Search This Blog

Wednesday, 18 January 2023

Mun Kashe $1bn Wajen Kwato Yankunan Da ’Yan Ta’adda Suka Mamaye – Buhari


Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce Najeriya ta kashe sama da Dala biliyan daya wajen sayen makaman da ta yi amfani da su wajen yaki da ’yan ta’adda tun 2015.

Buhari ya bayyana haka ne ranar Talata sa’ilin da yake jawabi a wajen Babban Taron Zaman Lafiya na Afirka na 2023, da ya gudana a birnin Nouakchott, Jamhuriyar Musulunci ta Murtaniya.


Shugaban wanda aka karrama da lambar yabo ta “Karfafa Zaman Lafiya a Afirka” a Abu Dhabi, ya ce akwai bukatar a rungumi dabi’ar karrama juna da mutuntawa a makarantu, musamman kuma a tsakanin matasa.

Haka nan, ya yi kira ga shugabanni da su bai wa rayuwar matasa muhimmanci ta hanyar horar da su sana’o’in hannu domin maganin zaman kashe wando.

Cikin sanarwar da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Femi Adesina, Buhari ya ce dole a ba da himma wajen hana ta’ammali da kananan bindigogi da sauran makamai a cikin al’umma.

Kana ya bukaci yayin taron kasashen Afirka na gaba, a dauki matakin lalubo hanyar magance matsalolin da ke ci gaba da yi wa kasar Libiya tarnaki wanda hakan ya sa kasar ta zama dandalin ta’ammali da makamai da mayakan ketare.

“Ta’addanci da fashin daji da sauran

Ya kara da cewa kafewar Tafkin Chadi ta haifar wa al’ummar yankin rasa hanyoyinsu na samun masarufin rayuwa wanda hakan ya yi sanadiyyar jefa dimbin matasan yankin cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda.


A karshe, Buhari ya yi godiya ga Majalisar Zaman Lafiya ta Abu Dhabi karkashin jagorancin Shaykh Abdallah Bin Bayyah, bisa karrama shi da ta yi da lambar yabon.



Tuesday, 17 January 2023

Kotu Ta yi Sammacin Emefiele kan badakalar Dala Miliyan 53

Babbar Kotun Abuja ta sammaci Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, a kan ya bayyana gabanta ranar Laraba dangane da shari’ar sama da Dalar Amurka miliyan 53 na kudaden ‘Paris Club’.

A wata kara da aka shigar gaban kotun ranar 20 ga watan Oktoban 2022, Alkalin kotun, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya bai wa Emefiele odar ya bayyana a gaban kotun ran 18 ga Janairu don sauraron shari’ar.

Umarnin kotun ya biyo bayan karar da lauya Joe Agi, ya shigar ne kan kamfanin Linas International Ltd da Ministar Kudi da CBN ta hannun lauyoyinsa, Isaac Ekpa da Chinonso Obasi.

A cikin karar, yana neman kotu ta bai wa Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda odar cafke Emefiele da lauyoyinsa tare da gabatar da su ga kotu.K

Karar ta taso ne kan hukuncin Dala miliyan 70 da aka yanke wa Linas kan ayyukan lauyoyi game da kudin Paris Club, wanda aka ce Emefiele ya saki Dala miliyan 17 sannan Dala miliyan 53 sun makale.

A ranar 23 ga Janairu, 2020 kotu ta yanke hukuncin cewa dole Emefiele ya bayyana “a yi masa shari’a kan rantsuwar da ya shafi hanyoyin da kake da su ko kuma ka samu, tun daga ranar da aka ba da cikakken umarni, na biyan bashin Dala miliyan 53 a halin yanzu kuma za a biya a karkashin wannan umarnin kuma ya nuna dalilin da ya sa ba za a tura shi kurkuku ba na rashin biyan kudin.”

'Yan Najeriya Miliyan 25 na cikin barazanar yunwa a Shekara ta 2023


Adadin dai kari ne kan mutane miliyan 17 da ke cikin hadarin gamuwa da yunwar a Najeriya wanda aka yi hasashe tun a can baya.

Sanarwar da Hukumar Bunkasa Ilimin Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a shafinta, ta ce, rikice-rikice da matsalar sauyin yanayi da tashin farashin kayayyakin abinci, su ne ummul-haba’isin jefa ‘yan Najeriyar cikin kangi yunwa.

