Search This Blog

Monday, 17 April 2023

Adadin mutanen da aka kashe a rikicin Sudan ya kusan 100

 


Kungiyar likitoci a Sudan, ta ce adadin wadanda aka kashe a fadan da ake cigaba da gwabzawa tsakanin sojojin kasar da jami’an tsaron rundunar musamman ta kai daukin gaggawa wato ‘Rapid Response’, ya karu zuwa mutane 97, cikinsu kuwa har da jami’an majalisar dinkin duniya uku.

Tun a ranar Asabar, rikicin ya barke bayan da aka kwashe makwanni ana takaddama tsakanin hafsan sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar rundunar dakarun RSF mai karfin fada a ji, wadda shugaba Burhan ke son narkar da ita zuwa cikin rundunar sojin kasar.

Kazamin fadan ya cigaba da yin kamari ne kuma duk da cewar bangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar tsagaitar wutar wucin gadi a ranar Lahadi, domin ba da damar bai wa wadanda rikicin ya rutsa da su kulawar gaggawa.

Likitoci sun ce daruruwan mutane ne suka jikkata, yayin da hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa kusan dukkanin asibitoci 9 da ke birnin Khartoum, basu da jini da kuma ruwa da marasa lafiya ke bukata.

Wani yankin birnin Khartoum, bayan shiga rana ta biyu a rikicin da ya barke tsakanin sojojin Sudan da dakarun rundunar musamman ta RSF. 16 ga Afrilu, 2023
Wani yankin birnin Khartoum, bayan shiga rana ta biyu a rikicin da ya barke tsakanin sojojin Sudan da dakarun rundunar musamman ta RSF. 16 ga Afrilu, 2023 AP - Marwan Ali

A halin da ake ciki hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya WFP da aka kashewa jami’ai uku, ta dakatar da ayyukanta a Sudan har sai abinda hali yayi.

Tuni dai kasashe da dama suka yi Allah wadai da gumurzun da ake yi tsakanin sojojin gwamnati da dakarun musamman na RSF, yayin da wasu kasashen kamar Chadi da Masar suka rufe iyakokinsu da kasar ta Sudan.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da takwaransa na Birtaniya James Cleverly, sun bayyana matukar damuwa game da kazamin fadan da suka bayyana a matsayin barazana ga makwaftan Sudan ba ma al’ummar kasar kadai ba.

Yau Litinin ake sa ran shugaban kungiyar Tarayyar Afirka AU, Moussa Faki Mahamat, zai isa kasar domin shiga tsakani da jagorantar kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

RFI

Mbappe Ya Karya Da Tarihin Da Cavani Ya Kafa A PSG

 


Kylian Mbappe ya zama dan wasan Paris Saint-Germain da ya fi zura kwallaye a tarihin babbar gasar tamaula ta Faransa wato Ligue 1.

Dan wasan mai shekaru 24 ya riga ya karya tarihin zura kwallaye a kungiyar a watan da ya gabata, lokacin da ya wuce Edinson Cavani, wanda ya ci wa PSG kwallaye 200 tsakanin 2013 da 2020.

Amma har zuwa karshen wannan makon, Cavani ya kasance wanda ya fi zura wa PSG kwallo a gasar Ligue 1.

Sai dai hakan ya sauya a minti 31 da soma wasan da PSG ta doke Lens da ci 3-1 a ranar Asabar lokacin da Mbappe ya yi wa kungiyar rajistar kwallonsa ta 139 a gasar Ligue 1.

Yanzu dai Cavani ne na biyu a jerin wanda ya zura kwallaye 138 a gasar Ligue 1, yayin da Zlatan Ibrahimovic ke matsayi na uku da kwallaye 113.

Kylian Mbappe ne ya fara cin kwallo a wasan kuma na 139 a wasa 169 da ya yi wa kungiyar.

Lens ta karasa karawar da ’yan wasa 10 a cikin filin, bayan da aka bai wa Salis Abdul Samed jan kati minti 19 da take leda.

Lens mai maki 63 ce ta biyu, sai Marseille ta uku da tazarar maki biyu tsakaninta da Lens.

Paris St Germain za ta ziyarci Angers ranar Juma’a 21 ga watan Afirilu, domin buga wasan mako na 32 a Ligue 1.

