Search This Blog

Monday, 27 March 2023

Hajj 2023: NAHCON, Hukumar Alhazai Na Jihohi Zasu Hada Gwiwa Don Zabar Masauki Masu Inganci

Gabanin bayyana kudin aikin Hajjin shekarar 2023, Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta dorawa Hukumomin Alhazai na Jihohi (SMPB) damar samun matsuguni masu inganci kawai domin rage kudin Hajjin 2023.

NAHCON ta bayyana haka ne a yayin wani taro tsakanin shugabannin hukumomin Alhazai na jahohi da masu samar da masauki da kuma masu aikin hajjin 2023 da aka zabo masu ba da abinci a karo na biyu kafin aikin hajji a ranar Lahadi a birnin Makkah na kasar Saudiyya.

“Eh, kwamishinan kudi na NAHCON wanda ya jagoranci taron ya roke mu da mu nemo masaukai masu inganci da ba shi da nisa da babban masallacin Makkah amma ya kamata a rage farashi.

‘’Farashin masauki a Makkah ya tashi saboda dalilai kamar haka: Masarautar Saudiyya ta fara rusa wasu gidaje da alhazan Najeriya ke amfani da su a baya don share fagen sabon shirinsu na ci gaba.

“Ba kamar a shekarar 2022 da mahajjata miliyan daya kacal suka yi aikin hajji ba, sama da mahajjata miliyan 3 ne ake sa ran za su yi aikin hajji a bana – wanda ke nufin karin yawan mahajjata da karancin masauki. Haƙiƙa, yana da ƙalubale a gare mu jahohi amma za mu yi aiki tuƙuru don ganin yadda za mu iya tafiya,” wata majiya mai ƙarfi ta shaida wa manema labarai na Hajji a Makkah.

Binciken da masu aiko da rahotannin alhazai suka yi ya nuna cewa a yanzu haka an ruguje akasarin  otal-otal da ke kan titin Hijra a Misfala yayin da wasu kuma hukumar masarautar Makkah da wuraren tsarki ta Saudiyya ta ruguza su.

Mahajjata daga jihohin Sokoto, Katsina, Kaduna, Bauchi, Kano, Kwara, Plateau da Niger suna karbar maniyyatan su ne a cikin garin Misfala ta hanyar Hijira da Ibrahim Khalil Road a Makkah.

An dage aikin duba masauki da kicin da aka shirya tun karfe 10:30 na rana zuwa karfe 5 na yamma agogon Saudiyya a yau.

Lokaci na duba ya canza saboda yawan zirga-zirga a kewayen Harami musamman bayan sallar tarawihi.
IHR

Saturday, 25 March 2023

Hajj2023: Tawagar Hukumar NAHCON Sun Gudanar Da Taron Cikin Gida A Yayin Ziyararsu Zuwa Makka

Tawagar Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) a yayin da suke kasar Saudiyya sun gudanar da taronsu na farko na cikin gida don a yayin ziyara kafin aikin Hajji karo na biyu a shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2023 a ofishin NAHCON dake Ummuljud Makka 

Tawagar tana da alhakin ayyuka kamar haka:

1) Duba dakunan dafa abinci na Makkah da Madina.
2) Tattaunawar kwangila tare da masu gudanar da ayyuka 
3) Don gudanar da tarurruka tare da AHOUN, Jihohi, Muassasah, masu ba da masu bayar da  masauki,
4) Horon E-track da 5) Rahoton ƙarshe ..

Taron ya gudana karkashin jagorancin Kwamishinan kudi Alhaji Nura Hassan Yakasai wanda shi ma ya jagoranci tawagar da ta samu rakiyar wakilan CBN da Jama’atu Nasril Islam da kwamishinan yankin Kudu
Daga cikin yan tawagar a taron: Sun hada da Daraktan Gudanarwa da HR, Darakta harkokin shari'a, Mataimakin Darakta PEO, sauran Daraktoci da manyan ma'aikatan gudanarwa.
NAHCON 

Monday, 20 March 2023

Sanata Uba Sani Ya Samu Nasarar Zama Gwamnan Kaduna

An bayyana dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Sanata Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kaduna a shekarar 2023.



Jami’in kula da masu kada kuri’a na jihar Kaduna kuma mataimakin shugaban jami’ar Usman Dan Fodio Sokoto, Farfesa Lawal Suleiman Bilbis ne ya bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.



Sani ya samu kuri'u 730,002 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa Isa Ashiru na jam'iyyar PDP wanda ya samu kuri'u 719,196.


Dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP), Jonathan Asake ya zo na uku mai nisa bayan ya samu kuri’u 58,283 yayin da dan takarar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Suleiman Hunkuyi ya samu kuri’u 21,405.

Sunday, 19 March 2023

Hukumar Zabe Ta Sanar Da Abba K Yusuf A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kano

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta bayyana Abba Kabir Yusuf na jam'iyar NNPP  a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano da aka kammala kwanan nan da kuri'u 1,019,602.

Thursday, 16 March 2023

Za Mu Kama Duk Wanda Ya Dauki Makami Ranar Zabe A Kano —’Yan Sanda

 


Mataimakin babban sufeto-Janar na ’yan sanda DIG Hafiz Muhammad Inuwa da ke kula da harkokin zaben shekarar 2023 a yankin jahohin Arewa maso Yammacin Najeriya, ya gargadi ’yan siyasa da magoya bayansu, da su kauce wa yin wani abu da zai tada hankulan masu zabe. 

DIG Hafiz M. Inuwa ya bayyana cewa shugaban ’yan sanda Usman Alkali Baba ya umarce su, da su gargadi ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki da su ja wa magoya bayansu kunne gabanin zaben da ke tafe a ranar Asabar 18 ga watan Maris 2023.

Ya bayyana hakan ne a Jihar Kano, a ci gaba da shirye-shirye da rundunar ke yi na tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyinsu.

Ya kara da cewa fatansu, shi ne a yi zabe lafiya a kammala lafiya, ba tare da nuna siyasa da gaba ba.“Duk wani dan siyasa in dai yana son ci gaban Kano, to zaman lafiya shi ne ci gaban, so ake a zauna lafiya.

“Kuma na zo da jawabi, in gargade su, Wallahi ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen maganin duk wani da ya nemi ya tada fitina,

“Saboda haka ina tabbatar muku da cewa duk wanda ya nemi ya dau makami ko don ya hana wani fitowa zabe, ko don ya jikkata wani, to Wallahi Tallahi fushin hukuma ne a tattare da shi” in ji shi.Ya ce ba zu raga wa kowa ba duk girmansa kowaye , domin ci gaban Nijeriya da ci gaban Kano da kuma zaman lafiya shi ne agaban mu.

Tun kafin wannan lokacin ne Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa sun tanadi ’yan sanda masu yawa don tabbatar da tsaro a zaben ranar 18 ga watan Maris 2023.

Sai Buhari Ya Yi Magana Za Mu Karbi Tsohon Kudi —’Yan Kasuwa


 ’Yan kasuwa a wasu yankunan Najeriya sun bayyana cewa ba za su fara karbar tsoffin takardun N5oo da N1,000 har sai sun ji Shugaban Kasa Muhamamdu da bakinsa ya ce su fara karba.

’Yan kasuwa da kwastomominsu jihohin Kaduna da Legas da kananan hukumomin Abaji da Kwali a Yakin Babban Birnin Tarayya na kin karbar tsoffin kudin ne, a washgarin da bankunan kasuwanci suka fara bayar da su, bisa umarnin Babban Bankin Najeriya (CBN).

Sai dai a Jihar Kano, harkokin kasuwanci sun fara komawa yadda aka saba, tun bayan da bankuna suka fara bayar da tsoffin kudi, kuma mutane suka ci gaba da amfani da su a harkokin kasuwanci.

Harkoki sun fara kankama a Kano

Wani tan kasuwa a Kasuwar Kantin Kwari da ke Kano, Adamu Hamza, ya ce sun fara samun karuwar ciniki,  “tsakanin jiya (Talata) da yau (Laraba), kudi ya fara yawo a hannun jama’a, suna kawowa kuma muna karba.”

