Search This Blog

Monday, 9 January 2023

Taro yakin neman zabe: Gwamnatin Kano ta bukaci jam’iyyun siyasa su yi amfani da filin wasa, da sauran wurare

A ci gaba da alkawarin da ta dauka na ganin an samu daidaito a tsakanin jam’iyyun siyasar jihar, jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano, ta ce a matsayinsu na ‘yan kasa, ‘yan adawa na da hakkin yin amfani da dukiyar al’umma wajen gudanar da ayyukansu na gangamin yakin neman zabe.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar kuma mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Gawuna/Garo, Malam Muhammad Garba, wanda ya bayar da tabbacin a wata sanarwa a ranar Litinin din da ta gabata, ya ce jam’iyyun za su iya samun kayan aiki irin su filin wasa ne kawai, idan sun samun izini daga hukumomin tsaro kan amfani da wuraren lafiya.
 
Ya ce gwamnatin jihar ta tsaya tsayin daka kan manufofinta na ba da hakki daidai a matsayin alamar mutunta manufofinta na dimokuradiyya.

Sanarwar ta kara da cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umarnin a samar da kayayyakin ga jam’iyyun siyasa tare da yin kira gare su da su tabbatar da amfani da kayayyakin yadda ya kamata tare da kiyaye duk wata barna da za a yi musu.

Ya kuma bayyana fatan jam’iyyun su gudanar da gangamin yakin neman zabensu cikin lumana.

Sunday, 8 January 2023

Gwamnatin Najeriya ta rufe tashar jirgin ƙasa a Edo bayan harin 'yan bindiga

 




Rahotonni sun ce lamarin ya faru ne a daidai lokacin da fasinjojin ke shirin hawa jirgin ƙasan zuwa garin Warri da ke jihar Delta

Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Edo Chidi Nwabuzor, ya ce kawo yanzu ba su samu labarin rasa rai ba.

To sai dai ya tabbatar da cewa wasu fasinjojin sun samu raunukan harbin bindiga daga maharan.

Ya ce 'yan bindigar ɗauke da bindigogi sun far wa tashar jirgin ƙasan da maraicen ranar Asabar, inda suka riƙa harbi a sama kafin su kama wasu da yawa daga cikin fasinjojin.

Lamarin na zuwa ne ƙasa da shekara guda bayan da 'yan ta'adda da ake kyautata zaton 'yan ƙungiyar Boko Haram sun kai hari kan jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a arewacin ƙasar tare da yin garkuwa da fasinjoji masu yawa, inda suka kwashe tsowon watanni a hannun 'yan bindigar.

Lamarin da ya tilasta wa gwamnatin ƙasar dakatar da zirga-zirgar jiragen tsakanin manyan biranen biyu na kusan sama da wata shida.

Labari da dumiduminsa : 'Yan bindiga sun sake yin garkuwa da fasinjojin Jirgin kasa

Watanni bayan da ‘yan ta’addan suka kai hari tare da yin garkuwa da fasinjoji da dama a cikin jirgin kasa zuwa Kaduna, wasu ‘yan bindiga sun kuma kai farmaki tashar jirgin kasa tare da kwashe mutane da yawa a Jihar Edo dake kudu maso kudancin Najeriya.

Fasinjojin da suka samu raunuka, an ce suna jiran su hau jirgin kasa a wurin da lamarin ya faru, kafin su nufi garin Warri mai arzikin man fetur.

Tuni dai hukumar 'yan sanda ta Rahotanni sun tabbatar da faruwar lamarin a cewar tashar talabijin ta TVC.

Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta ce ‘yan bindigar da ke dauke da bindigogi kirar AK-47 sun kai farmaki tashar jirgin da misalin karfe 4 na yammacin ranar Asabar 7 ga watan Janairu, inda suka yi ta harbe-harbe kafin su fito da shirinsu. 

A ranar 28 ga Maris, 2022 ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan jirgin kasa da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, inda suka kashe wasu tare da yin awon gaba da wasu fasinjoji. 2022 .

