira 1000 da 500 da kuma 200.

Nan da ranar 10 ga wannan wata ne, wa’adin da shugaban ya nema zai cika, yayin da ‘yan kasar suka zura idanu domin ganin yadda za ta kaya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa nan da ‘yan kwanaki kalilan, yayin da batun karancin Nairar ya yamutsa hazon siyasar kasar, inda har dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ke zargin cewa, zagon-kasa ake yi masa, shi ya sa aka bullo da shirin sauya Nairar gami da kirkirar matsalar karancin man fetur a cewarsa.

 (RFI)

Dillalan Man Fetur Sun Lashe Amansu Kan Shiga Yajin Aiki

Yan sa’o’i bayan umartar mambobinta su rufe ilahirin gidajen man fetur a Najeriya, Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Kasa (IPMAN) ta bukaci a bude gidajen a ci gaba da sayarwa.

Aminiya ta rawaito yadda a ranar Talata kungiyar ta bukaci a rufe ilahirin gidajen man da ke kasar nan take sannan a fara yajin aiki, kamar yadda wata sanarwa da Shugaban kungiyar na kasa, Mohammed Kuluwa, ya fitar ranar Talata.


IPMAN ta ce, “Sakamakon mawuyacin halin da muka tsinci kanmu a ciki wajen samo man da kuma sayar da shi da tsada, da kuma yadda hukumomi ke tilasta mana sayar da shi a kan farashin da muke faduwa.

“Muna umartar ilahirin mambobinmu da su dakatar da sayar da mai, sannan su dakatar da biyan kudin duk wani man da suka riga suke kokarin sarowa daga yanzu har sai abin da hali ya yi.”


To sai dai ’yan sa’o’i bayan waccan sanarwar, IPMAN ta yi mi’ara koma baya.

“Bayan tattaunawa da hukumomi masu ruwa da tsaki, muna umartar gidajen mai da su bude su ci gaba da sayarwa, yayin da uwar kungiya za ta ci gaba da tattaunawa,” kamar yadda sabuwar sanarwar ta IPMAN, wacce ita ma Shugaban nata ya sanya wa hannu ta fada.

Sanarwar ta dillalan man na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke ci gaba da kokawa da dogayen layuka da wahalar man ta haifar a fadin kasar.

Kazalika, ana fama da tsadar man a kusan duk fadin kasar, inda a wasu wuraren ya haura N370 a kan kowacce lita, yayin da a wasu Jihohin kuma rahotanni suka ce har ma ya haura N400

Hakan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fama da karancin takardun kudi sakamakon canjin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi.

(AMINIYA) 

Monday, 6 February 2023

Kotu Ta Hana Buhari Da CBN Kara Wa’adin Karbar Tsoffin Takardun Kudi


 Babbar Kotun Birnin Tarayya ta hana Shugaba Buhari da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, kara wa’adin amfani da tsoffin takardun Naira da aka sauya fasalinsu.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Eleoje Enenche ya kuma hana daukacin bankuna da ke Najeriya yin duk wata hulda da ta danganci tsoffin takardun kudin ko neman kara wa’adin amfani da su daga ranar 10 ga watan 10 ga watan Fabrairu da muke ciki.

Da yake sauraron ƙarar da wasu biyar daga cikin jam’iyyun siyasa 18 da ke Najeriya suka shigar, alkalin ya bukaci shugabannin bankuna da jami’ansu su kawo dalilan da za su hana a kama su da kuma gurfanar da su a gaban kotu kan zargin su da yin zagon kasa ga tattalin arziki, bisa yadda suke boye sabbin takardun Naira 1,000 da N500 da kuma N200 da CBN ya sauya wa fasali ya kuma ba su, amma suke kin ba wa mutane.

(AMINIYA)

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Ahmed Lawan A Matsayin Dan Takarar Sanata Na Yobe Ta Arewa

Kotun koli a ranar Litinin ta tabbatar da Ahmed Lawan, shugaban majalisar dattawa a matsayin dan takarar sanata na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Yobe ta arewa.


A wani hukunci mafi rinjaye da mai shari’a Centus Nweze ya yanke, kotun kolin ta amince da daukaka karar da jam’iyyar APC ta shigar kan takarar Bashir Machina.

Hukuncin da mafi rinjayen alkalai uku suka yanke wa 2, ya yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta Abuja ta yanke a ranar 28 ga watan Nuwamba, 2022, ta tabbatar da Bashir Sherrif Machina a matsayin dan takarar sanata na jam’iyyar APC na jihar Yobe ta Arewa a zabe mai zuwa.


Sai dai mai shari’a Adamu Jauro da Emma Agim sun nuna rashin amincewa da hukuncin da aka yanke, wanda hakan ya sanya suka yanke hukuncin watsi da karar da jam’iyyar APC ta shigar tare da tabbatar da sakamakon binciken da kotunan da ta shigar da kara suka yi.


Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa Mai shari’a Monica Dongban-Mensen, wacce ta jagoranci kwamitin mutane uku na kotun daukaka kara, ta bayyana hakan ne a wata daukaka kara da jam’iyyar APC (mai daukaka kara) ta shigar inda take kalubalantar hukuncin da mai shari’a Fadimatu Aminu ta babbar kotun tarayya da ke Damaturu, ta yanke. a ranar 28 ga Satumba, 2022, ta ayyana Machina a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani da jam’iyyar ta shirya a ranar 28 ga Mayu, 2022.


Sai dai tun bayan da Bola Tinubu ya lashe zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, jam’iyyar ta zabi Lawan ne domin maye gurbin Machina.