Aminiya ta ruwaito cewa tun ranar Talata injinan ATM a birnin Kano suka fara bayar da tsoffin kudin, sai dai yawanci N500 ne.

Haka kuma an samu raguwa mutane da ke neman cirar kudi, dai dai wasu bankunan sun bayyana cewa tsabar kudin da ke hannunsu  ya kare, shi ya sa ba a ganin layin mutane a ATM dinsu domin cirar kudi.

‘Sai mun ji daga bakin Buhari’

Aminiya ta zaiyarci yankin Abaji a ranar Laraba, inda ta iske mutane na ta gunaguni cewa bankuna sun koma ba wa mutane tsoffin takardun kudin.

Wani dan kasuwa, Bashir Aliyu, ya yi mana korafin cewa ya ce cikin banki cirar kudi , amma aka ba shi tsoffin takardun N1,000 da aka sauya, amma ya ki karba, sabo ba zai iya kashe su cikin sauki ba, idan ya je kasuwannin kauye.

A cewarsa, duk da cewa CBN ya ba umarnin bankuna su ci gaba da harkokinsu da tsoffin kudin, shi ba zai samu natsuwa ba sai sai ya ji Shugaba Buhari da kansa ya yi wa ’yan kasa magana cewa su ci gaba da amfani da tsoffin kudin.

Wani jami’in banki da ya nemi mu boye sunansa ya shaida mana cewa bankin ya fito da Naira dubu 500 na tsoffin takardun kudi da yake da su domin ba wa mutanen da suka zo cirar kudi, amma yawancin mutanen sun ki karba.

“A takaice, daga cikin N500,000 da bankin ya fitar domin ba wa kwastomomi N150,000 kadai aka samu wadanda karba,” in ji jami’in bankin.

Hakazalika wasu ’yan kasuwa a yankin Kwali na kin karbar tsoffin kudin, saboda har yanzu ba su ji Shugaba Buhari ya yi magana a kai ba.

Wata ’yar kasuwa mai suna Misis Laraba Gwatana ta ce, “Ni ba zan karbi tsohon kudi ba, saboda har yanzu rade-radi muke ji cewa CBN ya umarci bankuna su koma bayar da tsoffin kudaden.

“Amma ni dai ba zan karbe su ba, sai lokacin da na ji Buhari ya fito ya yi wa ’yan Najeriya jawabi cewa su rika karbar tsoffin kudin; gaskiya ba wanda ke so ya kara yin asara.”

’Yan kasuwa kaduna ma haka

Zuwa ranar Laraba, ’yan kasuwa da dama a Jihar Kaduna na kin karbar tsoffin takardun N500 da N1,000 a Kasuwar Sheikh Gumi, inda suke bayyana fargaba kan batun amfani da tsoffin kudaden.

Wakilinmu ya lura cewa maimakon karbar tsoffin kudaden, ’yan kasuwa da dama sun tanadi na’uarar tura kudi ta PoS ga kwastomominsu.

Wani dan kasuwa mai sayar da kayan gwari, Malam Lawal Ibrahim, ya shaida wa Aminiya cewa, “ban fara karbar tsoffin takardun N500 da N1,000 tukuna; amma ina karbar tsohuwar N200.”

Ya ce dalilinsa shi ne, “Gwamnati na ta kumbiya-kumbiya, don haka ina tsoron in karba, daga baya CBN ya ce ya canza shawara a bar ne da asarar biyan kudin kaya, shi ya sa ba na karba.”

Mohammed Isa mai kayan gwari shi ma ya ce, gara ya ki karbar tsoffin kudaden da ya bari su ja masa asara.

“Lokacin da aka fara cewa mu kai tsoffin kudin CBN, sai da na yi kwanaki a kofar CBN don in ajiye N100,000. Shi ya sa na yi wa kaina riga-kafi, da in yi asara gara kaya na sun yi kwantai.”

Yankin Kudu

Wannan yanayi haka yake a wasu sassa na Jihar Legas, inda bakuna suka fara bayar da tsoffin kudin, amma na dar-dar wajen yin cinikayya da su, duk kuwa da umarnin CBN na ci gaba da amfani da su zuwa ranar 31 ga watan Disamba.

