An samu cimma matsaya tsakanin Kungiyar Masu Gidajen Burodi da Hukumar Karbar Korafe-Korafe
Gwamnatin Jihar Kano da Kungiyar masu hada Burodi ta jihar Kano sun cimma matsaya akan farashin Burodi a jihar.
Wannan na zuwa ne bayan da farashin buhun Fulawa ya sauka a Najeriya zuwa naira dubu 60 daga sama da naira dubu 80,saidai ba’a ga saukin farashin Burodi a jihar Kano da sauran jihohin Najeriya ba.
Amma a madadin gwamnatin Kano, hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta kano tayi wani zama na musamman da Kungiyar masu Burodi domin cimma matsaya akan rage Burodin.
A cikin sanarwar da ta fitar a karshen taronta da kungiyar masu yin burodi a ranar Laraba, hukumar ta karbar korafe korafe ta bayyana cewa, duk da faduwar farashin buhun Fulawa amma farashin Burodi bai sauya ba.
A cikin sanarwar mai dauke da sa hannun hadin gwiwa da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, ta Kano Barista Muhuyi Magaji Rimin-Gado da kuma shugaban kungiyar masu yin burodin Alhaji Jibrin Hamza da sakataren Kungiyar, sun amince cewa ba zasu rage farashin Burodin ba , maimakon haka saidai su kara girmansa da ingancinsa.
A cikin sanarwar, masu yin burodin sun bayyana cewa, baya ga fulawa, akwai wasu muhimman abubuwan da ake bukata wajen yin Burodin wanda farashinsu bai ragu ba,sai Fulawa kadai don haka ba’a bukatar rage farashin Burodin saboda Fulawa kadai.
Dukannin bangarorin biyu sun amince da matsayar da aka samu.
TST Hausa ta rawaito cewa daga yanzu zuwa kowanne lokaci za’a ga sauyi a Burodin da jama’ar Kano suke saya ta bangaren girma da dandano kamar yadda Kungiyar masu Burodin ta tabbatar.