Tsadar Kayan Abinci: Hukumar Yaki Da Cin Hanci Ta Kano Za Ta Fara Kama Dukkanin Wadanda Ta Samu Suna Boye Kayan Abinci

Shugaban Hukumar, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a ofishinsa

Muhuyi Magaji ya ce " ..a dokar jahar Kano, boye kayan abinci haramun ne" don haka zamu dauki matakin da ya dace kan masu aikata hakan.

Shugaban Hukumar ya ci gaba da cewa duk da cewar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gudanar da zama na musammam tare da manyan 'yan kasuwa, Amma yace hakan na zai hana ofishinsa nasa yin abun da ya dace ba, kasancewar daman hukumar na karkashin Ofishin Gwamnan ne.

"Mun yi wani aiki a baya wanda al'uma suka ji dadin shi, don haka mun karbi kiraye - kiraye ta hanyoyin sadarwa, wasu sun tako kafa da kafa su kira su ce wai abubuwan da muka yi a baya me yasa yanzu ba ma yi, to shi ne na ja hankali cewa kowanne abu ya na zuwa ne da nasa matsalar, wancan lokacin matsalar ta faru ne lokacin zaman gida sanadiyyar cutar Coronation.."

Batista Muhuyi ya kara da cewa wancan yanayi ya haifar da tashin farashin kayan abinci, wanda hakan ta sanya Hukumar ta yi aikinta har Allah ya sa farashin kayan ya sauka

Yace nan ba da jimawa ba Jami'an hukumar zasu fara aikin kai sumame zuwa dukkanin wuraren da ake zargin an boye kayan domin kwace ta hanyar amfani da dokar da ta kafa hukumar

Don haka Muhuyi yayi amfani da taron wajen yin kira ga daukacin jama'ar Jahar Kano, su ci gaba da bawa Hukumar hadin kai kamar yadda suka yi a baya domin cimma burin da aka sanya a gaba

Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da 'yan kasuwa, su taimaka wajen rage wannan halin matsi da al'uma ke ciki inda ya Jaddada cewa ita ma hukumar za ta nata bangaren don shawo kan lamarin baki dayansa

Daga nan sai Barista Muhuyi ya yi fatan cewar wannan yunkuri na hukumar zai magance matsalar ba wai a Kano ba, har ma da sauran sassan kasar nan baki daya 




Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki