Shugaban Hukumar NAHCON Ya Bayyana Cigaban Da Ya Samar Cikin Kwanaki 100, Ya Bukaci Maniyyata Su Ba Da Hadin Kai – Daga Nura Ahmad Dakata
Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana muhimman nasarorin da hukumar ta samu a karkashin jagorancinsa a cikin kwanaki 100 na farkon jagorancinsa
A wata tattaunawa ta musamman da wakilinmu a Kano Farfesa Sale Usman, ya jaddada muhimmancin koyi da shugabancin da ya gabata, inda ya ce, “A rayuwa duk wanda ya riga ka mulki, ko ya yi kura-kurai, ko ya yi nasara, sai ka yi addu’a Allah ya karba nasa ayyukan alheri kuma ya gafarta masa kurakuransa. Muna yin iya kokarinmu a yanzu kuma muna addu’ar Allah Ya taimakemu mu ci gaba da tafiya kan hanya madaidaiciya”.
Ya kuma bayyana cewa shugabancinsa yana daukar darasi daga ayyukan magabata, da amfani da nasarorin da suka samu da kuma gujewa kura-kuransu.
Da yake yin tsokaci kan hakan, ya ce, “A cikin kwanaki 100 da muka yi muna shugabanci, mun cimma yarjejeniya da kamfanonin jiragen sama na rage farashin tikitin jirgin sama idan aka kwatanta da wanda aka biya a bara. Mun kuma amince da yadda za a rika biyan kudin a Naira maimakon Dalar Amurka, wanda hakan wani gagarumin ci gaba ne.”
Farfesa Sale Usman ya bayyana wata babbar nasara: karbo sama da naira biliyan biyar na ayyukan da ba a yi wa maniyyata aikin hajjin 2023 ba daga hukumomin Saudia. Ya bayyana hakan ne a matsayin wani bangare na kokarin hukumar na tabbatar da bin doka da kuma kare muradun alhazan Najeriya.
Dangane da batun Fasfo da biza kuwa, shugaban hukumar ta NAHCON ya bayyana cewa hukumar na aiki kafada da kafada da hukumar kula da shige da fice ta kasa domin tabbatar da bayar da Fasfo na maniyyata a kan lokaci. Ya ce, “Suna ba mu haɗin kai, kuma muna samun ci gaba sosai a wannan batun.”
Day a juya kan batun tsarin biza, Farfesa Sale Usman ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa hukumomin Saudiyya sun shirya tsaf don magance matsalolin NAHCON. Ya yi nuni da cewa a yanzu babban abin da hukumar ta fi mayar da hankali a kai shi ne warware matsalolin da suka shafi takardar izinin Umrah. “Ta hanyar ofishin Ministan Harkokin Waje, mun gayyaci Ministan Hajji na Saudiyya zuwa Najeriya don magance duk wasu batutuwan da suka shafi Umrah,” inji shi.
Shugaban ya kuma yi kira ga masu niyyar zuwa aikin Hajji da su tabbatar da biyan kudin aikin Hajji a kan lokaci, yana mai jaddada cewa yin jirkirin biya yana kawo cikas ga tsare-tsare da manufofi. Ya yi kira ga masu irin wannan halayya da su daina domin a samu aiki mai inganci.
Da wannan kokari, Farfesa Abdullahi Sale Usman ya tabbatar da aniyar NAHCON na inganta aikin Hajji ga daukacin alhazan Najeriya, yayin da ya bukaci masu ruwa da tsaki da su goyi bayan ayyukan hukumar.