Sanarwar ta ce, an gaza samar da abinci a jihohin Borno da Adamawa da Yobe da ke yankin arewa maso gabashin Najeiya sakamakon tashe-tashen hankula, ga kuma hare-haren ‘yan bindiga a jihohin Katsina da Sokoto da Kaduna da Benue da kuma Niger.

Alkaluman da Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Najeriya NEMA ta fitar sun nuna cewa, matsalar ambaliyar ruwa da aka gani a bara, ta lalata sama da kadada dubu 676  na gonaki, lamarin da ya sa aka samu karancin girbi tare da fuskantar barazanar karancin abinci a kasar.

Bayanai na nuni da cewa, ambaliyar ruwan dai, na daga cikin tasirin sauyin yanayi da ke addabar duniya.

Dan shugaban kasar Guinea ya sace jirgin sama na gwamnati


An tsare Ruslan Obiang Nsue a ranar Litinin, sannan aka yi masa daurin talala kamar yadda kafar talabijin ta kasar ta bayyana.

Tun a cikin watan Nuwamban da ya gabata, aka kaddamar da bincike bayan hukumomi sun gano cewa, daya daga cikin jiragen gwamnati mai lamba ATR 72-500 ya yi batan-dabo  a filin jiragen sama na kasa da kasa.

A shekarar 2018 ne aka tura wannan jirgin zuwa kasar Spain domin kula da lafiyarsa, yayin da aka zargi Obiang da sayar da shi ga kamfanin Binter Technic, mai kula da lafiyar jirage a Las Palmas da ke tsibirin Grand Canary a Spain din.

Jirgin dai na daukar fasinjoji 74 kuma tun a tsakan-kanin shekara ta 1980, kamfanin ATR na hadin guiwa tsakanin Italiya da Faransa ya kera shi.

Da ma dai  Equatorial Guine ta yi kaurin suna a fannin cin hanci da rashawa, inda kungiyar Transparency International ta ayyana ta a matsayin ta 172 daga cikin jerin  kasashe 180  da suka fi kwarewa a rashawa a shekara ta 2021.

A bangare guda ana kallon mahaifinsa, shugaba Teodoro Obiang Nguema da yin mulkin kama-karya a kasar.

(RFI) 

A shirye muke don zuwa zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasa - Shugaban INEC

Shugaban Hukumar Zaɓe mai zaman ƙanta a Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya ce hukumarsa a shirye take game da zuwa zaɓen zagaye na biyu na shugaban ƙasar idan har ba a samu wanda ya yi nasara a zagayen farko ba.

Farfesa Yakubu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi kan shirye-shiryen hukumar na tunkarar babban zaɓen ƙasar da ke tafe a Chatham House da ke birnin Landan a Birtaniya.

Ya ƙara da cewa a INEC ta yi shirin yiyuwar zuwa zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasar, kamar yadda take yi a zaɓuka uku da suka gabata.

Shugaban hukumar zaɓe ya kuma ce zaɓen ƙasar da za gudanar cikin wannan shekara zaɓe ne na matasan ƙasar.

Farfesa Yakubu ya kuma ce rajistar masu kaɗa ƙuri'a ta nuna cewa matasa ne suka mamaye adadi mafi yawa na masu rajistar zaɓen.

Shugaban Hukumar ya ce ya ji daɗin yadda mutane suka fito domin karɓar katinan zaɓensu, yana mai cewa fiye da mutum 600,000 sun karɓi katinansu a jihar Legas kaɗai cikin watan da ya gabata.

Ya ƙara da cewa a yanzu adadin masu rajistar zaɓe a Najeriya sun kai miliyan 93.4, kuma daga ciki miliyan 37 wato kashi 39 na rajistar zaɓen matasa ne 'yan tsakanin shekara 19 zuwa 34.

Ya kuma tunasar da maharta taron cewa hukumar za ta tsayar da rabar da katin zaɓen daga ranar 29 ga watan Janairun da muke ciki.
(BBC HAUSA) 


Gwamnatin Kano ta kori 'yan mata biyu daga gidan marayu kan zargin tayar da husuma

Hukumomi a jihar Kano ta kori wasu 'yan mata daga gidan marayu na gwamnatin jihar.

Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne saboda 'yan matan ba sa bin ƙa'idar zaman gidan tare da ƙoƙarin tayar da husuma tsakanin marayu da ma’aikata.

Sai dai marayun sun ce wasu ma’aikatan gidan ne ke cin zarafinsu ta hanyar ƙoƙarin yin lalata da wasu daga cikinsu.

Ma’aikatar harkokin mata da walwalar al‘ummar ta jihar Kano, ta ce ta kori ‘yan matan biyu daga gidan marayun na Nasarawa ne saboda rashin kiyaye ka’idoji da dokokin zaman gidan.

Sai dai waɗannan ‘yan mata sun ce saboda sun kwarmata lalatar da ake zargin wani ma’aikacin gidan ne ya sa aka kore su, kamar yadda ɗaya daga cikinsu ta shaida wa Majiyarmu 

Ta ce ''saboda yana da mabuɗin sito a hannansa, yana ganin kamar shi ke da iko da gidan gaba ɗaya, sai muka je muka gaya wa shugabar gidan, daga baya sai ta zo ta ce ai mun yi masa ƙazafi, daga sai suka rubuta takarda suka kai wa Kwamishina, ita kuma ta bayar da umarnin da a rubuta takarda wai an kore mu, daga baya aka zo aka kira mu aka yi mana wa'azi, cewa mu yadda da ƙaddara mai kyau da marar kyau''

Daga nan sai a ka sanar da su cewa gwamna ya bayar da umarni a kore su daga gidan tun da za su janyo masa matsala kamar yadda ta shaida wa majiyarmu .

Ta ƙara da cewa ''mun ɗauki matakin bayyana abin da ma'aikacin gidan ke yi wa 'yan matan da ke gidan ne, saboda 'yan matan da yake lalata da su 'yan uwanmu ne, dan haka bai makata mu yi shiru ba''

Dan haka a cewarsu bai makata a ajiye ma'aikaci ba amma kuma ya riƙa cin amanar yara da gwamnati.

Daga ƙarshe 'yan matan sun yi kira ga gwamnati da ta shiga cikin lamarin tare da taimaka wa wajen samar musu da wurin zama.

Haka kuma 'yan matan sun ƙaryata batun zargin da ake yi musu na tunzura sauran yara da kuma fita daga gidan kuma ba sa dawowa sai lokacin da suka ga dama, domin kuwa a cewarsu suna zaman lafiya da sauran yaran.
(BBC HAUSA) 

Dole ’Yan Magani Su Koma Kasuwar Dan Gwauro A Watan Fabrairu – Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ba gudu ba ja da baya kan batun mayar da masu sayar da magani kasuwar duniya ta Dan Gwauro ranar 10 ga watan Fabrairu mai zuwa.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa Kwamishinan Kasuwanci na Jihar, Barista Ibrahim Muktar ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da filin Inda Ranka na gidan rediyon Freedom da ke Kano, inda ya ce gwamnatin ta riga ta kammala duk wani shirin da ya kamata na tarewarsu

A cewar Kwamishinan, “Ka san mutane ba sa son canji daga wajen da suka saba, ko mai kyau ne ko mara kyau ne, sai daga baya zaka ga an zo ana rububin komawa can.

“Duk da muna sane da masu kokarin yin zagon kasa ga irin wannan shirin. Su kuma ba za mu kyale su ba idan muka zakulo su.

“Muna neman wata alfarma a matsayinmu na masu kananan karfi a kasuwar ’yan magani.

Wannan guri ya yi karanci, kuma yanzu haka a cikin kaso 100 na ’yan kasuwar, ba na jin kaso 17 sun samu wurin zama.

“Don haka muna rokon gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su taimaka mana a kara wa’adin da za mu samu damar shiga wurin cikin nutsuwa”, in ji wani dan kasuwa.


“Wannan shirin na gwamnati ya biyo bayan korafin da al’umma ke yi tsawon lokaci cewa ’yan kasuwar na fake wa da sana’ ar suna sayar da jabun magunguna da miyagun kwayoyi ga masu shaye-shaye,” in ji Kwamshinan.

Kasuwar ta Da Gwauro dai na dab da shiga Kano ne a kan babban titin Zariya zuwa Kano, kuma tuni aka kammala kaso mai yawa na shagunan cikinta.

Malaman Makaranta Sun Fara Yajin Aiki A Ingila Kan Karin Albashi


Malaman makaranta a Ingila da yankin Wales sun sanar da tsunduma yajin aiki daga watan Fabrairu mai zuwa saboda karin albashi.

Kungiyar malaman mai suna (NEU) ta ce mambobinta sun amince da gagarumin rinjaye a fara yajin aikin har sai an yi musu karin da zai yi daidai da yanayin hauhawar farashin kayayyaki a kasar.

Bayan wata 11, farashin kayayyaki ya sauka a karshen 2022 a Najeriya – NBS
Kotu ta yanke wa mutum 6 hukuncin kisa ta hanyar rataya a Osun
Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin ma’aikatan gwamnatin kasar da dama ke guna-guni kan karancin albashi.

