Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Sale, Zai Fara Aiki A Matsayin Shugaban Riko Kafin Majalisar Dattijai Ta Tabbatar Da Nadinsa

Farfesa Abdullahi Sale Usman wanda aka nada a matsayin shugaban hukumar alhazai ta kasa NAHCON, zai fara gudanar da aikinsa a matsayin Shugaban riko har sai majalisar dattawa ta amince da nadin. 


Wannan tsari dai zai kasance har sai majalisar dattawa ta dawo daga hutu domin tattaunawa kan nadin nasa.


Hakan na kunshe ne a wata takarda da jaridar Hajj Chronicles ta gani, mai kwanan wata 5 ga Satumba 2024, kuma mataimakin shugaban ma’aikata a ofishin mataimakin shugaban kasa, Ibrahim Hassan Hadejia ya sanya wa hannu. 

Wasikar ta bayyana cewa Farfesa Usman zai sa ido kan ayyukan Hukumar yayin da yake jiran amincewar majalisar dattawa.


Nadin Farfesa Usman ya samu gagarumin goyon baya saboda dimbin gogewa da gudummawar da ya bayar a fannin aikin Hajji a Najeriya, musamman a jahar Kano lokacin da ya rike matsayin shugaban Hukumar Alhazai ta Kano 


Ana sa ran tabbatar da shi a zaman majalisar da zarar ta koma hutu

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki