Search This Blog

Tuesday, 24 January 2023

Babu Gudu Ba Ja Da Baya Kan Wa’adin Tsofaffin Kudade – Emefiele

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya ce babu gudu babu ja da baya kan wa’adin daina karbar tsofaffin takardun kudade a ranar 31 ga watan da muke ciki.

Emefiele ya jaddada kudurin babban bankin na daina amfani da kudade a ranar Talata a Abuja.

Mun lalata miyagun kwayoyi na N95bn a Kwatano – NAFDAC
‘An kashe ’yan sa-kai 1,773 a rikicin Boko Haram a Arewa maso Gabas’
Ya ce “Ba ni da wani sabon labari ga wadanda suke so a tsawaita kwanakin daina karbar tsofaffin takardun kudade.

“Mutane sun tara kudade a gidajensu kuma suna sane da cewar ba su da lasisin yin hakan.”


Ya ce CBN ya samu nasarar karbar sama da tiriliyan 1.5, kuma yana sa ran cimma tiriliyan 2 kafin wa’adin ya cika a karshen watan nan.

Ya ce “Mun roki Hukumar Yaki Da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Zangon Kasa (EFCC) da Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa (ICPC) da kada su musgunawa kowa kan mika tsofaffin kudaden bankuna, kuma saboda ni sun tabbatar da min ba za su yi komai ba,” in ji shi.

Wannan dai na zuwa ne bayan da jama’a da dama ke korafin cewar wa’adin da CBN ya bayar na daina amfani da tsofaffin kudaden ya yi kadan, inda mutane suke tsimayin a kara wa’adin.
(AMINIYA) 


Monday, 23 January 2023

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Gurfanar Da Tukur Mamu

Wata Babbar Kotu a Jihar Kaduna, ta bayar da umarnin gurfanar mawallafin Jaridar Desert Herald, Alhaji Tukur Mamu a gaban kuliya.

Kotu ta nemi Hukumar Tsaro ta Farin Kaya reshen Jihar Kaduna (SSS) da kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami da su gaggauta gurfanar da Mamun ne tare da wasu mutum biyar.

Everton ta kori Frank Lampard
An tsaurara matakan tsaro a Legas gabanin ziyarar Buhari
Bayanai sun ce ababen zargin da kotun ta nemi a gurfanar da su bisa ga madogara ta binciken da aka yi a kansu sun hada; Tukur Mamu, Faisal Tukur Mamu, Ibrahim Hussain Tinja, Abdullahi Mashi, Mubarak Hussain Tinja da Yahaya Bello.

Da yake zartas da hukunci kan karar mai dauke da kwanan watan 15 ga Disambar 2022, Alkakin Kotun Mai Shari’a E. Andow, ya ce Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya yi tanadin bai wa duk wani wanda ake zargi ’yancin gurfanar da shi a gaban kuliya hadi da tuhume-tuhume da masu kara za su gabatar.


Umarnin kotun na zuwa ne watanni bayan da jami’an tsaron kasa da kasa na Interpol suka cafke tsohon mai shiga tsakanin gwamnati da ’yan ta’adda a kokarin kubutar da fasinjojin jirgin kasan nan na Abuja zuwa Kaduna da aka sace a watan Maris na bara.

A watan Satumbar bara ne aka kama Mamu a birnin Alkahira na kasar Masar yayin da yake jiran jirgi domin tafiya kasar Saudiyya inda zai gabatar da aikin Umrah

Mutane biliyan biyar ka iya kamuwa da bugun zuciya a duniya


Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce, kimanin mutane biliyan biyar na fuskantar gagarumin hatsarin kamuwa da ciwon zuciya saboda cin abinci mai dauke da kitse da ta bayyana amatsayin gubaL

A shekarar 2018 ne, Hukumar Lafiyar ta Duniya ta yi roko da a kawar da cimakar da ke dauke da kitse ganin yadda mutane dubu 500 suka yi mutuwar-farar-daya a sassan duniya sakamakon wannan cimakar.

WHO ta ce, kasashen duniya 43 da ke dauke da jumullar mutane biliyan 2 da miliyan 800, sun dauki matakin daina kalace da irin wannan cimakar a kasashensu, amma har yanzu akwai mutanen duniya kimanin biliyan biyar da aka gaza ba su kariya a sassan duniya.

