Search This Blog

Sunday, 23 April 2023

Sarkin Kano Ya Bukaci Gwamnati Ta Samar Da Wata Hanyar Da Al'uma Zasu Samu Saukin Rayuwa

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci hakan ne lokacin da ya kai ziyarar barka da sallah gidan Gwamnatin jihar Kano a hawan Nassarawa da ya gabatar yau Lahadi a cigaba da gudanar da haye hayen sallah karama.

A sanarwar da babban sakataren yada labaran Sarkin, Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya sanyawa hannu, Sarkin yace sakamako matsin rayuwa da ake fama da ita akwai bukatar Gwamnati da mawadata su tallafawa marasa shi domin samun saukin gudanar da al'amuran rayuwarsu.

Ya kuma tunasar da al'uma shirin gwamnati na Kidayar al'uma da za'a gudanar a dukkanin fadin kasar nan inda ya bukaci al'uma dasu tabbatar an kidayasu a lokacin gudanar da aikin kidayar.

Mai Martaba Sarkin godewa Gwamnatin jihar Kano bisa kokarinta na samar da Tsaro da Zaman lafiya inda ya godewa Malamai da limamai wajan gudanar da addu'oi domin dorewar Zaman lafiya a jihar Kano.

Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga al'uma su cigaba da baiwa gwamnati goyon baya yace duk wasu aikace aikace da gwamnati takeyi tana yin domin al'uma.

Ya godewa Gwamnatin jihar Kano bisa kokarinta na samar da ilimi, Noma, Masana'antu da gina tituna da Gadoji inda yace wannan yasa an samu cigaban habaka tattalin arzikin jihar nan da masu saka hannun jari da kuma shigowar masu yawon bude idanu.

Daganan sarkin ya godewa Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje Khadimul tareda yi masa addu'a da fatan alheri samun matsayi na gaba sakamakon gabatowar karshen wa'adin mulkinsa.

Da yake Jawabi Mukaddashin Gwamnan Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya godewa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR bisa wannan ziyara da yakawo gidan Gwamnati ta Hawan Nassarawa inda yace wannan ziyara ce ta al'ada da aka gada daga wajan magabata.

Dr. Gawuna ya godewa al'umar jihar Kano bisa hadin kai da goyon baya da suka baiwa gwamnatinsu har na tsawon shekara 8 da sukayi suna mulki, Yana mai kira a garesu dasu cigaba da kasancewa masu bin doka da oda a kowanne lokaci.

Saturday, 22 April 2023

Ganduje Ya Yi Wa Fursunoni Sama Da Dubu Hudu Afuwa A Cikin Shekaru Takwas


 Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi afuwa ga fursunoni dubu hudu da goma sha uku a cikin shekaru takwas a fadin gidajen gyaran hali na Kano.

 Haka kuma a cikin shekaru takwas gwamnatinmu ta biyan tara da diyya ga fursunonin da suka kai naira miliyan hudu da dubu dari tara da arba’in da tara.

 Gwamnan wanda ya sami wakilcin mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana haka a lokacin da ya yi afuwa ga fursunoni 43 da suka aikata laifuka daban-daban kuma suke zaune a gidan yari, a yayin bikin karamar Sallah da aka yi a gidan yari na Goron Dutse.

Ganduje ya jaddada cewa ’yanci shi ne komai na rayuwar dan Adam, ya yi kira ga fursunonin da aka yi wa afuwar da su nuna kyawawan halaye a duk inda suka samu kansu a cikin al’umma.


A jawabinsa Kwanturola na hukumar gyaran jiki a jihar kano, Suleiman Muhammad Inuwa ya bayyana cewa matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na yin afuwa ga fursunonin da biyan tara, diyya ya taimaka wajen rage cunkoso da kuma samar da zaman lafiya a  gidajen gyaran hali dake kano.

 Ya kuma yi kira ga sauran jihohi da su yi koyi da wannan matakin sannan kuma ya bukaci wadanda suka amfana da su kasance jakadu nagari  su kasance masu bin doka da oda ta hanyar nuna kyawawan halaye.
 
A sanarwar da Sakataren yada labaran mataimakin gwamna Hassan Musa Fagge ya aikowa kadaura24, yace a nasa bangaren, Shugaban kwamitin yiwa fursunoni afuwa na jihar kano Abdullahi Garba Rano, ya mika godiyarsa ga Gwamnan bisa amfani da damar da kundin tsarin mulki ya ba shi na sakin fursunonin don.
KADAURA24 

Thursday, 20 April 2023

Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Gudanar Da Taron Shan Ruwa Na Mutum Dubu Biyu

Zababben Dan majalisar  tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa (Jarman Bebeji) ya jagoranci taron shan ruwa da al'umar Kiru da Bebeji mutane 2000 a gidansa dake garin Kofa.

Bayan buda baki Kofa ya jagoranci mahalatta wannan taro Sallah. 

Taron shan ruwan ya sami halartar Dagatai, Limamai, 'Yan siyasa, da sauran mutane daban-daban dake mazabarsa ta dan majalisar tarayya 

Yayin taron, anyi amfani da wannan dama wajen yi wa Zababben Dan Majalisar Tarayyar, Alhaji Abdulmumin Jibrin Kofa addu'a da  Gwamna jihar Kano mai jiran rantsuwa Injiniya Abba Kabir . Yusif tare da Jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Haka kuma an roki madaukakin Sarki Allah ya dauwamar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jahar Kano da ma Najeriya baki daya

Fiye da mutane 85 sun mutu a turmutsitsin rabon kudi a Yemen

 


Akalla mutane 85 suka mutu, wasu daruruwa kuma suka jikkata, sakamakon tirmtsitsi da aka yi yayin wani taron raba kudade da aka yi a Sanaa, babban birnin kasar kasar Yemen da ke karkashin ikon ‘yan tawayen Houthi.

Ya zuwa yanzu mutane 3 aka tsare bisa zarginsu da hannu wajen haddasa tirmitsitsin da sanyin safiyar ranar Alhamis, bayan da daruruwan mutane suka taru a wata makaranta domin karbar kyautar kudin Riyal din kasar ta Yemen 5,000, kwatankwacin dalar Amurka 8 da ake bai wa mutum guda guda, a daidai lokacin da watan Ramadan mai alfarma ya zo karshe.

Hotunan bidiyo sun nuna yadda mutanen da mummunan cinkoson ya rutsa da su, suka rika tsala ihu da neman ceto sakamakon kasa motsawar da suka yi, yayin da wasu tsiraru suka rika yunkurin fitar da mutanen da suka ji rauni.

Wasu hotunan bidiyon kuwa, sun nuna gawarwakin wasu daga cikin wadanda tirmitsitsin ya rutsa da su ne yashe a kasa, sai kuma tarin takalma da sauran nau’ikan tufafin da aka yi watsi da su, yayin da kuma wani mai bincike ke tattara wasu daga cikin abubuwan da aka yasar a matsayin shaidu.

Wani jami’in tsaron Houthi da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewar akalla mutane 85 suka mutu cikinsu har da mata da kananan yara, wasu fiye da 322 kuma suka jikkata.

RIF

Labari Da Dumiduminsa: An Wa Watan Sallah A Saudiyya

 


Hukumomin Saudiyya sun sanar da ganin watan Shawwal na sallah a ranar Alhamis 20 ga watan Afrilun 2023.

An ga watan ne a yankin Tumair na Saudiyya kamar yadda kwamitin duban wata na yankin ya bayyana, hakan na nufin Saudiyya ta kammala azumin Ramadan 29.

Gobe Juma'a 21 ga watan Afrilu zai zama 1 ga watan Shawwal.

Wednesday, 19 April 2023

Abu bakwai da ya kamata ku yi don tafiya sallar Idi

Sallar Idin ƙaramar salla Ibada ce da Allah Ya shar'anta a matsayin kammala Ibada ta azumin watan Ramadan.

Sallar Idi na ɗaya daga cikin sunnoni masu ƙarfi a addinin musulunci wadda ake yi sau biyu a shekara wato, ƙaramar salla da babbar salla.

Don haka ne ma sallar idin ke buƙatar wasu abubuwa domin yin guzuri a tafiya zuwa masallacin idin.

Dakta Muhammad Nazifi Inuwa wani malamin addini ne a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ya bayyana jerin abubuwan da ya kamata mutum ya yi kafin tafiya sallar idi.

Wankan Idi
Wankan Idi É—aya ne daga cikin wanka na sunnah a addinin musulunci wanda ake yi sau biyu a shekara.

Dakta Muhammad Nazifi Inuwa ya ce an so duk mai tafiya masallacin idi ya gabatar da wankan Idi, domin dacewe da sunnah.

Dangane da wankan, dakta Nazifi ya ce mutum zai iya yin wanka na soso da sabulu domin tsaftace jikinsa, sannan daga baya kuma sai ya yi wankan idin, domin dacewa da ladan sunnar wankan.

Haka kuma malamin ya ce sigar wankan iri ɗaya ne da na sauran wankan addinin muslunci, kamar na janaba, da na ɗaukewar jinin al'ada ko na biƙi, sai dai kawai niyya ce ta bambanta.

Tsaftace jiki
Malamin ya ce tsafta na daga cikin ladubban addinin musulunci, don haka kasancewar ranar Idi rana ce ta musamman, yana da kyau mutum ya ƙara tsaftace jikinsa.

''Wannan ko ya haɗar da aske gashin hammata da na gaba, da aske ƙumba ko farce'', in ji Dakta Muhammad Nazifi.

Malamin addinin ya ci gaba da cewa ''an so mutum ya tsaftace jikinsa ta yadda zai je masallaci ba tare da ya cutar da masallata, da warin jikinsa ba''.

Cin abinci'
A na taruwa a ci abinci tare da 'yan uwa ranar salla
'Ya kamata a samu wani abu a ci kafin tafiya masallacin idi'

Dakta Muhammadu Nazifi ya ce idin ƙaramar salla da babbar salla ya bambanta ta fuskar cin abinci.

''A idin ƙaramar salla ba a so mutum ya tafi masallaci ba tare da ya ci wani abinci ba, domin kada ya je Idi kamar yana azumi'', in ji Malamin.

Dakta Ibrahim Abdullahi ya ce ''ya kamata a samu wani abu a ci kafin tafiya masallacin idi ko da kuwa dabino ne, ko wani abu ko ruwa''.

''Amma a Idin babbar sallar musamman idan mutum zai yi layya to an so ya jinkirta cin abinci har sai ya dawo daga masallacin Idi, ya yanka dabbar layyarsa a gasa masa wani ɓangare na naman dabbar ya fara da shi'', in ji Dakta Muhammadu Nazifi
Yawaita kabarbari
Dakta Nazifi ya ce ana so mai tafiya masallaci ya ci gaba da kabarbari. Dakta Nazifi ya ce ya zo a cikin ruwayoyi masu yawa na irin kabarbarin da za a riƙa yi.

''Allahu Akbar, Allahu Akbar, La'ilaha illallah Allahu Akbar, Allahu Akbar walillahil hamdu'', Malamin ya ce haka mutum zai riƙa fada, kuma da sauti mai ƙarfi ta yadda zai jiyar da na kusa da shi.

Malamin ya ce hikimar yin kabarbarin cikin sauti mai ƙarfi shi ne don tunatar da waɗanda suka manta da yin kabarbarin.

Dakta Nazifi ya kuma koka kan abin da ya ce wasu matasa ke yi a lokacin tafiya masallacin idin, inda ya ce sai ka ga wasu matasan sun shagalta da hirarrakin duniya a kan hanyarsu ta tafiya masallacin idin.

