Search This Blog

Friday, 26 May 2023

Ya Kamata A Yi Wa Ruqayya Aliyu Jibia Adalci - Nasir Salisu Zango

Daga Nasir Salisu Zango 

Ruqayya Aliyu Jibia’yar jarida ce dake wakiltar gidan talabijin na Tambarin Hausa a jihar Katsina,kuma a kwanakin nan ta samu sabani da ‘yansandan jihar Katsina bayan da ta wallafa bidiyo a shafin ta na TikTok wanda a ciki ta bayyana rashin da cewar abin da ‘yansanda keyi na sakin bidiyon wadanda ake zargi da laifi musamman yadda ake nuna fuskokin su.

Amma abin takaici bayan sakin bidiyon sai Ruqayya tayi kukan cewar, ‘yansandan sun ci zarafin ta har ma an kama ta an fasa mata waya an kuma kai ta gaban sarkin Katsina wanda acan ma tace an yi tayi mata barazana. Kamar yadda ta bayyana.

Na dai tuntubi mai magana da yawun rundunar‘yansandan jihar Karsina CSP Gambo Isa wanda yace min Abin da Ruqayya take musu akan aikin su bai dace ba.
Babban abin takaicin shine a daidai lokacin da Ruqayya ke cikin firgici da barazana sai kuma muka ga gidan talabijin din da take wa aiki sun saki takardar dake cewar Ruqayya ba ma’aikaciyar su bace. Kome suke tsoro oho.

Kamar yadda kuke gani dai ga katin shaidar aiki na Ruqayya da takardar daukar ta aiki, bayan haka ma akwai shaidar biyan ta albashi da suke,kaga kenan tsakanin gidan talabijin din da Ruqayya Waye ya zukala karya?

Idan har Ruqayya tayi gaskiya to abu ne me sauki ta iya neman hakkin ta a gaban kotu.

Yanzu haka Ruqayya tace ta buya saboda firgici da take ciki,anan ina kira ga kungiyoyin kare hakkin dan adam da kungiyar CPJ me kare hakkin’yan jaridu da sauran masu fafutuka musamman lauyoyin kare hakkin marasa galihu domin kawowa Ruqayya dauki.

Shin akwai laifi a cikin bayanan da Ruqayya ta wallafa wanda har yasa ‘yansanda ke cigaba da neman ta? Yakamata a je kotu a tantance.

Gabanin Rantsuwa: Zababben Gwamnan Kano, Abba Gida Gida Ya Bayyana Kadarorinsa

Gabanin kaddamar da taron a ranar Litinin, zababben gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, (wanda aka fi sani da Abba Gida Gida) ya bayyana kaddarorin sa da kuma bashin da ake bin sa a cikin fom din da ya cike  ya mika a ranar Juma’a ga ofishin hukumar da'ar ma'aikata dake Kano 

SOLACEBASE  ta rahoto cewa  Abba wanda ya samu tarba daga Daraktar hukumar ta jihar Kano Hajia Hadiza Larai Ibrahim, ya bayyana cewa kwazonsa na bayyana kadarorinsa nuni ne na gaskiya da rikon amana da zai zama ginshikin gwamnati mai zuwa a jihar Kano.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sunusi Bature Dawakin Tofa babban sakataren yada labarai na zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya fitar a ranar Juma’a.

Ya ce: "A yau, na cika hakkin da kundin tsarin mulki ya dora min na bayyana kadarorina kafin na shiga Ofis, ranar 29 ga Mayu."

''Zababben Gwamna,  ya shaida wa mata cewa aikin gwamnati kira ne; hidima ce ga bil’adama kuma a shirye nake a koyaushe in yi hidima bayan samun amincewar mutanen jihar Kano, in ji sanarwar.

''Bugu da kari, Engr. Abba ya bayyana cewa a halin yanzu haka komai ya fito fili don tafiyar maido da ci gaba mai dorewa a dukkan bangarori, inda duk wani Kobo na asusun gwamnati da aka kashe ba kawai zai zama ta hanyar rashin gaskiya ba, har ma a jihar Kano karkashin kulawar sa.

