Search This Blog

Thursday, 12 January 2023

Za a shafe wata shida nan gaba cikin karancin Fetur a Najeriya - Inji IPMAN

Kungiyar dillalan man fetur a Najeriya ta ce za a ci gaba da fuskantar karancin fetur a faɗin kasar har zuwa watan Yunin wannan shekarar.

Kungiyar ta ce wahalhalun ko karancin na da alaƙa da shirin gwamnati na janye tallafin mai baki daya a cikin watan Yuni.

Tun a shekarar da ta gabata al'ummar kasar ke fama da karanci mai a sassa daban-daban na Najeriya, musamman arewaci.

A ranar Litinin ministan albarkatun fetur, Timipre Sylva, ya ce kamfanin mai na NNPC na tafka asara kan farashin da ake sayar da man a yanzu.

A makon da ya gabata, ministan kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ya ce gwamnatin Tarayya ta ware naira tiriliyan 3.6 domin biyan tallafi zuwa Yunin 2023.

Kamawa zasu maimaita abun da ya faru a zaben 1993 - Ganduje

Abdullahi Umar Ganduje, ya ce Kanawa za su sake maimaita abin da ya faru a zaben Shugaban Kasa na 1993, inda suka goyi bayan dan takarar da ya fito daga yankin Kudu – suka yi watsi da nasu na Arewa kuma dan asalin jihar.

Ganduje ya yi wannan furuci ne a yayin wani rangadin yakin neman zabe da ya fita tare da ’yan takarar jam’iyyar APC masu neman mukamai daban-daban a zabe mai zuwa.


Aminiya ta ruwaito cewa gwamnan ya yi furucin ne yayin da ya ziyarci Hakimin Kibiya, Sunusi Abubakar Ila, bayan gudanar da taron yakin neman zabe da tuntubar juna a kananan hukumomin Rano da Bunkure na jihar.

A zahiri dai Ganduje ya tabbatar da goyon bayansa ga dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, inda ya yi hannun riga da tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ke takarar kujerar Shugaban Kasa a jam’iyyar NNPP.

A jawabinsa yayin hikaito tarihi, Ganduje ya ce, “Mun zabi Cif MKO Abiola na jam’iyyar SDP kuma muka ki amincewa da Bashir Othman Tofa na jam’iyyar NRC saboda dukkanmu mun yi imani da hadin kan kasa da la’akari da cancanta.

“Sanin mu ne cewa Tinubu ya kasance ginshiki wajen fitowar Atiku Abubakar a matsayin dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar Action Congress (AC).

“Ya [Tinubu] kuma tsaya tsayin daka wajen ganin Nuhu Ribadu ya zama dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN).

“Saboda haka, Asiwaju Tinubu ya yi aiki tukuru wajen ganin an samu daidaito, kuma a baya ya rika fadi–tashi wajen goyon bayan ’yan takarar Shugaban Kasa da suka fito daga a Arewa.

“Duba da wannan dalili, ya cancanci mu saka masa da irin alherin da ya yi. Kuma a yanzu ba mu da wani zabi da ya wuce mu goyi bayan takararsa.

“A halin yanzu Tinubu shi ne daya tilo wanda ya cancanta kuma ya fi cancantar takarar Shugaban Kasa a zabe mai zuwa.

“Ba zai gushe ba Arewa na goyon bayansa saboda akidarsa ta gina kasa, da sanin ya kamata, da tsayuwar daka ga ci gaban bil’adama da kasa, da dai sauran abubuwa,” in ji Ganduje.

Hukumar DSS ta kama tsohon Shugaban Kungiyar Yakin Neman Zaben dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar LP, Doyin Okupe

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama tsohon Shugaban Kungiyar Yakin Neman Zaben dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar LP, Doyin Okupe.

A cewar Tolu Babaleye, lauyan Okupe, an kama dan siyasar ne a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Ikeja a Jihar Legas, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Landan.


Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, ta samu Okupe, mai bai wa tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan shawara kan Harkokin Jama’a, da laifin karkatar da kudaden makamai daga Ofishin mai bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro.

Mai shari’a Ijeoma Ojukwu ta bayyana cewa, masu tuhuma sun gabatar da karar satar kudi a kan Okupe wanda aka ci shi tarar Naira miliyan 13.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa, A shekarar 2019, Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arziki Zangon Kasa, ta tuhumi Okupe da laifuka 59 ciki har da wadanda suka shafi karkatar da kudi har Naira miliyan 240 daga hannun Sambo Dasuki.

An gurfanar tare da shi tare da wasu kamfanoni biyu – Value Trust Investment Ltd da Abrahams Telecoms Ltd.

Mai shari’a Ojukwu, ta samu Okupe da laifuka 26 daga cikin tuhume-tuhume 59 da EFCC ta gabatar a kansa.

Alkalin ya yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu kan kowanne laifi daga cikin tuhume-tuhumen 26 ko kuma zabin biyan tarar N500,000 ga kowanne laifin.


Alkalin ta kuma bayar da umarnin cewa idan ba a biya tarar cikin sa’o’i 24 ba, za a tisa keyar Okupe zuwa gidan yari, lamarin da ya yi gaggawar cika wa’adin saboda gudun zaman wakafi.

A cewar Babaleye, DSS ta bukaci Okupe ya gabatar da hanyoyin da ya bi wajen biyan kudaden da kotun ta yanka masa duba da laifin da ake tuhumarsa da shi.

Har yanzu dai hukumar DSS ba ta ce komai kan ikirarin lauyan nasa ba.

Okupe dai ya ajiye mukaminsa na shugabancin yakin neman zaben Peter Obi bayan da aka yanke masa hukunci, inda hadimin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, Akin Osuntokun ya maye gurbinsa.

Wednesday, 11 January 2023

Dan China Ya Yi Ikirarin Kashe Wa Marigayiya Ummita Miliyan 60

Dan kasar Chinan nan da ke zargi da kisan budurwarsa, Ummulkusum Buhari (Ummita), Frank Geng Quanrong, ya shaida wa kotu cewa ya kashe wa marigayiyar kudin da yawansu ya kai Naira miliyan 60.

Yayin zaman Babbar Kotun Jihar Kano Mai lamba 16 a ranar Laraba, Geng, ya yi ikirarin cewa ya kashe mata kudaden ne a tsawon shekaru biyun da suka yi suna soyayya.

“Baya ga manyan kudade da na kashe mata, nakan kai ta wuraren cin abinci kamar a otel din Bristol da Central da sauransu.

“Haka kuma na saya mata gida na Naira miliyan hudu da mota ta Naira miliyan 10. Haka kuma na ba ta jarin Naira miliyan 18 don fara kasuwanci baya ga takalma da jakunkuna da na zuba mata a shagon da ta bude na kimanin Naira dubu 500 da kuma atamfofi da lesi na kimanin Naira miliyan daya. Haka kuma na saya mata fili a Abuja inda ta fara ginawa,” in ji dan Chinan

A cewarsa, ya saya mata gwala-gwalai da kimarsu ta kai Naira miliyan biyar.


“Har ila yau, na saya mata wayar hannu kirar iPhone guda biyu da kudindu ya kai Naira miliyan daya da rabi. Haka kuma na ba ta Naira miliyan 6 don karbo satifiket din karatu daga Jami’ar Sakkwato don a lokacin tana sona.


Haka kuma na ba ta Naira miliyan daya da ta hada wutar sola a gidansu,” in ji shi.


A cewar Mista Geng, lokacin da suka fara shirye shiryen aurensu ya saya mata kayan aure da suka hada da atamfofi da lesi da mayafai da kudinsu ya kai Naira miliyan daya da rabi.

Da take sake bayar da shaida a gaban kotun, mahaifiyar Ummulkusum Buhari, wato Fatima Zubairu ta ce ta ga raunuka guda 11 a jikin gawarta.