'Ba a yin sallar nafila gabanin sallar Idi'

Dakta Nazifi ya ce idan mutum ya isa masallacin Idi, abin da ake son ya yi shi ne ya zauna jiran ƙarasowar liman, tare da ci gaba da kabarbari.

''Ba a yin sallar nafila gabanin sallar Idi don haka abin da ake son mutum ya yi shi ne ya zauna jiran isowar liman, ya kuma ci gaba da kabarbari'', in ji malamin.

Ya ƙara da cewa ''da zarar liman ya iso masallaci babu abin da zai yi kawai sai tayar da sallah ba tare da ɓata lokaci ba.

Haka kuma ana so a zauna a saurari hudubar liman, bayan kammala sallar, ba a son daga sallame sallah a fice daga masallaci don tafiya gida.

Duk da cewa ba wajibi ba ne, amma malamai na cewa yana daga cikin alherin da Annabi SAW ya yi nuni da shi domin samun albarkar addu'ar musulmi da ake yi a cikin huÉ—ubar.


Sauya hanyar komawa gida
Haka kuma an so mutum idan zai koma gida daga masallacin idi, to inda hali ya sauya hanya, kada ya bi ta hanyar da ya bi wajen zuwa masallacin, a lokacin da ya tashi komawa gida.

Dakta Ibrahim Abdullahi Rijiyar Lemo ya ce ''an karbo hadisi daga Jabir ɗan Abdullahi, yana cewa Manzon Allah SAW yana saɓa hanyar zuwa da ta dawowa daga sallar idi''.

Dakta Muhammad Nazifi Inuwa ya shawarci waɗanda gidajensu ke kusa da masallatan Idin da su tafi a ƙafa matuƙar yin hakan ba zai cutar da su ba.

Domin kuwa hakan ma bai fi tsinka jini ba, sannan kuma hakan zai rage cunkoson ababen hawa tare da sauƙaƙa wa jama'a, kamar yadda malamin ya ce.
BBC 

Tuesday, 18 April 2023

INEC Ta Bayyana Gwamna Ahmadu Fintiri A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Jahar Adamawa

Hukumar zaɓe a Najeriya ta sanar da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar Adamawa, wanda ya ƙare cikin taƙaddama.

Jami'in sanar da sakamakon zaɓen gwamna na Adamawa, Farfesa Mohammed Mele ya ce Ahmadu Fintiri ya yi nasarar lashe zaɓen ne da ƙuri'a, 430, 861.

Gwamnan mai ci ya samu nasara a kan babbar abokiyar fafatawarsa Aisha Ɗahiru Binani wadda ta samu ƙuri'a, 398, 788.

Wannan nasara ta bai wa Fintiri ikon ci gaba da mulkin jihar Adamawa a wa'adi na biyu.

Da yammacin Talata ne, jami'in sanar da sakamako, Farfesa Mohammed Mele cikin rakiyar wasu manyan jami'an INEC na ƙasa, ya isa zauren karɓar sakamako da ke Yola, inda ya ci gaba da aikin tattara sakamakon ƙananan hukumomin da suka rage.

A ranar 15 ga watan Afrilu ne, hukumar zaɓe ta gudanar da cikon zaɓen cikin wasu rumfuna da ke faɗin ƙananan hukumomin jihar 20.

An sake kaɗa ƙuri'u ne a tashoshin zaɓe 69.

Sakamakon zaɓen da aka ƙarasa ya nuna cewa 'yar takarar jam'iyyar APC, Aisha Binani ta samu ƙuri'a 6,513, yayin da Gwamna Fintiri na PDP ya samu 9,337.