‘’Ya ba da tabbacin cewa dukkan jami’an gwamnati da suka hada da masu rike da mukaman siyasa da za su yi aiki a gwamnatinsa za a ba su izinin bin tsarin bayyana kadarorin kamar yadda doka ta tanada.

Labari da dumiduminsa: Jirgin Nigeria Air Na Shirin Tashi Zuwa Abuja

A halin yanzu jirgin Najeriya Air wanda gwamnati ta dade tana alkawarin zai fara aiki, yana hanyarsa ta zuwa Abuja daga kasar waje
AMINIYA 

Thursday, 25 May 2023

Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Fara Tashin Alhazan 2023, Inda Yay Kira Garesu Dasu Zama Jakadu Na gari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da jigilar jigilar maniyyata aikin hajjin bana. An kaddamar da jirgin na farko a ranar Alhamis a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe International Airport Abuja. Shugaban ya kaddamar da jirgin na farko da karfe 1:30 na rana


Shugaban wanda Karamin Ministan Harkokin Waje, Ambasada Zubairu Dada ya wakilta a wajen taron ya yabawa Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) bisa nasarar shirye-shiryen Hajjin 2023.

Da yake jawabi ga hukumar ta NAHCON, Ambasada Dada ya ce "NAHCON tana yin aiki mai ban al'ajabi kuma Shugaba Buhari ya yaba da abubuwan da kuke yi tun hawan ku".

Daga nan sai shugaban ya gargadi jami’an aikin Hajji da kada su yi kasa a gwiwa, amma “ku ci gaba da tafiya. Bari wannan ya zama farkon aikin wanda shine Jin dadin Alhazai.

“Ka taimaka musu gwargwadon iko don ba su damar sauke nauyin da suke kansu na addini da suke can. Wasu daga cikinsu ba su taba yin balaguro a wajen al’ummarsu ba, aikinku yana nufin cewa an damka rayuwar wadannan mutane gaba daya a hannunku,” inji shi.


Shugaban ya kuma bukaci dukkanin ma'aikatan da su dauki nauyin da ya rataya a wuyansu, ya kara da cewa duk wani abu da hukumar NAHCON ta bukata gwamnati ce ta samar da shi don haka babu wani uzuri.

Ga maniyyatan, shugaban ya bukace su da su kasance jakadu na kwarai a Najeriya. Ya bukaci su dauki kansu a matsayin wakilan Najeriya da Musulunci.

"Ku wakilci mafi kyawun abin da Musulunci ya tsaya a kai," in ji shi.

Ya kuma bukace su da su yi addu’ar zaman lafiya a kasar da kuma gwamnati mai zuwa.

Da yake jawabi tun da farko, Gwamna Abdullahi Sule, wanda ya samu wakilcin mai martaba Sarkin Lafiya, Mai Shari’a Sidi Bage, ya yi fatan alheri ga maniyyatan da su yi aikin Hajji.


Ya kuma yi addu’ar samun sauki ga wasu alhazan da suka samu raunuka a kan hanyarsu ta zuwa Abuja a safiyar ranar Laraba.

Hakazalika ya mika godiyarsa ga hukumar NAHCON da ta baiwa jihar Nasarawa damar zama ta farko da ta tashi zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana.
IHR

EFCC Ta Kammala Shirin Kama Wasu Gwamnonin Najeriya

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, wato EFCC ta kaddamar da gagarumin bincike akan wasu

Wani bincike da Jaridar Premium Times da ake wallafawa a Najeriya ta gudanar, yace Hukumar EFCC ta baza komarta domin cafke wasu daga cikin gwamnonin da mataimakansu 28 dake shirin sallama da gidajen gwamnati a makon gobe. 

Binciken yace tuni EFCC ta bukaci takardun kadarorin da wadannan gwamnoni suka cika kafin fara aiki, wanda ya bayyana irin dukiyar da suka mallaka a wancan lokaci, yayin da kuma take dakon wadanda zasu bayar ayanzu domin nazari akansu. 

Jaridar tace hukumar tayi shiri tsaf domin ganin wadannan gwamnoni basu gudu sun bar kasar ba, bayan mika mulki ga wadanda zasu gaje su a ranar litinin mai zuwa. 