Har yanzu dai Hukumar Jiragen kasa ta Najeriya ba ta ce uffan ba game da sabon ci gaban da aka samu a daidai lokacin da ake hada wannan rahoto.

Saturday, 7 January 2023

BIDIYO: Abun da ya faru lokacin zuwan Tinubu Kano


 

Aminu Alan Waka ya ajiye takarar sa ya fice daga jam’iyyar Sha’aban Sharada

Bayan ficewarsa daga jam’iyyar ADP Shahararren mawakin nan wanda kuma ya shiga siyasa Aminu Ala, ya fice daga Jam’iyyar ADP ta Sha’aban Sharada ya kuma koma jam’iyyar APC.

KADAURA24 ta rawaito cewa Alan Waka dai yana daga cikin ‘yan Kannywood da suka shiga tafiyar Sha’aban Sharada, Inda har ma ya rabauta da takarar dan majalisar tarayya na karamar hukumar Nasarawa a jam’iyyar ADP bisa jagorancin Dauda Kahutu Rarara.


Jim kadan bayan ficewarsa daga jam’iyyar ADP, Kadaura24 ta gano Alan waka tare da mataimakin gwamnan kano Dr Nasiru Yusuf Gawuna wanda Kuma shi ne dan takarar gwamnan Kano na Jam’iyyar APC, hakan Kuma ya tabbatar da cewa ya yanke shawarar marawa Gawuna baya.

 Hakan dai na alamta cewa Alan Waka ya koma tafiyar jam’iyyar APC Kuma zai marawa takarar Dr. Gawuna bayan maimakon ta Sha’aban Sharada da ya faro.


Ku biyo mu nan gaba kadan idan mun tattauna da Aminu Alan zaku ji cikakken bayani kan dalilansa na ficewa daga tafiyar Sha’aban Sharada zuwa APC ta Dr. Nasiru Gawuna

LABARI CIKIN HOTUNA : Abdulmumin Jibrin Kofa ya kai ziyarar ta'ziyya ga al'umomi daban-daban

Dan takakarar majalisar tarayya na mazabar Kiru da Bebeji a jam’iyyar #NNPP, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya kai ziyarar ta'ziyya da dubiyar marasa lafiya ga Unguwanni da garuruwa daban-daban dake yankin Kiru da Bebeji 

2023:Za Mu Sama Wa Katsina N10bn Daga Hasken Rana A Shekara —NNPP


Dan takarar Gwamnan Katsina a Jam’iyyar NNPP, Nura Khalil, yi alkawarin tara kudaden shiga Naira biliyan 10 daga hasken rana a duk shekara a jihar.

Injiniya Nura Khalil ya ce kudaden shigar N10bn da jihar za ta rika samu daga bangaren hasken rana zai sa ba sai ta jira daga Asusun Tarayya ba.

A gaggauta kammala masana’atar tiransfomar Najeriya —Buhari
A jawabinsa a taron fara yakin neman zabensa a Karamar Hukumar Mashi, ya ce, “Na fara da Mashi ne saboda da ita da Daurawa ta Jihar Jigawa da Kankiya bisa ga binciken da muka yi sun fi samar da hasken rana da za ta samar da lantarki ba sai an jira daga wani wuri ba.

“Za mu yi amfani da wannan hasken wutar lantarkin don sama wa jihar kudaden shigar da akalla za a samu bilyan N100 a shekara.


“Kudaden za mu yi amfani da su wajen gudanar da ayyukan gwamnati ba sai mun jira na Gwamnatin Tarayya ba.”

Ya kara da cewa idan ya ci zaben da ke tafe a watan Maris, “Muna da shirin kafa banki mallakar gwamnatin jiha wanda zai iya bayar da damar yin ajiya mai kama da shirin adashe don dai mu farfado da tattalin arzikin jihar.”

Game da matsalar tsaro, dan takarar ya ce Katsina tafi sauran jihohi hadari, amma idan NNPP ta hau mulki zai zama tarihi.

Ya kuma yi shagube ga wadanda yake zargi da sayen katinan zabe da nufin yin magudin zabe, da cewa a wannan karon karyarsu a kare.
“Ana bin mata ana sayen katunan zabensu a kan N10,000 amma a karshe sai a ba su N500.

“To a sani, babu batun magudi a wannan zaben, balle a ba wani katin wani ya je ya jefa kuri’a sama da goma,” in ji shi.

Ya zargi gwamnatin APC ta Jihar Katsina da yin watsi da fannin ilmi; inda ya ce a shekara bakwai na gwamnatin, yara 100,000 sun kasa rubuta jarabawa.

Don haka ya bukaci jama’a su zabi Jam’iyar NNPP don ta fitar da su daga kunci da rashin tsaron a jihar.
Tun da farko shugaban NNPP na jihar Katsina, Sani Liti ’Yankwani, ya ce, matsalolin satar jama’a, kisa da jahilci, sun ishi mutane hankali, saboda abin da ya kira rashin kulawar gwamnatin jihar.

A kan haka ne a ce idan aka zabi NNPP, za ta kawo karshen matsalolin musamman na rashin tsaro.

Shugaban NNPP na Kasa kuma dan takararta na shugaban kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso wanda ya dan takarar Gwamnam Kano na jam’iyar, Abba Kabir Yusuf (Abba gida-gida) ya wakilta, ya ce, jam’iyy ta yi kyawawan tanade-tanaden samar da ayyukan yi da tallafin sana’o’i ga mata da matasa da kuma kawo karshen matsalar tsaro.
(AMINIYA) 


Muna buƙatar Buhari ya sa baki kan ƙarin kuɗin makaranta - Kungiyar Dalibai

Ƙungiyar Ɗalibai ta Najeriya NANS ta buƙaci shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya yi ''gaggawar sa baki'' game da ƙarin kuɗin makaranta da jami'o'in ƙasar ke shirin yi tun kafin hakan ya janyo matsaloli a faɗin ƙasar''.

Sakataren ƙungiyar na ƙasa Usman Baba Kankia, ya shaida wa BBC cewa ''duk makarantun gwamnatin tarayya sun ƙaƙƙara kuɗaɗe fiye da kashi 250 cikin dari'',

A baya-bayan nan dai an ga yadda wasu daga cikin jami'o'in ƙasar suka bayyana ƙarin kuɗin makaranta.

To sai dai Sakataren ƙungiyar ya ce suna zargin cewa makarantun sun samu umarnin ƙara kuɗin makarantar ne daga sama.

Dalilin ya da sa kenan suka rubuta wasika ga shugaba ƙasa, inda suka buƙace shi a matsayinsa na uba, ya sa baki domin mayar da kuɗin makarantar yadda yake a baya.

Wasu jami'o'in dai sun bayyana cewa sun yi ƙarin kuɗin makarantar ne domin samun damar gudanar da makarantun nasu.

dalibai
othersCopyright: others
To sai dai ƙungiyar ta ce kundin tarin mulki ya wajabta wa gwamnati samar da ingantaccen ilimi ga 'yan ƙasa, don haka dole ta samar da kuɗin gudanar da ɓangaren ilimi.

Haka kuma Sakataren na NANS ya ce ''matuƙar ba a soke ƙarin kuɗin makarantar da aka yi ba, to kashi 40 zuwa 50 cikin 100 na ɗaliban ƙasar ba za su koma makaranta ba, saboda ba za su iya biyan wannan kuɗi ba''.

Abin da kuma a cewarsa zai ƙara yawaitar masu aikata miyagun laifuka a fadin ƙasar saboda rashin makoma da ɗaliban ke da shi.

Mista Kankia ya kuma yi gargaɗin cewar ''matukar buƙatarmu ba ta biya ba, to za mu gudanar da gagarumar zanga-zangar da za ta shafi abubuwa da dama a faɗin kasar nan''.