AMINIYA

INEC Za Ta Yi Taron Gaggawa Kan Zaben Adamawa

 


Hukumar Zabe ta Kasa INEC za ta yi taron gaggawa a yau Litinin kan dambarwar da ta dabaibaye tattara sakamakon zaben gwamnan Jihar Adamawa.

Tun a ranar Lahadi INEC ta umarci duk jami’anta da ke lura da zaben gwamna a Adamawa, da su kama hanyar zuwa Abuja domin yin wani taron gaggawa.

Wannan dai na zuwa ne bayan INEC ta bayyana dakatar da aikin tattara sakamakon zaben gwamna da aka karasa a ranar Asabar.

Aminiya ta ruwaito cewa, tun ana tsaka da tattara sakamakon zaben ne Kwamishinan INEC na Adamawa, Barista Hudu Ari, ya ayyana ’yar takarar gwamnan ta jam’iyyar APC, Sanata Aishatu Dahiru Binani a matsayin wadda ta yi nasar

Lamarin ke nen da ya sanya cikin wata sanarwar gaggawa da babban jami’inta kan yada labarai da wayar da kan masu zabe na kasa, Barrista Festus Okoye ya fitar, INEC ta ce matakin da kwamishinan zabe na Jihar Adamawa ya dauka na sanar da wanda ya lashe zaben haramtacce ne, don haka ta ce ba za a yi amfani da shi ba.

Sanarwar ta ce kawo yanzu ba a kammala tattara sakamakon zaben gwamnan Jihar Adamawa ba.

Hukumar INEC ta gudanar da cikon zaben gwamnan Jihar Adamawa ne a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, bayan ta ayyana zaben da aka yi a makonnin da suka wuce a matsayin wanda bai kammala ba.Gwamna Ahmadu Umar Fintiri na jam’iyyar PDP shi ne ke kan gaba bisa alkaluman da INEC ta sanar kawo yanzu, yayin da Aishatu Dahiru Binani ta jam’iyyar APC take bi masa a yawan kuri’u.

An wayi gari Lahadi a Jihar Adamawa cikin wani yanayi na dakon sakamako da rudani.

Tun da farko dai INEC ta dage aikin tattara sakamakon zaben a ranar Asabar, bayan karbar sakamakon zaben cike-gibi da aka yi cikin wasu tashoshin zabe na kananan hukumomin jihar 20.

A ranar Asabar da daddare, jami’in sanar da sakamakon zabe, ya bayyana sakamakon da aka samu a kananan hukumomi guda goma.

Sai dai da misalin karfe 10 na safe, sai babban jami’in INEC wato Barista Hudu Ari, ya shiga zauren tattara sakamakon zaben a Yola tare da rakiyar wasu sun rufa masa baya, inda ya ayyana Sanata Aishatu Binani ta APC a matsayin wadda ta lashe zaben.

Bai dai yi bayani filla-filla na sakamakon da kowacce jam’iyya ta samu da kuma yadda aka ci zaben ba.

Wakiliyarmu ta ruwaito cewa yana gama bayyana nasarar Binani ya kama hanya filin tashi da saukar jirage zai bar gari.

AMINIYA

Sunday, 16 April 2023

Yanzu-Yanzu :Hukumar INEC Ta Ce Ba Ta Amince Da Yadda Aka Bayyana Sakamakon Zaben Gwamnan Adamawa Ba, Inda Ta Gayyaci Dukkanin Masu Ruwa Da Tsaki Don Warware Matsalar

An ja Hankalin hukumar zabe Mai zaman kanta ta Kasa kan  sanarwar da hukumar zabe ta jihar Adamawa ta yi wacce ta jawo cece-kuce na cewa Aisha Binani ya lashe zaben gwamnan jihar ko da a fili ba a kammala aikin ba.

A cewar Barrister Festus Kayemo, kwamishinan yada labarai na hukumar, yace Matakin da kwamishinan zaben ya dauka kuskure ne babba  na ikon Jami'in fadar sakamakon Dawowa. 

Saboda haka, an dakatar da tattara sakamakon zaben na wanda aka sake. Inda hukumar ke gayyatar gayyatar kwamishinan zaben da jami’in karbar sakamakon da duk wanda abin ya shafa zuwa hedikwatar Hukumar da ke Abuja nan take.

Cikakkun bayanai masu zuwa nan gaba kadan.