A Jihar Ribas kumma, manyan shaguna da gidajen mai da wasu wuraren kasuwanci na ci gaba da harkokinsu da tsoffin kudin.

Sai dai an korafi cewa duk da cewa bankuna na bayar da tsofifn kudaden, amma idan aka kai musu ba sa amsa.

Wata mazauniyar garin Fatakwal, Amaka Ike, wadda wakilinmu ya zanta da shi ya ce, ta ce da kyar ta iya yin sayayya da tsofifn kudaden.

Amaka ta ce, “wasu masu shaguna, gidajen mai da wasu ’yan kasuwa ba sa karbar tsoffin kudaden saboda a cewarsu, har yanzu ba su natsu ba, gwamnati za ta iya sauya shawara a kowane lokaci, kan batun.”

AMINIYA

DSS ta kama mutum biyu a Kano kan zargin tayar da rikici

 


Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ce ta kama wasu mutane biyu da take zargi da tunzura mutane domin tayar da hankali a jihar Kano gabanin zaɓen gwamna da na ‘yan majalisun jiha da za a yi a ranar Asabar.

 

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter hukumar ta DSS ta ce mutanen sun naɗi hoton bidiyo ne da suke bayanan tunzura jama’a a cikinsu, sannan suka riƙa wallafa shi a shafukan sada zumunta.

 

Ta kuma wallafa sunayen Sharu Abubakar Taɓule mai shekara 37 a duniya, da kuma Isma’il Iliyasu Mnagu mai shekara 51 a matsayin waɗanda ta kama.

 

“Cikin waɗannan saƙonnin masu haɗari, sun nuna jam’iyyar siyasar da suke goyon baya kuma suka yi kira ga magoya bayansu su kai wa abokan hamayyarsu hari duk inda suka gansu.

 “Waɗanda ake zargin sun yi kira da a kai wa jami’an tsaro hari yayin zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi da za a yi a ranar Asabar.


“Wata jam’iyyar siyasa a Kano na barazanar shirya zanga-zanga a sakamakon shirin kai hare-haren,” in ji hukumar ta DSS.


Sanarwar ta ƙara da cewa jam’iyyar siyasar ta shirya kutsawa ofisoshin wasu hukumomin tsaro a ranar 16 ga watan Maris a matsayin nuna goyon baya ga waɗanda ake zargin.“Yayin da hukumar ke sanar da mutane kan wannan haramtaccen mataki, ta kuma yi kira ga jam’iyyar da ta dakatar da wannan lamari, ko kuma ta shirya yaba wa aya zaƙinta.


“DSS ba za ta zuba ido tana kallon mutane suna tunzura al’umma ba su tayar da hankali da rashin tsaro a jiha ba.”


Sanarwar DSS ta ce za ta haɗa hannu da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da an samar da cikakken tsaron da zai bayar da damar da gudanar da zaɓe mai inganci a jihar.


Baya ga Kano hukumar tsaron ta kama wasu mutane da ke irin wannan kiraye-kiraye a wasu jihohi a faɗin ƙasar.


Hukumar ta shawarci jam’iyyun siyasa a fadin Najeriya da su gargadi mabiyansu su zama masu bin doka da oda, domin tabbatar da dimokuraɗiyya ta samu wurin zama yadda ya kamata


BBC

Tuesday, 14 March 2023

‘Kusan Sau Miliyan 13 Aka Yi Yunkurin Yi Wa Najeriya Kutse Yayin Zaben Shugaban Kasa’


 Gwamnatin Tarayya ta ce akalla sau 12,988,978 aka yi yunkurin yin kutse a shafukan intanet na Najeriya yayin zaben Shugaban Kasa da na ’yan Majalisun Tarayya da aka yi a ranar 25 ga watan da ya gabata.

Hare-haren, a cewar gwamnatin an kai su ne daga ciki da wajen kasar, kuma an yi su ne kan shafukan gwamnati, kusan sau 1,550,000 a kullum.