Dokta Ahmad BUK: Ba rabo da gwani ba

Sahabi Aliyu (RA) ya fadi ga Jabir dan Abdullahi (RA) cewa “Duniya ta dogara ne a kan abu hudu; addini da malami mai yin aiki da iliminsa, sai jahili wanda ba ya girman kai wajen neman sani da kuma mawadaci wanda ba ya rowa da dukiyarsa.”


Marigayi Sheikh Dokta Ahmad Muhammad Ibrahim wanda aka fi sani da Dokta Bamba ya ce ilimi ba komai ba ne sai sanin abu a zuciya da kuma gaskata shi a zahiri, yayin da jahilci ke nuni da kiyaye abu a zuciya wanda a zahirance ba gaskiya ba ne.


Saboda haka, a cewarsa ba kawai rashin sanin abu ake kira jahilci ba, a’a har ma da sani gami da riko da abin da bai gaskata ba.

Rayuwa irin ta Dokta Ahmad madubi ce ga daukacin al’ummar Musulmi.

M

utum ne mai kyakkyawar fahimta ga lamurran addini, amma mai zafafawa wajen kare martabar Annabi Muhammad (SAW).


Mai kimanin shekara 82 a duniya, wanda ya rasu a ranar Juma’a, 7/1/2022, marigayi Dokta Ahmad Bamba ya shafe daukacin rayuwarsa wajen nema da kuma yada ilimi.

Ya shafe sama da shekara 20 yana daukar darasi a Masallacin Annabi Muhammad (SAW) a Madina.

Sannan ya fassara Littafin Muwadda na Imamuna Maliku ɗan Anas daga harshen Larabci zuwa harshen Hausa, baya ga karantar da manyan littattafan Hadisi irin su Sahih Bukhari da Sahih Muslim da Sunanu Abu Dawud da Sunanu Nisa’iy da Sunanu Tirmizi da Sunanu Ibn Maja da Sunanu Darimi da Musnad Ahmad bn Hambal da sauransu duk a cikin harshen Hausa.


Tabbas, rasuwarsa babbar asara ce ga kafatanin al’ummar Musulmi musamman Hausawa.


Ya zo a cikin littafin ‘Al ilmu Huwal Imamu’ na Sheikh Ibrahim Nyassi cewa hanyar Aljanna tana hannun mutum hudu: Malami da mai gudun duniya da mai ibada da kuma mai jihadi fi sabilillahi.


Shi malami idan ya kasance mai gaskiya ne a cikin zuciyarsa, tabbas Allah zai azurta shi da hikima.

Duk kuwa wanda aka bai wa hikima alal hakika an ba shi gagarumar baiwa a nan duniya da gobe Lahira kamar yadda yadda ya zo a cikin Littafin Allah wato Alkur’an

An tambayi Dan Mubarak cewa su wane ne mutane? Sai ya ce ‘Malamai,’ sai aka ce masa su wane ne sarakuna? Sai ya ce ‘masu gudun duniya,’ sai aka ce su wane ne kaskantattu? Sai ya ce ‘masu cin duniya da addini.’


Don haka, ana iya cewa lallai malamai mutane ne masu daraja a cikin al’umma.

Abdul’aswad yana cewa babu wani abu wanda ya fi ilimi daukaka. Sarakuna masu yin hukunci ne ga jama’a, yayin da malamai ke yin hukunci a gare su.



Ahnaf (RA) yana cewa malamai sun kusa kasancewa iyayen giji, dukkan daukakar da ba a karfafe ta da ilimi ba, karshen ta kaskanci ne.


Annabi Muhammad (SAW) ya ce “Malamai su ne magada Annabawa.” (Tirmizi, Abu Dawood da Ibn Maja duk sun ruwaito shi) Allah Ta’ala kuwa Ya ce, “Iyaka dai masu jin tsoron Allah su ne malamai.” (Suratul Fathi, 28).