Shi ma a tasa shaidar, dan sandan da ya gudanar da bincike a ofishin ‘yan sanda na Dorayi, ya shaida wa kotun cewa ya ga wukar da aka kashe Ummita da ita.

Ita ma da take bayar da shaida a madadin Hukumar Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, Dokta Hauwa Ibrahim, ta shaida wa kotun cewa ta sanya hannu ne a takardar rahoton gawar a madadin Shugaban Asibitin.

Daga nan ne Alkalin kotun, Mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Janairu don ci gaba da sauraren shaidun masu kariya.

(AMINIYA)


Babu abun da zai hana a gudanar da zabe a Najeriya - Gwamnati

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar wa da al’ummar kasar cewa babu abin da zai hana gudanar da babban zaben kasar da ke tafe a watannin Fabariru da Maris din shekarar da muke ciki ta 2023 duk da barazanar tsaron da kasar ke fuskanta.


Minstan yada labarai na Najeriyar, Lai Mohammed wanda ya bayyana haka a Abuja, ya ce gwamnati ba ta sauka daga kudirinta na gudanar da zabe kamar yadda aka tsara ba.

Kalaman gwamnatin dai na zuwa ne bayan hukumar zaben kasar mai zaman kanta INEC ta yi kashedi cewa idan har ba a shawo kan matsalar tsaron da wasu sassan kasar ke fama da shi ba, babban zaben kasar na iya faskara.

A cewar INEC ko da an iya gudanar da zaben a wasu sassan alamu na nuna cewa babu tabbacin iya gudanar da su a wasu sassa saboda matsalar ta tsaro, lamarin da tuni ya haddasa cece-kuce tsakanin 'yan Najeriya.

Haka zalika tuni, masana tsaro suka fara nuna yatsa ga hukumar ta INEC wadda suka ce bata da hurumin sanar da wannan mataki a radin kanta har sai ta tuntubi bangarorin tsaron kasar.

Najeriya dai na fama da jerin matsalolin tsaron da suka kunshi 'yan ta'adda da ke ci gaba da kaddamar da hare-hare a yankin arewa maso gabashin kasar baya ga 'yan bindiga da ke satar mutane da kuma kashewa don neman fansa a yankin arewa maso yammaci.

Kauyuka da dama ne musamman a jihohin Zamfara da Sokoto da kuma Neja yanzu haka ke karkashin ikon 'yan bindigar wadanda ke sanya musu haraji gabanin samun damar yin warkajami ko kuma gudanar da sana'o'insu koma noma a yankunan na su.


LABARI DA DUMIDUMINSA : Gwaman jahar Kwara ya nada Abdussalam Abdulkadir a matsayin sabon Sakataren zartarwa na hukumar Alhazan Jahar

Gwamnan Jihar Kwara Mallam Abdulrasaq Abdulrahaman ya nada Alh Abdulsalam Abdulkadir a matsayin sabon Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kwara Ilorin.

Cikin sanarwar da Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kwara ta fitar, ta ce nadin ya fara aiki ne nan take.

Kafin sabon nadin nasa, Alhaji Abdulsalam Abdulkadir ya kasance Kwararren Akanta a jihar Legas.

An haife shi a ranar 1 ga Yuli, 1964 a Unguwar Ilorin Pakata ta Jihar Kwara.


Hukumar NAHCON da Hukumar aikin Hajji taIndonesiya zasu hada gwiwa don samun nasarar aikin Hajji na 2023


Daga Mousa Ubandawaki 

Gabanin shirye-shiryen aikin Hajji na 2023, Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) tana nazarin tsarin hadin gwiwa da Hukumar Alhazai ta kasar Indonesiya domin bunkasa da karfafa fasahar yada labarai da kuma samar da kudade don inganta ayyukan aikin Hajjin bana.