Ministan Sadarwa, Isah Ali Pantami ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata.

To sai dai ya ce yunkurin kutsen ya yi tashin gwauron zabo zuwa sau 6,997,277, a ranar zaben Shugaban Kasa ta Asabar.

Ministan ya kuma ce ma’aikatarsa ta kafa wani kwamitin yaki da irin wadannan hare-haren, kuma ya fara aiki ne ranar 24 ga watan na Fabrairu, sannan ya kammala ranar 28.

AMINIYA

Sufeto Janar Ya Sake Turo Usaini Gumel A Matsayin Sabon Kwamishinan 'Yan Sanda Na Kano


Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali, ya sake soke turo kwamishinan ‘yan sandan Kano.

A wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, Sufeto Janar din ya soke aika Feleye Olaleye a matsayin kwamishinan ‘yan sandan Kano tare da sanya CP Ahmed Kontagora a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Sai dai a wata siginar da aka sake fitarwa a daren jiya, sufeto janar din ya nada CP Usaini Gumel a matsayin wanda zai jagoranci rundunar 'yan sanda ta Kano lokacin zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha a jihar.

A ranar 8 ga Maris, bayan zanga-zangar da ‘yan adawa suka yi, IGP ya sauya matakin da aka tura CP Balarabe Sule, tsohon babban jami’in tsaro ga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, a matsayin wanda zai maye gurbin CP Mohammed Yakubu

A cikin sabuwar takardar da aka fitar mai dauke lamba TH.5361/FS/FHQ/AB3/SUB.6/146, Mista Alkali kuma ya sake yin wasu ƙananan canje-canje a cikin umarnin.

IGP ya umurci DCP Auwal Musa da ya karbi DCP Nuhu Darma a matsayin mataimakan kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ayyuka da binciken manyan laifuka (CID)

Daily Nigerian 

Dokar Zabe Ta Inganta Zabukan Najeriya —Fadar Shugaban Kasa

 


Fadar Shugaban Kasa ta ce zabukan da aka yi na Shugaban Kasa da ’yan Majalisar Dokokin Tarayya a ranar 25 ga watan Fabarairu, sun inganta ne albarkacin Dokar Zabe ta 2022.

Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu, ya ce albarkacin Dokar Zabe, an samu gagarumin ci gaba idan aka kwatanta da zabukan da aka yi a kasar a baya.

A sanarwa da kakakin shugaba Buhari ya fitar, fadar ta ce duk da cewa an samu wasu matsaloli nan da can, wannan ba zai sa a ce zaben ya gaza ba.

Fadar shugaban ta nuna godiya kan damuwar da manyan jagororin masu sanya ido na kasashen waje musamman tsoffin jakadu; Mark Green da Johnnie Carson suka nuna a kanmatsalolin da aka samu kan kayan aiki a lokacin zabukan.Sanarwar ta ce duk da ’yan matsalolin da aka samu ba za a ce zaben ya gaza ba, illa dai wadanda suka fadi ne suke nuna gazawarsa.

Kakakin ya ce zaben na Najeriya ba shi kadai ba ne ake samun ire-iren wadannan matsaloli abu ne da kusan a kowa ce kasa ake iya samu a zabe.

Malam Garba ya ci gaba da cewa “ko ba komai, yadda Ma’aikatar Harkokin Waje ta Amurka da Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak da sauran shugabannin Afirka ta Yamma da na Tarayyar Afirka suka taya murna ga dan takarar APC Bola Ahmed Tinubu, wanda ya yi nasara a wannan zabe da ya kasance wanda aka fi fafatawa a tarihin Najeriya, hakan ya nuna cewa abin a yaba ne“Tabbas Dokar Zabe ta 2022 ta inganta zaben, la’akari da yadda na’urar tantance masu zabe BVAS ta kawo karshen aringizon kuri’u da duk wata cuwa-cuwa wajen kada kuri’a.”

AMINIYA

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Head of Service Urges Civil Servants to Uphold Ethical Conduct

The Head of Service, Kano State, has called on civil servants to strictly adhere to the Civil Service ethical code and show grea...