Zaɓen dai ya gamu da taƙaddama bayan kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa Hudu Ari ya sanar da Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen ba tare da ya fayyace sakamakon kowacce jam'iyya dalla-dalla ba.


ne a Yola tare da rakiyar 'yan sanda da safiyar Lahadi, inda ya ayyana Sanata Aishatu Binani ta APC a matsayin wadda ta lashe zaɓen.

Bai dai yi bayani filla-filla na sakamakon da kowacce jam'iyya ta samu, da kuma yadda aka yi Aisha Binani ta ci zaɓen ba.

Sai dai cikin wata sanarwa da babban jami'inta kan yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe na ƙasa, Barista Festus Okoye ya fitar, INEC ta ce matakin da kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa - REC ya ɗauka na sanar da wanda ya lashe zaɓe haramtacce ne, don haka ta ce ba za a yi amfani da shi ba.

INEC ta kuma ce Hudu Ari ya sanar da sakamakon ne a lokacin da ba a riga an kammala aikin tattara sakamakon zaɓen ba.

Lamarin dai ya janyo ruɗani a Najeriya, inda a Adamawa 'ya'yan jam'iyyar PDP suka shiga gudanar da zanga-zanga don matsa lamba ga hukumar zaɓe ta kammala aikin sanar da sakamako.

A zaɓen ranar 18 ga watan Maris, INEC ta bayyana gwamna mai ci Ahmadu Umar Fintiri da cewa ya samu ƙuri'a 421,524.

Sai babbar abokiyar fafatawarsa ta jam'iyyar APC, Sanata Aisha Dahiru Binani wadda ta samu ƙuri'a 390,275.

Ita ce mace ta farko da ta taɓa zuwa wannan mataki na zaɓen da aka ƙarasa a takarar gwamna, tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokraɗiyya a 1999.


Tuni dai aka ga wasu magoya bayan gwamnan a kan tituna suna shagulgulan nasarar da Gwamna Ahmadu Fintiri ya samu.
BBC 

LABARI DA DUMIDUMINSA : INEC Ta Dauki Matsaya Dangane Da Zaben Adamawa

A taronta na yau, 18 ga Afrilu, 2023, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, ta tattauna batutuwan da suka taso daga zaben Gwamnan Adamawa inda ta yanke shawarar:

1. Rubuta takarda zuwa ga Sufeto-Janar na 'yan sanda domin gudanar da bincike cikin gaggawa tare da yiwuwar gurfanar da Kwamishinan Zabe na Jihar Adamawa, Barr. Hudu Yunusa Ari.

2. Ya bukaci sakataren gwamnatin tarayya da ya jawo hankalin hukumar da ke nadawa kan rashin da'a na REC don ci gaba da daukar mataki.

3. Za a ci gaba da tattarawa a daidai lokacin da Jami'in da jami'in tattara sakamakon ya amince

Cikakken bayani zai biyo baya nan ba da jimawa ba.
INEC 

Yau INEC Za Ta Taron Gaggawa Kan Zaben Adamawa

A yau Talata Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za ta gudanar ta taron gaggawa da ta kira kan dambarwar sakamakon zaben gwamnan Jihar Adamawa da ya tayar da kura.

Daga taron ne za a ji shawarar da INEC ta yanke a game da sakamakon zaben gwamnan, wanda a ranar Lahadi hukumar ta dakatar da tattarawa saboda rikicin da ya dabaibaye shi.


A ranar Litinin hukumar ta dakatar da Kwamishinan Zabe (REC) na Jihar Adamawa, Barista Hudu Yunus Ari, saboda ya yi gaban kansa wajen ayyana Sanata Aisha Dahiru Binani ta Jam’iyyar APC a matsayin zababbiyar gwamna, alhali ba a kammala tattara sakamakon zaben ba.

Lamarin dai ya yamutsa hazo, amma Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, wanda yake neman a zaben a Jam’iyyar PDP, ya bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu, domin INEC za ta dauki matakin da ya dace.


Tuni dai Fintiri da PDP da kungiyoyin kare dimokuradiyya suka yi tir da abin da kwamishinan zaben ya yi, inda suka bukaci INEC ta dauki mataki a kan wannan kwamacala.