“Mun tabbatar gwamnati ta san akwai bukatar a gyara albashin malaman makaranta,” in ji Kevin Courtney, Babban Sakataren NEU, yayin wani taron kungiyar da aka watsa kai tsaye.


Shugabannin kungiyar dai na shirin ganawa da Ministan Ilimin kasar ranar Laraba.

Shi ma wani Sakataren kungiyar, Mary Bousted, ya ce, “Sun san ba da wasa muke ba. Da gaske muke yi wajen kokarin kare ayyukanmu.”

Kungiyar dai ta sanar da fara yajin aikin ne daga ranar daya ga watan Fabrairu mai zuwa, sannan za ta shafe kimanin kwana shida tana yin yajin aikin a matakan yankuna a watan Fabrairu da Maris masu zuwa.

Sai dai ta ce kowacce makaranta yajin aikin zai shafe ta ne na tsawon kwana hudu.

Ko a cikin makon nan a Ingila da Wales da Arewacin Ireland, ana sa ran ma’aikatan lafiya na Nas-nas ake sa ran su dawo yajin aikinsu a ranakun Laraba da Alhamis.
(AMINIYA) 


Gwamnatin Kano Ta Musanta Cin Zarafin Yara A Gidan Marayu

 


Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da rahoton zargin cin zarafin yara da wasu jami’anta suka yi a gidan marayu da ke Nassarawa a jihar.

Kwamishinar Harkokin Mata da Ci Gaban Al’umma ta jihar, Dakta Zahra’u Muhammad Umar, ta yi watsi da rahoton yayin da ta zanta da manema labarai a ranar 

“Wasu masu yin barna ne suka hada labarin don bata sunan gwamnatin jihar nan.

“Amma abin da ta faru shi ne ba mu da hurumin ci gaba da zama da kuma kulawa da yaran da suka haura shekara 18 a gidan marayu. Doka ma ba ta ba mu wannan damar ba.“An bukaci wasu mutum biyu, Ladidi da Saudat da su bar gidan marayun tun da yanzu sun zama manya.”

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa kwamishinar Ta bayyana cewa matan biyu, wadda daya daga ciki bazawara ce, dayar kuma na da aure har da ’ya’ya uku, sun ki barin gidan sannan sun shiga yi wa kwamishinar bita da kulli da sauran ma’aikatan don bata musu suna.

“Sun shiga gidan rediyon sun yi kazafin cewar ana cin zarafin yara, ana kai su wurare daban-daban ba bisa ka’ida ba.”Ta ce gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti wanda ya gudanar da bincike sannan ya gano zargin karya ne, inda ta ce kwamitin ya yanke shawarar cewa Ladidi da Saudat su bar gidan saboda sun haura shekara 30.“Lokacin da na zama kwamishina, na tausaya wa manya, na zama uwa gare su, na sanya wasu daga cikinsu a manyan makarantu.”

Ta ce gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na daukaka darajar rayuwa a tsakanin ‘yan kasa ta hanyar manufofi da tsare-tsare.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin binciken, Alhaji Kabiru Zubairu, ya ce kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa ya kunshi mambobi tara da za su kula da yadda ake kulawa da marayun.

Kwamitin ya hada da Jami’in ‘yan Sanda a matsayin Sakatare, REPA, Darakta (Yaron Ma’aikatar), Masanin Ilimi daga Ma’aikatar Ilimi, Jami’in Shari’a, Likita da Jami’an Jin Dadin Jama’a a matsayin mambobi.

Monday, 16 January 2023

Hukumar DSS Ta Musunta Mamaye ofishin Gwaman Babban Bankin Najeriya


Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta mamaye harabar babban bankin Najeriya, a ranar Litinin, kamar yadda ake yada labarin a yanar gizo.

Rundunar ‘yan sandan sirrin a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar tsaron ta farin kaya, Peter Afunanya ya fitar ta ce labarin karya ne.

Idan dai za a iya tunawa a ranar Litinin din da ta gabata ne aka ga motocin a harabar babban bankin da ke Abuja.

Hukumar ta DSS a cikin sanarwar ta ce jami’anta ba su yi yunkurin kama gwamnan na CBN ba.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Presidential delegation pays condolence visit to Hamza Darma’s family in Kano

A high-powered presidential delegation has paid a condolence visit to the family of late Alhaji Hamza Usman Darma, a prominent K...