Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba — Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa
Shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwa na Jihar Kano mai Yaƙi da Shan Miyagun Kwayoyi da Safarar Su Ba Bisa Ka'ida ba, Barista Muhuyi Magaji Rimingado, ya yi gargaɗi mai ƙarfi ga 'yan siyasa da su daina neman a saki 'yan daba ko waɗanda ake zargi da laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi bayan an kama su.
Da yake zantawa da manema labarai a Kano, Rimingado ya ce kwamitin zai gudanar da aikinsa cikin adalci ba tare da nuna son kai ko tsoro ba, yana mai jaddada cewa ba zai bari wani tasirin siyasa ya kawo cikas ga yaƙin da ake yi da shan miyagun kwayoyi, safarar su da kuma ayyukan 'yan daba ba.
Ya ce babu wani ɗan siyasa da ya kamata ya zo neman a saki duk wani wanda aka kama da laifuka.
"Kada wani ɗan siyasa ya zo wurina yana neman na saki ɗan daba idan muka kama shi. Wannan Kano ce, kuma dukkanmu 'yan asalin jihar ne.
Ba za mu bari wasu tsirarun mutane su lalata makomar jiharmu ba."
Rimingado ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ne ya ƙaddamar da kwamitin bayan ayyana shaye-shayen miyagun kwayoyi a matsayin matsalar gaggawa ta lafiyar al'umma a ranar 22 ga Yuli.
Ya ce kwamitin ya ƙunshi wakilan hukumomin tsaro da sauran hukumomin gwamnati masu ruwa da tsaki.
A cewarsa, an ɗora wa kwamitin alhakin murƙushe hanyoyin safarar miyagun kwayoyi, yaƙi da shaye-shaye, tallafa wa masu neman gyara ta hanyar shirye-shiryen farfaɗowa da kuma tabbatar da gurfanar da masu laifi a gaban kotu.
Ya bayyana masu safarar miyagun kwayoyi a matsayin manyan maƙiyan al'umma, yana mai cewa su ne babban abin da kwamitin zai fi mayar da hankali a kansa.
Shugaban kwamitin ya kuma bayyana cewa, bisa ƙididdigar Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano, kusan kashi 70 cikin 100 na manyan laifukan da aka samu a jihar a shekarar 2025 suna da alaƙa da shan miyagun kwayoyi.
Ya ƙara da cewa kwamitin zai kuma ɗauki mataki kan ƙungiyoyin 'yan daba, yana mai tunatar da cewa umarnin zartarwa da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya ya haramta irin waɗannan ƙungiyoyi ƙarƙashin Sashe na 97A na Dokar Hukunta Manyan Laifuka ta Jihar Kano. Ya ce duk wanda aka samu da laifin kasancewa mamba a irin waɗannan haramtattun ƙungiyoyi na fuskantar hukuncin ɗaurin shekaru biyar aƙalla idan kotu ta same shi da laifi.
Rimingado ya ce kwamitin zai yi amfani da tattara bayanan sirri, haɗin gwiwa da hukumomin tsaro da kuma goyon bayan al'umma wajen yaƙi da laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi da tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Ya kuma yi kira ga iyaye da su ƙara sa ido kan tarbiyya da ayyukan 'ya'yansu, yana mai cewa kulawar iyaye na taka muhimmiyar rawa wajen hana shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma shigar matasa cikin ayyukan ta'addanci da laifuffuka.
A ƙarshe, shugaban kwamitin ya buƙaci kafafen yaɗa labarai, shugabannin al'umma da sauran masu ruwa da tsaki da su mara wa gwamnati baya ta hanyar wayar da kan jama'a game da illolin shan miyagun kwayoyi da safarar su ba bisa ka'ida ba.
(TE)