Tsohon Shugaban NAHCON Ake Bincika Ba Farfesa Abdullahi Sale Usman Ba - Ibrahim Abubakar

Mun lura a matsayinmu na ‘yan kasa masu bibiyar harkokin da suka shafi jin dadin alhazan Najeriya kan batun wani gajeren fafen bidiyo mai cike da radani dake yawo a dandalin sada zumunta kan taron jin ra’ayoyin jama’a wanda kwamitin kula da harkokin aikin haji na majalisar wakilai ya shirya a ranakun 13 da 14 ga watan Nuwamban 2024 da muke ciki kan binciken aikin Haji na 2024, inda shi wanda ya yada wannan fefen bidiyo bai fito karara ya bayyanawa mutane shin tsohon shugaban hukumar NAHCON ko sabon ake bincika.

A sanarwar da babban jami’in tawagar tallafawa harkokin yada labarai ga hukumar NAHCON na kasa, Ibrahim Abubakar ya sanyawa hannu, yace, muna so mu sanarwa da jama’a musammam masu shirya wannan makirci, cewa shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Sale Usman ba ya cikin wannan badakala da ta faru lokacin aikin Hajin 2024, a takaice shi an nada shi shugabancin hukumar ne watanni bayan gudanar da aikin aikin Hajin 2024.

Ibrahim ya ci gaba da cewa Zuwan Farfesa Abdullahi Saleh wajen taron jin ra’ayoyin jama’ar ya faeu ne sakamakon kasancewarsa shugaban hukumar a halin yanzu domin ya shaida yadda lamarin zai kasance kana kuma ya kara aniya domin fuskantar babban aikin dake gabansa a matsayin sabon shugaban hukumar

A saboda haka, muke kira ga masu shirya wannan makirci su guji aikata wannan mummunan aiki kan shugaban hukumar NAHCON

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki