Za Mu Sa Kafar Wando Da Masu Ambato Juyin Mulki — Sojoji
Rayuwa ta yi tsada a Najeriya, lamarin da ya sanya wasu fara kiranye-kiranye da sojoji su yi juyin Rundunar Sojin Najeriya ta gargadi masu kiraye-kirayen juyin mulki, sakamakon matsalar tsaro da kuma tsadar rayuwa da ake fuskanta a fadin kasar nan. Najeriya dai na fuskantar matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa mafi muni a tarihi, abin da ya haifar da zanga-zanga a wasu sassan kasar nan. Wasu daga cikin ’yan kasar sun jima suna kiraye-kirayen sojoji su kifar da gwamnatin Tinubu tare da karbe iko kamar yadda aka yi a Jamhuriyar Nijar. Sai dai Daraktan Tsaro na Sojin Najeriya, Janar Christoper Musa, ya ce masu wannan kiraye-kiraye ba sa nufin kasar da alkahairi. Kazalika, dakarun sojin Najeriya za su sa kafar wando daya da masu wannan kiranye-kiranye. Ya ce abin da sojoji za su yi a yanzu shi ne kawai duba hanyoyin samar da sauki da kuma ciyar da kasar gaba, amma ba maganar juyin mulki ba. Da yake amincewa da halin matsi da ’yan Najeriya ke ciki, Janar Musa, ya ce babu inda juyin mulki