WHO ta ce, Masar da Australia da Koriya ta Kudu, na  cikin kasashen duniya da suka yi watsi da gargadinta duk da cewa, su ke kan gaba a jerin kasashen da aka fi samun masu kamuwa da ciwon zuciya skamakon yawan cin abinci mai kitse.

Ana yawan cakuda wannan kitsen a cikin cimaka daban-daban da suka hada da man girki da abincin gwangwani da wasu kunsassun kayan kwalama.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, irin wannan kitsen na dauke da sinadarin guba mai kisa , kuma ya kamata a daina amfani da shi a abinci.

Kamfanoni dai na sanya kitsen ne da zummar hana abinci lalacewa da wuri, sannan yana da saukin samu fiye da sauran sinadarai masu kara wa abinci tsawon wa’adin lalacewa.

(RFI)

Bayan Ficewa Daga Tafiyar Tinubu, Naja’atu Ta Koma Wajen Atiku

 


Fitacciyar ’yar siyasar nan ta Jihar Kano kuma daya daga cikin tsofaffin Daraktocin kamfen din dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, Naja’atu Muhammad, ta koma wajen dan takarar PDP, Atiku Abubakar.

Matakin nata na zuwa ne ’yan sa’o’i bayan ta sanar da ajiye mukamin na Tinubu, tare da ayyana ficewarta daga jam’iyyar mai mulki.

Ta tabbatar da hakan ne yayin ziyarar da ta kai wa Atiku a gidansa ranar Lahadi.

Daga bisani dai ta shaida wa Aminiya cewa yanzu tana goyon bayan takarar ta Atiku a zabe mai zuwa.

A baya dai, Naja’atu, wacce ita ce Daraktar Kungiyoyin Fararen Hula a Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu, ta ce za ta gana da ’yan takarar jam’iyyun siyasa kafin ta dauki matsaya kan wanda za ta mara wa baya.

Ta ce ta dawo daga rakiyar Tinubu ne saboda a cewarta, sam ba ya iya yin tunani da kansa.

Ta ce, “Gaskiya ne yanzu ba na yin Tinubu, dalili ke nan ma da na bar jam’iyyar. Abubuwa da dama sun faru, da kyar yake iya tunani da kwakwalwarsa. Wannan ko shakka babu, mai musu kuma ya je ya nemi bidiyonsa ya kalla.

“Ni ba na la’akari da bambancin addini ko kabilanci a siyasa, shi ya sa tunanina ya fadada. Lokaci ya yi da ya kamata mu ajiye son zuciya mu ciyar da kasarmu gaba. Ba zai yiwu mu ci gaba da tafiya a haka ba. Dalilina ke nan, amma ba ni da wata nifaka a kan kowa,” in ji ta.

Sunday, 22 January 2023

Naja’atu Muhammad Ta Bayyana Dalilin Ficewa Daga Jam’iyyar APC

Fitacciyar ’yar siyasar nan ta Jihar Kano, Hajiya Naja’atu Muhammad, ta fice daga jam’iyyar APC mai mulki a kasar yayin da Babban Zabe ya karato.

Hajiya Naja’atu ta sanar da hakan ne cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 19 ga Janairun 2023, wadda ta aike wa Shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu.

’Yan sanda sun yi ajalin wani mutum a Kano
Wainar da aka toya a haduwar ‘karshe’ tsakanin Messi da Ronaldo
Naja’atu wadda yanzu haka Kwamishina ce a Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan sanda a Najeriya, ta ce kalubalen da kasar nan ke fuskanta a yanzu ya sanya dole ta fito daga takunkumin duk wata jam’iyya don ta shiga gwagwarmayar kai kasar nan zuwa tudun tsira.

A wata sanarwa da fitar a wannan Asabar din, Naja’atu ta ce duk jam’iyyyu a fadin kasar nan ba su da wani bambancin akida.


Ta bayyana ta cewa jam’iyyun kasar kamar tufafi mabanbanta da ’yan siyasa sukan saka don wata bukata ta kansu kebantacciya.

’Yar siyasar ta ce ta mayar da hankali wurin goyon bayan jama’a da ke da burin shawo kan matsalar kasar nan tun daga tushe a Najeriya.