Labari Da Dumiduminsa : Hukumar INEC Ta Bayyana Aisha Binani A Matsayin Wacce Ta Lashe Zaben Gwamnan Adamawa

Hukumar Zabe Mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Aisha Dahiru (Binani) a matsayin wacce ta samu nasarar zaben Gwamnan Jahar Adamawa 

Saturday, 15 April 2023

Sojojinmu ne ke iko da muhimman wurare - shugaban Sudan

 


Janar Abdel Fattah al-Burhan, jagoran Sudan kuma babban hafsan hafsoshin sojin ƙasar ya musanta iƙirarin rundunar jami'ai masu kayan sarki ta RSF, cewa dakarunta ne ke iko da fadar shugaban ƙasa da hedkwatar sojoji da kuma filin jirgin sama.

A wani saƙon waya da aka naɗa lokacin hira da gidan talbijin na Al Jazeera, Janar al-Burhan ya dage kan cewa dakarunsa ne har yanzu ke da iko.

Ana ci gaba da samun rahotanni masu cin karo da juna game da abin da ke faruwa a tsawon wannan rana kan taƙamaimai wane ne ke iko da muhimman wurare a birnin Khartoum.

BBC

Alhassan Doguwa ya yi tazarce a karo na hudu

 


Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Tarayya Alhassan Ado Doguwa ya ci zabe a karo na biyar.

Baturen zaben da aka kammala a ranar Asabar, Farfesa Sani Ibrahim, ya ce Alhassan Ado Doguwa ya yi nasarar komawa kan kujerarsa ne bayan ya samu kuri'u 41,573 a yayin da dan takarar jam'iyyar NNPP, Yusha'u Salisu, ya zo na biyu da kuri'u 34,831.


Idan za a iya tunawa bayan zaben da aka gudanar ranar 25 ga watan Maris, INEC ta bayyana Doguwa a matsayin wanda ya yi nasara.


Amma daga bisani aka janye nasarar Doguwa bayan da baturen zaben, Farfesa Ibrahim Yakasai ya cewa tursasa masa bayyana sakamakon aka yi, don haka bai samu nutsuwar yin lissafin kuri'un da aka jefa yadda ya kamata ba, kasancewar rayuwarsa da ta ma'aikata na cikin hadari a lokacin.


Amma daga baya da aka yi lissafi aka gano zaben bai kammalu ba saboda kuri'un da aka soke sun zarce tazarar da ke tsakanin kuri'un Doguwar da na Yusha'u.


Hakan ne ya sa aka kammala zaben a yau, wanda Alhassan Ado Doguwa ya yi nasara.

Wednesday, 12 April 2023

Yadda jami'an tsaro suka tsare Peter Obi a London

 


Kwamitin yaÆ™in neman zaÉ“en shugaban Æ™asa na jam’iyyar LP ya ce jami’ai sun tsare tare da hantarar É—an takarar shugaban Æ™asa na jam’iyyar, Peter Obi a birnin London.

Mai magana da yawun kwamitin kamfe na jam’iyyar LP, Diran Onifade ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a filin jirgin sama na Heathrow da ke London.

Ta Æ™ara da cewa jami’an shige da fice na Birtaniya É—in ne suka titsiye tsohon É—an takarar shugaban Æ™asar.

Diran Onafide ya ce hukumomi a Birtaniya sun tsare tare da yin tambayoyi ga tsohon gwamnan na jihar Anambra kan wani lamari da ya shafi wani mutum da ke yin sojan-gona da suna Peter Obi.

Sanarwar ta Æ™ara da cewa jami’an sun sassauta wa Petetr Obi ne bayan wasu Æ´an Najeriya da ke a filin jirgin sun sanya baki.

Peter Obi dai ya isa birnin na London ne domin bukukuwan Easter na mabiya addinin Kirista.

Bayanin ya nuna cewa bayan saukar Peter Obi a filin jirgin na Heathrow da ke London, jami’an tsaro sun zo wurin sa a lokacin da yake kan layin tantancewa, tare da miÆ™a masa wata takarda da ke Æ™unshe da umurnin tsarewa, sannan suka buÆ™ace shi da ya fita daga layi.

Onifande ya ce jami’an sun yi wa Peter Obi tambayoyi na tsawon lokaci, wanda abu ne da ba a saba ganin ya faru ga wani mutum da ya kwashe sama da shekara 10 yana rayuwa a Æ™asar ba.