Shugaban NAHCON, Alh. Zikrullah Kunle Hassan, wanda ya jagoranci tawagar zuwa taron ya bayyana cewa, tallafin fasahar sadarwa da na aikin Hajji na da matukar muhimmanci wajen samun nasarar duk wani shiri na aikin Hajji, don haka akwai bukatar a bibiyi tare da karfafa gwiwa."Domin mu tabbatar da lafiya da walwalar Alhazan Najeriya, ba mu da wata mafita face neman wadatar shirye-shiryen mu na fasahar sadarwa daga mafi kyawun duniya, don tabbatar da ingantaccen tsarin aiki."

Taron da aka yi a cikin bikin baje kolin ayyukan Hajji da Umrah na kwanaki 4 da ake gudanarwa a cibiyar Super Dome da ke birnin Jeddah inda sama da mahalarta 400 suka halarta na kara karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Alh Zikrullah ya bayyana fatansa cewa tsarin hadin gwiwa zai yi tasiri a kan sakamakon aikin Hajjin 2023. 

Ya ce, "Ina fatan samun kyakykyawan dangantaka tsakanin hukumomin guda biyu, wanda na yi imanin idan aka sallame su da himma, za su amfanar da Alhazan Najeriya tare da samun nasarar gudanar da aikin Hajji."

A nasa jawabin, shugaban kungiyar Badan Pengelola Keuangan Haji(BPKH), Fadlul Imansyah, ya jaddada muhimmiyar rawa da fasahar sadarwa da samar da kudade ke takawa wajen samun nasarar aikin Hajji da Umrah, ya kuma shawarci NAHCON da ta tabbatar da na’urar tantance ayyukanta domin amfanin alhazai. da al'ummar kasar.

Don haka ya bayyana jin dadinsa da goyon bayansa ga kawancen da ya ce zai taimaka wajen karfafa alakar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu.

Tawagar NAHCON ta kuma hada da kwamishinan tsare-tsare, sarrafa ma'aikata da kudi (PPMF), Alh Nura Hassan Yakassai, kwamishinan ayyuka, lasisi, masu kula da yawon shakatawa da yawon bude ido, Alh Abdullahi Magaji Hardawa, kwamishinan tsare-tsare, bayanan kididdiga da ayyukan laburare (bincike) PRSILS), Sheikh Suleman Mommoh, mambobin hukumar da wasu ma'aikatan hukumar.

 


Almundahanar N96bn: Wike Ya Sake Maka Amaechi A Kotu

Gwamnatin Ribas ta shigar da sabuwar kara kan tsohon gwamnan jihar kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, kan zargin yin sama da fadi da Naira biliyan 96.

An maka Amaechi tare da Tonye Cole, dan takarar gwamna na Jam’iyyar APC a jihar bisa zargin sayar da kadarorin jihar.

HOTUNA: Masaukin Ronaldo da burwarsa a Saudiyya
DAGA LARABA: Dalilin Da Maza Ke Tsoron Auren Mata ’Yan Boko 
Zacchaeus Adangor, babban lauyan Gwamnatin Jihar Ribas, ya tabbatar da shigar da karar.

Nyesom Wike, gwamnan Ribas, ya kafa wani kwamitin mutum bakwai don bincikar Amaechi kan zargin cirar Naira biliyan 96 daga asusun gwamnatin jihar a lokacin da yake gwamna.
Kwamitin ya kuma binciki batutuwan da suka shafi sayar da kadarorin da tsohon gwamnan ya yi.

Kwamitin ya gabatar da rahotonsa a 2015 kan binciken, amma Amaechi ya musanta aikata laifin da ake tuhumar sa.

A ranar 27 ga Mayu, 2022, wata babbar kotu ta yi watsi da bukatar Amaechi na hana kwamitin gudanar da bincike a kansa.

Sakamakon haka ne, Wike, ya umarci babban lauyan jihar da ya gurfanar da tsohon gwamnan tare da Tonye Cole da wasu mutum biyar da ake zargin na da hannu a badakalar.