Ko a makon jiya, shugaban hukumar Abdurasheed Bawa, ya dada jaddada shirin EFCC na bin diddigin wadannan gwamnoni da mataimakansu dake shirin sauka, sakamakon korafe korafe da kuma zarge zargen da ake musu da rub da ciki da kudaden talakawa. 

Daga cikin gwamnonin da Bawa ya bayyana, akwai na Jihar Zamfara, Bello Matawalle wanda yace ana zargin sa da karkata akalar naira biliyan 70 mallakar jihar, yayin da gwamnan yace yarfe shugaban EFCC ke masa, saboda yaki bashi cin hancin naira biliyan 2 da ya nema a wurinsa. 

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Wannan dai ba shine karo na farko da EFCC ke cafke gwamnonin da suka kammala wa’adin mulkinsu ba, domin ko a shekarun baya hukumar ta cafke tsoffin gwamnoni irin su Godswill Akpabio da Ramalan Abubakar da Saminu Turaki da Sule Lamido da Danjuma Goje da Abdullahi Adamu da Jonah Jang da Joshua Dariye da Jolly Nyame da Lucky Igbenedion. 

Sai dai a wani bangare, yan Najeriya da dama na bukatar ganin hukumar EFCC ta mayar da hankali sosai akan ministocin gwamnatin Buhari da suka kawo karshen wa’adin mulkin su. 

Kungiyoyin fararen hula da dama da kuma masu fafutukar yaki da cin hanci da rashawa na zargin wasu ministocin da saba ka’idar aiki da kuma karkata kudaden gwamnati da dama zuwa mallakar kansu. 

Ko a makon jiya, sanda Hukumar ta cafke tsohon ministan wutar lantarkin Buhari, Saleh Mamman wanda ake tuhumarsa da karkata makudan kudaden gwamnati. 
RFI 



Bankuna Za Su Fara Ba Da Katin Dan Kasa Mai Hade Da Na ATM —Pantami

Gwamnatin Tarayya ta ba wa bankunan kasuwanci izinin fara ba wa abokan huldarsu katin cirar kudi na ATM da ke hade da katin shaidar dan kasa a wurin guda.

Ministan Sadarwa mai barin gado, Isa Ali Pantami, ya sanar cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince bankuna su fara bayar da katin na bai-daya ba tare da sun caji kwastomomi ko sisi a kan kudin katin ATM da aka saba ba.

“An ba wa bankuna izinin buga katunan Mastercard ko Visa da za su yi amfani a matsayin katin shaidar dan kasa ba tare da sun caji ’yan Najeriya karin kudi ba.

“Duk mai son karbar katin banki, sai ya sanar da su cewa mai hade da katin dan kasa yake so, sai su ba shi kati daya da ya hade abubuwa biyun,” in ji Pantami.
Ya bayyana cewa, Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa (NIMC) ta yi haka ne da hadin gwiwar Babban Bankin Najeriya (CBN) “domin saukaka wa duk mai bukata samun katin dan kasa ta hannun bankinsa.”

Da yake jawabi bayan zaman karshe na Majalisar Zartarwa ta Tarayya da gwamnatin Buhari ta gudanar, a Fadar a Shugaban Kasa ministan, Pantami ya bayyana cewa Dokar NIMC ta 2007, ta wajabta wa ’yan Najeriya mallakar lambar shaidar dan kasa (NIN) ne kawai.

Ya ci gaba da cewa, “A lokacin mallakar katin shaidar ba dole ba ne, ra’ayi ne; Amma sai mutane suka rika kai wa NIMC korafi cewa ba su samu katinsu na dan kasa ba.

“A kan haka ne a shekarar 2022 muka fito da katin shaidar dan kasa na zamani, wanda mutun zai iya saukewa a wayarsa, wanda kuma ke amfani ba lallai sai mutum ya buga shi a takarda ba.

“Duk da haka aka ci gaba da samun korafi, musamman daga mazauna yankunan karkara, cewa suna bukatar rike katinsu na dan kasa a hannu.