Amma Machina ya dage cewa ba zai janye wa Shugaban Majalisar Dattawa ba.

A yayin da ake fuskantar cece-kuce, jam’iyyar APC ta mika sunan shugaban majalisar dattawa ga hukumar zabe mai zaman kanta a matsayin dan takararta na Sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa.

Sakamakon rashin gamsuwa da hukuncin da jam'iyyarsa ta yanke ba, Machina ya garzaya kotu domin neman hakkinsa.

Machina a cikin karar sa, ya bukaci kotu da ta bayyana shi a matsayin zababben dan takarar sanata na jam’iyyar APC mai wakiltar Yobe ta Arewa.

Mai shari’a Aminu ya soke zaben fidda gwanin da aka yi wanda ya samar da Lawan a ranar 9 ga watan Yuni, 2022, inda ya dage cewa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC ya gudanar da sahihin zaben fidda gwani a ranar 28 ga watan Mayu, wanda Bashir Sheriff Machina ya lashe.

Don haka ne alkalin kotun ya umarci APC da ta mika sunan Machina ga INEC a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na jihar Yobe ta Arewa.

Sunday, 5 February 2023

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Jigawa ya amince da nadin Sabon Sarkin Dutse

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya amince da nadin Muhammad Hameem Nuhu Sanusi a matsayin sabon sarkin Dutse.

Kadaura24 ta rawaito Sanarwar amincewa da nadin na dauke da sa hannun kwamishinan aiyukan na musamman na jihar Jigawa Auwalu D Sankara,wadda kuma aka rabawa manema labarai.


Nadin ya biyo bayan zaben Masu Zaben Sarki na Masarautar Dutse su bakwai suka yi wa Hameem daga cikin masu neman kujerar sarautar har su su uku.

 Majalisar Sarakunan Jihar Jigawa ta amince da zaben, sannan kuma nadin sa ya fara aiki daga ranar 5 ga Fabrairu, 2023.

 Sabon Sarkin dai ya gaji Mahaifinsa ne Alhaji Nuhu Muhd Sanusi II wanda Allah ya yiwa rasuwa a makon daya

Saturday, 4 February 2023

Hajj2023: Hukumar NAHCON Ta Bawa Kano Kujerun Hajji 2,902

Rabon ya kasance kamar haka:

Abia 53

Adamawa. 2669

Anambara. 39

Bauchi. 3, 132

Bayelsa. 35

Binuwai. 236

Borno. 2,735

Cross Rivers. 66

Delta 74

Nassarawa. 1,567

Nijar. 5,165

Ogun. 1,139

Ondo 436

Osun. 1,054

Oyo. 1 441

Yobe. 1,968

Ebony 117

Edo 274

Ekiti. 197

Enugu. 40

FCT 3,520

 

 

Gombe. 2,301

Imo. 30

Jigawa. 1,525

Kaduna. 5982

Kano. 5,902

Katsina. 4,913

 

Kebbi. 4871

Kwara. 3,219

Legas. 3,576

Plateau. 1,984

Rivers. 50

Sokoto. 5,504

Taraba. 1,590

Za a saki jihar Kogi ne bayan kammala nazarin ayyukanta yayin da aka dakatar da rabon jihar Akwa Ibom saboda rashin sabunta lasisin aiki.

A halin da ake ciki, ana sa ran dukkan jihohin za su mika wa Hukumar biyan kashi 50% na kudin kujerun 2022 kafin ranar 10 ga watan Fabrairu. 

Rashin yin hakan ka iya sanyawa a rage yawan adadin kujerun da aka bawa jahar 
 

 

HANNU

Mousa Ubandawaki

Mataimakin Daraktan Labarai da wallafe-wallafe

NAHCON, Abuja

Friday, 3 February 2023

Gwamnoni Sun Roki Buhari A Ci Gaba Da Amfani Da Tsoffin Kudi

 


Gwamnonin Jam’iyyar APC sun bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa baki a ci gaba da amfani da tsofaffi da kuma sabbin takardun kudi.

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ne ya bayyana hakan bayan ganawar sirri da suka yi da shugaban kasa a Abuja.

Ya ce yayin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya karbi sama da Naira tiriliyan biyu na tsofaffin kudi, amma iya Naira biliyan 300 kacal ya iya bugawa wanda a cewarsa hakan ba zai wadatar da mutane ba.

El-Rufai, wanda ya samu rakiyar takwaransa na Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce kamata ya yi CBN ya buga akalla rabin abin da suka tara.

Ya ce gwamnonin jam’iyyar sun shaida wa shugaban kasa wawahalar da talakawa ke sha, da asar kayayyaki da ’yan kasuwa ke yi saboda rashin samun masu sayen kayansu.

Ya ba da misali da yadda masu sayar da tumatur suka je Legas da kayansu amma suka lalace saboda mutane ba su da kudin saye.

El-Rufai ya ce gwamnonin sun roki shugaban kasa da ya sake duba halin da ake ciki.

Ya kara da cewar shugaban gamayyar gwamnonin, Atiku Bagudu, ya sake ganawa da shugaban kasa shi kadai don jan hankalinsa kan bukatar janye dokar daina amfani da tsofaffin kudi.

A nasa bangaren, Gwamna Ganduje, ya ce shugaba Buhari ya yi alkawarin duba bukatarsu.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

SAPZ Kano partners ABCOAD to organize FFS Training for Youth and Women.

The Special Agro-Industrial Processing Zones (SAPZ) Programme, Kano State, in collaboration with Audu Bako College of Agricultur...