“Watsi da siyasar jam’iyyu a wannan lokacin yana daya daga cikin wadannan matakan.

“Kowa ya san cewa Najeriya tana fuskantar kalubale daban-daban da suka hada da rashin tsaro, talauci, rashin daidaito da rashin samun ababen more rayuwa.


“Wadannan kalubalen suna bukatar namijin kokari daga jajirtattun shugabanni masu kishin kasa a dukkan matakan gwamnati.

“Dole ne ’yan Najeriya sun san cewa akwai yiwuwar shiga matsanancin hali bayan sun kori shugabanni da suka gaza a kasar nan a cikin shekarun da suka wuce.

“Dole ne ’yan Najeriya sun san abinda hukuncinsu da zabinsu zai iya haifarawa. Don haka, ajiye zabin ka a jam’iyya daya na iya zama hatsari ga ci gaban kasar mu da dimokuradiyyarmu.

“A matsayina na ’yar Najeriya da ke da kishin kasa, a yanzu na mayar da hankali wurin gwagwarmayar tabbatar da adalci da kuma samar da daidaito a tsakanin al’umma.


“Ina da yakinin cewa duk ’yan Najeriya sun cancanci rayuwa mai aminci,”a cewar Naja’atu.
(AMINIYA) 


Zan Kammala Aikin Tashar Jiragen Ruwa Ta Baro Idan Kuka Zabe Ni – Atiku

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi alkawarin kammala aikin tashar jiragen ruwa ta Baro da ke Jihar Neja, muddin aka zabe shi a zabe mai zuwa.

Atiku ya kuma ce jam’iyyarsa ce kawai take da siddabarun da za ta magance kalubalen tsaro da ya addabi kasar, musamman ma Jihar Neja.

Burkina Faso ta ba sojojin Faransa wata daya su fice daga kasarta
Ya yi wadannan alkawuran ne lokacin da yake jawabi ga wasu kusoshi da magoya bayan jam’iyyar a Minna, babban birnin Jihar Neja ranar Asabar.

Atiku ya ce PDP ce ta faro aikin na Baro rimi-rimi lokacin da take mulki, amma APC na zuwa ta yi watsi da shi.


A cewar tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, “Muna addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya a Jihar nan. Kun san PDP ce kawai za ta iya dawo da zaman lafiya a Neja. Lokacin da take mulki daga 1999 zuwa 2015, akwai matsalar tsaro a Neja? Muna so mu tabbatar muku cewa muddin PDP ta dawo, matsalar za ta zama tarihi.

“Muna kuma so mu tabbatar muku cewa aikin tashar Baro da PDP ta fara, amma aka yi wasti da shi lokacin da kuka bukaci canji, yanzu kun ga canjin ko? Me suka canza? Matsalar tsaro, tsadar rayuwa ko matsin tattalin arziki?

“Muna rokonku ku dawo PDP saboda ingantuwar al’amuran tsaro da ci gana Jihar Neja da ma na Najeriya baki daya,” in ji Atiku.

Shi ma a nasa jawabin, Shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, wanda ya karbi tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar, Ahmad Musa Ibeto da dubban magoya bayansa, ya ce Allah Ya albarkaci Jihar da dimbin ma’adinai.

Amma abin takaici, duk da wadanna tarin ni’imomin, APC ta mayar da ita hedkwatar talauci da rashin zaman lafiya. Akwai lokuta da ma wasu sassan wannan Jihar suka koma karkashin ’yan bindiga. Idan kuka zabe mu, za mu kawo ci gaba mai amfani,” in ji Ayu.

Saturday, 21 January 2023

CBN Ya Zargi Bankuna Da Boye Sabbin Takardun Kudade


Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zargi wasu bankuna da yi masa zangon kasa ta hanyar boye sabbin takardun kudade tare da ci gaba da bayar da tsofaffi.

Hakan na zuwa ne yayin da ya rage kwana 10 a daina amfani da tsofaffin kudaden kwata-kwata a kasar nan.

Babban Jami’in bankin a Jihar Ribas, Maxwell Okafor, ne ya yi zargin a Fatakwal, babban birnin Jihar lokacin da ya jagoranci ayarin CBN yayin ziyarar duba yadda bankuna da kasuwannin Jihar ke ta’ammali da sabbin kudaden ranar Juma’a.