“Shi ya sa muka saukaka samun katin, inda NIMC da bankin CBN suka yi hadin gwiwa domin tabbatar da ganin mutane za su iya zuwa bankunansu su karbi katin dan kasa mai hade da ATM.”
Sai dai bai fayyace lokacin da bankunan za su fara bayar da katin na bai-daya ba.

Idan za a iya tunawa a baya CBN ya sanar da shirinsa na bullo da katin cirar kudi a banki na bai-daya, wanda mutum zai iya cirar kudi daga asusun ajiyarsa da ke bankuna daban-daban.
AMINIYA 

Wednesday, 24 May 2023

Gwamna Ganduje ya mika takardun bayar da mulki ga Dr Abdullahi Baffa Bichi

Da yake mika takardun a gidan gwamnati Alhaji Usman Alhaji ya yi nuni da cewa kwamitocin biyu suna da kyakkyawar alakar aiki yayin da suka yi musayar shirye-shirye kan yadda za a gudanar da muhimmin taron don tabbatar da mika mulki cikin sauki.

Ya bayyana cewa kwamitocin duka suna aiki ne don maslahar al’ummar Kano.

Alhaji Usman Alhaji ya yi nuni da cewa mika wuya ga gwamnati mai zuwa zai amfanar da su wajen ci gaba da yi wa al’ummar Kano hidima.

Ya kara da cewa takardun sun cika kuma suna dauke da dukkanin bayanan da ake bukata 

A nasa bangaren shugaban kwamitin Karbar Mulki na gwamnati mai jiran gado, Dr Abdullahi Baffa Bichi ya nuna godiya ga kwamitin mika mulki na jihar Kano bisa kyakkyawan aikin da aka yi wajen hada takardun mika mulki.

Ya ba da tabbacin cewa a matsayinsu na yan kwamiti,  za su duba takardun sosai kafin su mika su ga zababben gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Ya yi amfani da taron wajen yaba wa kwamitin gwamnati bisa aikin da aka yi da kuma ci gaba da hadin gwiwa a wannan fanni.

Daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a taron sun hada da gabatar da mika takardun 


Tuesday, 23 May 2023

Kwana 6 Kafin Saukar Buhari NNPC Ya Ci Gaba Da Hako Mai A Borno


Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya ci gaba da aikin hako danyen mai a yankin Tafkin Chadi da ke Jihar Borno, bayan shekara shida da dakatar da aikin.

An ci gaba da aikin ne washegarin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da Matatar Mai ta Dangote, wadda ita ce mafi girma a Afirka, wadda ake sa ran za ta taimaka wajen rage wahalar mai a Najeriya.

Kamfanin NNPP na da kaso 20 cikin 100 na hannun jarin sabuwar matatar mai karfin samar da tataccen mai ganga 650,000 a kullum, mallakin attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote.

Matata dai sa ran masana’antar da ta biya bukatun man Najeriya 100% har ta ba wa wasu kasashe 12 na Afirka, inda ake hasashen za ta rikar da kashi 36 na man da ake bukata a nahiyar.

Ana sa ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai halarci taron kaddamar da dawowar aikin Karamar Hukumar Jere ta Jihar Borno, ta intanet a ranar Talata, kwana shida kafin saukarsa daga mulki.

A shekarar 2017 ne aka dakatar da aikin neman danyen mai a rijiyoyin man masu suna Wadi-1 da kuma Kinasar-1, da ke yankin Tuba, sakamakon harin da mayakan Boko Haram suka kai wa ma’aikatan da ke aikin a lokacin.
Sai dai daga bisani, bayan bincike da samun tabbacin tsaro, NNPC ta ci gaba da aikin a shekarar 2022 rijiyar mai ta Wadi-B.

Babban Daraktan NNPCL mai kula da Hako Mai, Mukhtar Zanna, ya ce kamfanin ke amfani da fasahar zamani, kuma yana da kwarin gwiwar samun danyen mai da iskar gas da dangoginsu a rijiyar.

Shi ma a nasa bangaren, Aminu Maitama, wanda shi ne babban daraktan ayyukan hakar mai na NNPCL, ya ce, “Mun yi amannar cewa yawan danyen man da za a samu a yankin zai isa kasuwanci.”