Babu bukatar zurfafa yabo ga marigayi Malam Ahmad Bamba, domin shi ba mai son yabo ko kwarzantawa ba ne a zamanin rayuwarsa, amma yana gaba-gaba wajen jaddada Sunnah a Kasar Hausa bayan da ta dauko dusashewa.

Mutum ne shi wanda yake son Allah da ManzonSa (SAW), wanda yake tarbiyyantar zukatan bayin Allah a kan bautar Allah ta tsanin ManzonSa Annabi Muhammad (SAW) da mayar da lamura ga AlSadiq Tukur Gwarzolah, kuma mutum ne marar kwadayi, mai darajanta ilimi da darajanta kansa, gami da fadar gaskiya walau ga shugabanni ko ga  mabiyansu.

Allahu Akbar! Shi mutum ne mai daraja a duniyar Musulunci, tushen darajarsa kuwa bai wuce ga rikonsa ga Sunnar Annabi Muhammad (SAW) ba da tsantseninsa, kai ka ce shi ne Imam Maliku bn Anas ko Imam Hasanul Basri.

Hakika rayuwarsa ta kasance abar koyi ga al’ummar Musulmi.

Wani sashen masana sun ce an fifita Imam Hasanul Basri a kan sauran Tabi’ai ne saboda abubuwa biyar:

  1. 1. Ba ya umarni da aikata wani aiki face ya fara aikatawa.
  2. 2. Ba ya hana wani aiki face ya fara hanuwa daga gare shi.
  3. 3. Duk wanda ya nemi wani abu daga abin da Allah Ya hore masa zai ba shi.
  4. 4. Ya kasance yana wadatuwa da iliminsa ga barin neman wani abu a wajen mutane.
  5. 5. Ya kasance ciki da wajensa duk daya ne.

Tabbas duk wadannan siffofi biyar sun tabbata ga marigayi Sheikh Ahmad Ibrahim Bamba.

Ga shi kuma ya samu cikawa irin tasa, da fatan Allah Ya rahamshe su duka amin.

Abdullah bin Amr Ibnul Ass ya ruwaito daga Annabi Muhammad (SAW), cewa “Lallai, Allah ba Ya dauke ilimi daga hana shi ga bayinSa.

Sai dai Yana dauke ilimi ne daga mutuwar malamai ta yadda tsarkakakkun mutane za su gushe, sai mutane su nada wawayen (jahilai) mutane a shugabanci (su dauke su malamai).

Sannan idan aka tambaye su, sai su yi magana ba da ilimi ba. Sai su taɓe kuma su yi asara.” (Bukhari da Muslim suka ruwaito).

Muna juyayin rashin babban masani Dokta Ahmad Bamba, to amma ya kamata kowa ya sani wannan duniya ba abar dawwama ba ce.

Kowane mai rai zai dandana mutuwa. Kuma tabbas, yadda Dokta Ahmad ya koma ga Mahaliccinsa, kowanenmu lokaci yake jira domin komawa ga Allah.

Don haka, ya kamata mu shagaltu wajen aiki da koyarwarsa da neman ilimi da bin Allah da kuma neman dacewar Allah da samun Aljanna.

Allah Ya gafarta wa Dokta Ahmad Ibrahim Bamba, Allah Ya tallafi bayansa, amin
(AMINIYA) 

Friday, 6 January 2023

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Ya yi sabon Aure

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya auri mata ta biyu Hauwa'u Adamu Abdullahi Dikko a Kano ranar Juma'a.


Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa an gudanar da daurin auren  ne a gidan marigayi Jarman Kano Farfesa Isah Hashim da ke unguwar Nasarawa GRA a cikin babban birnin tarayya.

Sannan kuma Madakin Kano Alhaji Yusuf Nabahani Ibrahim ne ya wakilci Mai Martaba Sarkin a lokacin daurin auren, yayin da Alhaji Shehu Hashim ya kasance waliyin  amarya.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Presidential delegation pays condolence visit to Hamza Darma’s family in Kano

A high-powered presidential delegation has paid a condolence visit to the family of late Alhaji Hamza Usman Darma, a prominent K...