Ya ce tsakanin ranakun Alhamis da Juma’a kawai, CBN ya ba bankunan kasuwancin da ke jihar tsabar kudin da suka kai Naira biliyan hudu da rabi, inda ya nuna damuwa kan yadda har yanzu jama’a ba sa samun su.

Ya ce, “Mun jima muna sanya idanu a kan yadda ake ba da sababbin kudade, kuma abin da muka gano ba ya karfafa mana gwiwa.

“Mun ziyarci wasu bankuna, kuma daya daga cikinsu har yanzu yana bayar da tsofaffin kudi. Wasu injinan ATM dinsu kuma ba sa aiki, kuma mun ji cewar ko kafin mu karaso nan, CBN ya ba su sabbin kudaden.

“Wasu daga cikin bankunan sun karbi sabbin kudaden, amma sun je sun boye su.

“CBN na gargadin cewa akwai tsattsauran mataki ga duk bankin da ke boye kudaden yana ba wasu shafaffu da mai.

“Mun daina bayar da tsofaffin kudade tun da sababbin suka fito, don haka ban ga dalilin da zai sa ATM ya ci gaba da bayar da su ba,” in ji Babban Jami’in.

Shi ma Daraktan Tsara Manufofi na bankin, Emenike Chimele, ya ce ko shakka babu wasu daga cikin bankunan na kokarin yi wa CBN zagon kasa kan sabuwar manufar.

Idan za a iya tunawa, CBN ya tsayar da 31 ga watan Janairun 2023 a matsayin ranar da za a daina amfani da tsofaffin kudaden kwata-kwata a Najeriya.

Sai dai yayin da ya rage ’yan kwanaki kafin cikar wa’adin, har yanzu mutane ma kokawa kan karancin sabbin takardun, yayin da har yanzu bankunan da injinan ATM ke ci gaba da bayar da tsofaffin takardun.

(AMINIYA)

Friday, 20 January 2023

Wa’adin Tsofaffin Kudi: Mun Zuba Ido Mu Ga Yadda CBN Zai Kare Da Mutanen Karkara —Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ce Babban Bankin Najeriya (CBN) bai sanya su cikin masu ruwa da tsaki ba kan batun sauya fasalin takardun kudi, dalilin ke nan da suka zuba ido su ga yadda zai kare da mutanen karkara idan wa’adin karbar tsohuwar naira ya cika.

Sarkin ya bayyana hakan ne yayin karbar bakuncin Babban Jami’in Gudanarwa na CBN shiyyar Sakkwato, Dahiru Usman hadi da wasu jami’an babban bankin ranar Alhamis a fadarsa.

Alhaji Bako Zuntu ya riga mu gida gaskiya
Duk da gargadin CBN har yanzu bankuna na bai wa mutane tsohuwar naira ta na’urar ATM
Abubakar ya ce kamata ya yi a ce CBN din ya sanya dukkanin masu ruwa da tsaki tun a matakin farko na sauya takardun na naira, amma sai ya yi biris da sarakunan gargajiya.

“Akwai mutanen karkarar ma da ba su san an sauya kudin ba kwata-kwata, kuma idan ka ba su sabo ba za su karba ba saboda za su zaci na bogi ne.

“Mu ne muke kusa da su, mu ne kuma ke da hanyoyin isar musu da sakon, don bibiyar kafafen yada labarai ba dabi’ar mutanen karkara ba ce.

“Amma da muka ga ba a saka mu a lamarin ba, sai muka koma gefe mu ga yadda za a kare idan wa’adin karbar tsofaffin kudin ya cika.

“Duk da haka muna rokon CBN ya kara duba wa’adin da ya bayar, domin rashin tsaro na daga cikin dalilan da suka sa mazauna karkara ke tsoron dibar kudi masu yawa su kai bankuna, gudun yi musu fashi a hanya ko ma sace su gaba daya,” in ji shi.

A nasa bangaren, Babban Jami’in na CBN ya ce sun kawo ziyarar ce domin sanar da Sarkin a hukumance cewa an sauya takardun kudin, da kuma neman shawarwarinsa.