Sai dai mutane ƴan asalin Najeriya sun rinƙa ɗaga muryoyinsu domin sanin dalilin da ya sa aka tsare tsohon gwamnan.

Me ya sa aka tsare Obi?

Matakin da Æ´an Najeriya suka É—auka na tambayar dalilin da ya sa aka tsare Peter Obi a filin jirgin ya tursasa wa jami’an shige da ficen yin bayani kan musabbabin tsare shi.

Sun ce suna masa tambayoyi ne kan wani abu da ya jiɓanci sojan-gona.

Onifade ya ce illar sojan-gona ita ce akwai yiwuwar wanda ke sojan-gonar zai iya aikata laifukan da za a maƙala wa shi Peter Obi.

BBC

Majalisar Najeriya ta gayyaci ministoci kan bacewar gangunan danyen mai

 


Kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya da ke bincike kan zargin batar gangar danyen mai miliyan 48 a kasar ya gayyaci Ministocin Kudi da na Shari'a da wasu manyan shugabannin hukumomin kasar domin bayar da bahasi a game da wannan badakalar. 





Da yake magana kan rashin girmama gayyatar da kwamitin ta ya yi wa Ministocin Kudi da na Shari'a da wasu jami'an hukumomin gwamnatin kasar, Shugaban Kwamitin Binciken Hon. Mark Gbillah, ya ce ana zargin Ministar Kudi Zainab Ahmed da karya dokar gwamnati ta tsarin fallasa masu yi wa gwamnati zagon kasa ta hanyar kin biyan masu fallasawar adadin kudin da ya dace a ba su.  

Tun a watan Disamban shekarar da ta gabata ne Majalisar ta yanke shawarar fara bincike kan bantan miliyoyin gangar man, wadanda ake zargin wasu manyan jami'an gwamnatin kasar da karkatarwa zuwa China.    

Ya ce a daya bangaren kuma, ana zargin Ministan Shari'a na kasar da karbar kudade daga ketare ba tare da sanyawa cikin asusun gwamnati ba.   

Ya kuma bayyana cewa, kwamitin na da bayanan sirri na wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati da ba su bin ka'idar amfani da tsarin asusun ajiyar kudi na bai-daya.   

Sai dai bai bayyana ranar da jami'an gwamnatin za su bayyana a gaban kwamitin domin amsa tambayoyi ba. 

RFI

Tuesday, 11 April 2023

Buhari Zai Bar Najeriya Fiye Da Yadda Ya Same Ta – Fadar Shugaban Kasa

 


Fadar Shugaban Kasa ta ce a fannin tsaro da habaka tattalin arziki, Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Najeriya fiye da yadda ya same ta a 2015.

Kakakin Shugaban, Femi Adesina, ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da gidan talabijin na Channels ranar Talata.

Ya kuma ce karyata batun cewa a tsawon mulkin Buhari na shekara takwas, ya nuna kabilanci wajen nafin wadanda za su shugabanci hukumomin tsaron kasar nan.

A cewarsa, nadin nasu ba shi da wata alaka da addinin, yanki ko kabilar da mutum ya fito wajen nadinsu, an fi la’akari da cancanta tun da dai doka ta ba Shugaban ikon nada duk wanda ya ga dama.

Ya ce, “Ka san cewa akwai wani rahoto da ya ce an fi samun karancin mutanen da aka kashe a 2022 a cikin shekara 12 da suka gabata a sakamakon ayyukan ta’addanci? Mun fa sani a Najeriya cewa alkaluman sun ci gaba da sauka a tsawon shekaru.

“Babu wanda ke son a sami asarar rai, komai kankantarsa, amma idan aka ce an sami ragi a yawan mutanen da ake kashewa a kowacce shekara, ni ina ganin abin a yi farin ciki da shi ne.

“Buhari zai bar Najeriya fiye da yadda ya same ta a 2015, lokacin da Kananan Hukumomi 17 ke karkashin ’yan ta’adda. Hatta NYSC ba ta iya ba matasa masu yi wa kasa hidima horo a wadannan yankunan. Amma a yanzu fa?” in ji shi.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Head of Service Urges Civil Servants to Uphold Ethical Conduct

The Head of Service, Kano State, has called on civil servants to strictly adhere to the Civil Service ethical code and show grea...