Wike ya kuma umarci a shigar kan kamfanin Sahara Energy, wanda ake zargin an yi amfani da shi wajen satar kudaden.

A watan Oktoban 2022, Okogbule Gbasam, Alkalin Babbar Kotun Jihar Ribas, ya dakatar da tuhumar da ake yi wa kamfanin.

Wannan dai ba shi ne karon farko da gwamnati mai ci ke bincike kan gwamnatocin da suka shude ba, kan zargin cire makudan kudade ba bisa ka’ida ba.

A wasu lokuta ana zargin siyasa a cikin lamarin, da nufin daukar fansa musamman idan ya kasance akwai adawa a tsakan

HOTUNA: Masaukin Ronaldo da budurwarsa a Saudia

Cristiano Ronaldo, sabon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr da ke Saudiyya da budurwarsa sun tare a wani otel na alfarma da suke biyan kudin dakuna Yuro miliyan 3.04, kimanin Naira biliyan 1.5, a shekara.

Kudin dakunan da masoyan suka kama a birnin Riyadh ya kama Naira miliyan 122.6 a wata, wato Naira miliyan hudu a kullum.

Duk da Saudiyya ta haramta tarewar budurwa da saurayi, Ronaldo da masoyiyarsa, Georgiana Rodriguez, sun kama dakuna 17 a otel din da suka kama hawa biyu sukutum.

Rahotanni sun nuna an yi wa dan wasan da masoyiyarsa sassauci kuma za su rika zama ne tare da ’ya’yansu biyar a otel din, kafin daga bisani za su koma gidansu zai koma katafaren gidansu na Yuro miliyan 12.

Tuesday, 10 January 2023

Dogo Gide Na Neman N100m Kan Daliban FGC Birnin Yauri

Iyayen daliban da aka sace a Sakandaren Gwamnatin Tarayya (FGC) ta Birnin Yauri a Jihar Kebbi na neman agaji, bayan dan ta’addan da ya sace su, Dogo Gide, ya sa musu kudin fansa Naira miliyan 100.

Dogo Gide ya sanya sharadin biyan Naira miliyan 100 ne duk da iyayen yaran sun bi ta hannun mahaifiyarsa ta matsa masa lamba ya sako ragowar ’yan mata 11 da ke hannusa kusan tsawon shekara biyu.

Maharan jirgin Edo na neman fansar N520m
NAJERIYA A YAU: Ma’aikatar Shari’a ta fadi gwajin tsare gaskiya —ICPC
“Mun yi magana da Dogon Gide ranar 15 ga wagan Disamba, 2022, da farko ya ki magana, amma bayan mahaifiyarsa ta sa baki, ya amince zai sako yaranmu idan mun biya Naira miliyan 1oo, ko kuma mu hakura da su.

“Ya fada karara cewa idan ba mu yi abin da ya ce ba, har abada ba za mu sake jin duriyar ’ya’yanmu ba,” in ji Shugaban kungiyar iyayen daliban, Salim Kaoje.


Ya bayyana haka ne a wani taro da suka yi a makarantar a ranar Lahadi, inda suka ce sun riga sun ga gazawar gwamnati wajen ceto musu ’ya’ya, don haka ba su da zabi face yin abin da suke ganin za su iya.

Kusan shekara biyu ke nan, a watan Yunin 21, ’yan bindiga suka kai hari Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya ta Birnin Yauri suka yi awon gaba da dalibai 80, kuma har yanzu suna tsare da 11 daga cikin yaran.

Kaoje ya ce hakan ne ya susuke karo-karo daga hannun jama’a don tara kudaden da dan ta’addan ya shardanta, “shi ya sa muka zo domin yin wannan roko.”

Kaoje ya ce kowanne daga cikin iyayen daliban ya amince ya sayar da duk kadarorinsa domin su hada kudaden.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Presidential delegation pays condolence visit to Hamza Darma’s family in Kano

A high-powered presidential delegation has paid a condolence visit to the family of late Alhaji Hamza Usman Darma, a prominent K...