Ya kuma yi alkwarin isar da sakon Sarkin ga shalkwatar CBN din da zarar sun kammala zagayen duba yadda bankuna a jihar ke bayar da sababbin takardun kudin da suka je yi.

Gwamnatin Najeriya Ta Kara Farashin Man Fetur

Gwamnatin Najeriya ta ƙara farashin man fetur a hukumance da kashi 8.8 inda a halin yanzu farashin ya koma naira 185 daga 170.

Shugaban masu gidajen mai masu zaman kansu reshen Jihar Kano Bashir Danmallam ya tabbatar wa BBC da ƙarin inda ya ce sun samu umarni daga gwamnatin tarayya.

Sai dai dama tun kafin gwamnatin Najeriya ta yi wannan ƙarin farashin tuni wasu gidajen mai a Najeriya suke sayar da man a farashin da ya fi na hukuma.

Akwai masu sayarwa kan 190 har zuwa 350 a wasu jihohi da ke faɗin ƙasar.

Kafin yin wannan ƙarin, akwai gidajen mai da dama a fadin Najeriya waɗanda ba su iya sayar da mai saboda ƙarancinsa.

Ƙarin farashin dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ministar kuɗi ta Najeriya Zainab Ahmed ta tabbatar da cewa akwai yiwuwar a soma cire tallafin man fetur daga watan Afrilu.

Makomar tallafin man fetur a Najeriya bayan Yunin 2023
5 Janairu 2023
Amfani biyar game da samun man fetur a Arewacin Najeriya
23 Nuwamba 2022
Akwai yiwuwar cire tallafin man fetur a ƙasar sakamakon kusan duka ƴan takarar shugabancin Najeriyar sun lashi takobin cire tallafin fetur ɗin inda suka ce ba su ga amfaninsa ba.

Farashin makamashi a Najeriya dai ya yi tashin gwauron zabi ne tun a bara jim kaɗan bayan soma yaƙin Ukraine.

Farashin man dizal wanda ake amfani da shi wurin dakon man fetur sai da ya kai kusan naira dubu a kowace lita, wanda hakan ya sa masu sayar da mai suke kasa zuwa Legas domin su yi dakon fetur É—in.

Haka ma farashin gas É—in girki shi ma sai da ya kai har naira dubu goma a duk tukunya mai nauyin kilo 12.5
(BBC HAUSA) 

Thursday, 19 January 2023

Emeifele Ya Sake Kaiwa Buhari Ziyara A Sirrance

 


Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin  Emefiele, ya shiga bayan labule tare da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Fadar Gwamnatin Najeriya ta Aso Villa da ke Abuja.

Bayanai sun ce wannan dai ita ce ziyara ta biyu kuma cikin sirri da Gwamnan Babban Bankin Kasar ya kai wa Shugaba Buhari tun bayan dawowarsa Najeriya a ranar 12 ga watan Janairu.

Wannan ziyara na zuwa ne bayan Emefiele ya halarci taron Bankin Bunkasa Tattalin Arziki na Daular Larabawa wanda Darekta Janar na bankin, Dokta Sidi Ould Tah ya jagoranta a ranar Alhamis.

Tun a bara dai labarin Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya soma yamutsa hazo bayan da aka rika rade-radin cewa jami’an tsaron na sirri na nemansa ruwa a jallo.

A makonnin bayan nan ne dai Emefiele ya bar kasar biyo bayan binciken wasu zarge-zarge da ake yi masa, da suka hada da cin hanci da rashawa da kuma samar da kudade ga ayyukan ta’addanci.

Sai dai tuni CBN ya kore wannan zargi yana mai cewa Emefiele ya ketare kasar nan saboda dalilai na hutun karshen shekara da doka ta ba shi dama.

Gabanin wannan dai, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta nemi wata Babbar Kotun ta sahale mata cafke Emefiele, amma Alkalin kotun, M.A. Hassan ya yanke hukuncin sanya shamaki tsakanin DSS din da Emefiele.

(AMINIYA)

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Presidential delegation pays condolence visit to Hamza Darma’s family in Kano

A high-powered presidential delegation has paid a condolence visit to the family of late Alhaji Hamza Usman Darma, a prominent K...