Rikicin zaben ya dauki sabon salo ne a safiyar Lahadi a yayin da ake tsaka da jiran lokacin da za a karbi sakamakon kananan hukumomi 10 bayan an karasa zaben a ranar Asabar, amma Barista Hudu ya yi riga-malam-masallacin sanar da cewa Binani ta yi nasara.

Amma daga bisani Hedikwatar INEC ta soke ayyanawar da da Hudu ya yi, cewa haramtacce ne, ba shi da tasiri, sannan ba huruminsa ba ne sanar da sakamakon zabe, aikin Jami’in Tattara Sakamakon Zaben, Farfesa Mele Mohammed ne.


Daga nan Hukumar ta ba da umarnin dakatar da tattara sakamakon zaben, sannan ta umarci Hudu da Farfesa Mohammed da wakilan jam’iyyun da suka shiga zaben da sauran masu ruwa da tsaki su bayyana da hedikwatarta da ke Abuja domin lalubo bakin zaren.


An gudanar da karashen zaben ne a ranar 15 ga watan Afrilu, bayan da INEC ta ayyana wanda aka fara gudanarwa a ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammalu ba, saboda soke kuri’un wasu rumufanan zabe da aka yi sakamakon aringizon kuri’u da rigingimun da aka samu a lokacin zaben na farko.
AMINIYA 

Monday, 17 April 2023

DA DUMI DUMI: INEC Ta Dakatar Da Kwamishinan Zabe Na Adamawa, Ta Kuma Gargade Shi Da Ya Nisanci Ofis

 


Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta umurci Kwamishinan Zabe na Jihar Adamawa Malam Hudu Yunusa-Ari da ya yi gaggawar ficewa daga ofishin jihar har sai an sanar da shi.

 

INEC ta bayar da wannan umarni ne a wata wasika mai dauke da kwanan watan 17 ga Afrilu, 2023 mai dauke da sa hannun Sakatariyar Hukumar, Misis Rose Oriaran-Anthony.

 

Hukumar a cikin wasikar mai taken “Hukumar Hukumar ta nisantar da INEC, Jihar Adamawa,” ta kuma umurci sakataren gudanarwa na jihar da ya dauki nauyin ofishin jihar nan take.

 

Wasikar ta kasance kamar haka: “Ina isar da hukuncin Hukumar cewa kai (Hudu Yunusa-Ari), Kwamishinan Zabe na Jihar Adamawa, ka nisanci ofishin hukumar a Jihar Adamawa cikin gaggawa har sai wani lokaci.

 

“An umurci sakataren gudanarwar da ya dauki nauyin hukumar INEC, jihar Adamawa ba tare da bata lokaci ba.

 

"Don Allah, a yarda da tabbacin da hukumar ta yi."

 

A ranar Asabar ne Yunusa-Ari ya ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Adamawa yayin da har yanzu ba a kammala tantance sakamakon zaben kananan hukumomi ba.

 

Sai dai hedkwatar INEC ta bayyana matakin da ya dauka a matsayin batacce ne, inda ta dakatar da aikin tattara sakamakon zaben; sannan ya umarce shi da duk wanda ke da hannu a wannan mataki da su kai rahoto Abuja.

 

Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban, yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a Festus Okoye ne ya tabbatar da wasikar a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja.

 

Ya ce REC, wanda aka gayyace shi hedikwatar INEC a ranar Lahadi, ana sa ran har zuwa lokacin cike wannan labari da karfe 3:30 na rana.

 

“An umurci REC da ta bayar da rahoto a yau (Litinin). Har yanzu muna jiransa,” Okoye ya shaidawa NAN.(NAN)

 


Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Head of Service Urges Civil Servants to Uphold Ethical Conduct

The Head of Service, Kano State, has called on civil servants to strictly adhere to the Civil Service ethical code and show grea...