Aikin dai ya fara samo asali ne daga shekarar 1976, da aka fara binciken gano danyen mai, a yankunan Gubio da Maiduguri da kuma Baga, kafin a ci gaba da shi a 1996.

Zan Turo Wakilai Da Za Su Halarci Bikin Rantsar Da Tinubu — Joe Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce zai turo wakilan gwamnatinsa da za su halarci bikin rantsar da sabon Shugaban Najeriya Bola Tinubu.

Biden, ta wata sanarwa a shafin gwamnatin Amurka ranar Litinin, ya ce tuni sun kafa tawagar mutane tara karkashin jagorancin Sakatariyar Raya Gidaje da Birane ta Amurka, Marcia L. Fudge da za su halarci bikin rantsuwar a Abuja, babban birnin Najeriya.

Sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta za ta fara aiki a Sudan —MDD
An samu kamfanin Facebook da laifin sayar wa Amurka bayanan jama’a

Wannan sanarwar na zuwa ne kwanaki kadan bayan sukar da tsohon dan takarar Shugaban Kasa na PDP Atiku Abubakar ya yi wa kasar, bayan da Sakataren Gwamnatin Amurka, Antony Blinken, ya taya Tinubu murnar cin zabe.

Atiku ya ce sabanin matsayin da gwamnatin Amurka ta bayyana wa duniya kan zaben da ta ce tana sane da irin magudin da aka tafka, bai kamata a ce ta amince wa zaben ba wanda akasarin al’umma suka yarda yana cike da magudi.

Baya ga wakilan Shugaban Amurkan, tsoffin Shugabannin Kasashe da dama da shugabannin manyan kungiyoyin kasashen duniya da wakilansu da dama sun amsa gayyatar halartar bikin rantsuwar.

Kazalika tsohon Shugaban Kasar Kenya, Uhuru Kenyatta zai halarci bikin, inda har zai gabatar da wata mukala ranar 27 ga wata, duk dai a cikin shirye-shiryen rantsuwar.

Za a rantsar da Tinubu, tsohon gwamnan Jihar Legas a matsayin shugaban Najeriya na 16, a ranar ta 29 a dandalin Eagle Square da ke Abuja

Tun daga ranar Alhamis za a fara gudanar da bikin inda Shugaba Muhammadu Buhari mai barin-gado zai bai wa Tinubun lambar girmamawa mafi girma ta Najeriya wato GCFR wadda ake ba shugaban kasa, sai kuma mataimakinsa Kashim Shettima wanda za a ba shi lambar da ke bi mata ta GCON.
AMINIYA 

An Sanya Wa Gadar Neja Ta 2 Da Buhari Ya Gina Sunansa

An sanya wa Gadar Neja ta Biyu, wacce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gina a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya ya kuma kaddamar da ita ranar Talata sunansa.

Hadimin Shugaban a fannin kafafen sada zumunta, Bashir Ahmad ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na Twitter ranar Talata.

Jama’a sun kashe ‘barawon babur’, sun kone gawarsa a Gombe
Buhari ya kaddamar da Titin Kano-Kaduna da Gadar Neja II
A cewarsa, “Ya ku maza da mata, yanzu a hukumance ta tabbata an sanya wa gadar Neja ta Biyu sunan Muhammadu Buhari.”

Kazalika, shi ma Hadimin Buharin a kafafen sada zumunta, Tolu Ogunlesi, shi ma ya tabbatar da labarin a shafin nasa na Twitter.

Sai dai ya ce sanya sunan kawai zai tabbata ne bayan amincewar Gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki na yankin.

“Tare da amincewar Gwamnoni da saura masu ruwa da tsakin yankin Arewa maso Gabas, yanzu za a rika kiran gadar da sunan Muhammadu Buhari,” kamar yadda ya wallafa a shafin nasa na Twitter.
AMINIYA 

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Head of Service Urges Civil Servants to Uphold Ethical Conduct

The Head of Service, Kano State, has called on civil servants to strictly adhere to the Civil Service ethical code and show grea...