Yadda Dalar Amurka Ke Jefa ’Yan Nijeriya Cikin Kunci
Hauhawar farashin Dalar Amurka ya biyo bayan dokar da Shugaba Tinubu na barin Naira ta kwaci kanta a kasuwa.
A ranar Litinin ta makon jiya ce Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Remi Tinubu ta kai ziyara Jihar Kano domin kaddamar tsangayar karatun lauyanci na Jami’ar Maryam Abacha, wato MAUN.
A lokacin ziyayar ce Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ba wa Remi Tinubu sako ta sanar da mijinta cewa, al’ummar Nijeriyar na cikin halin kaka-nika-yi, saboda haka ya yi abin da ya dace.
Sai dai tun a farko, Uwagidan Shugaban Kasar ta yi kira ga mutanen Nijeriya da su kwantar da hankalinsu, inda ta tabbatar da cewa lallai akwai haske da nasara a gaba.
Idan ba a manta ba, tun a jawabin da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi lokacin rantsuwar karbar mulki, a ranar 29 ga watan Mayu ya bayyana cire tallafin man fetur, abin da ya haifar da karin kudin man nan take daga Naira 195 zuwa 540 a kan kowace lita daya.
Sannan hauhawar farashin Dalar Amurka ya biyo bayan dokar da Shugaba Tinubu na barin Naira ta kwaci kanta a kasuwa.
Tun wannan lokacin Dalar take da hauhawa, inda yanzu haka ta kai Naira 1,495 kusan Naira 1,500 ke nan a ranar Litinin da muke hada wannan rahoto.
Wadannan abubuwa biyun ne suka hadu, suka cakude, suka kusan sauya komai a kasar, inda farashin komai ya hauhawa.
Duk abin da ka taba, ko dai a ce ya tashi saboda da Dala ta tashi ko kuma a ce an cire tallafin mai.
Bayan tashin farashin Dalar kuma, Aminiya ta ruwaito a ranar Litinin cewa, farashin litar man fetur ya kai Naira 700 a wasu jihohin.
A zagayen kasuwanni da Aminiya ta gudanar, ta gano cewa, ana sayar da litar man fetur ne a tsakanin Naira 700 da Naira 690 a gidajen man ’yan kasuwa a Jihar Sakkwato.
Majiyarmu ta gano cewa, manyan ’yan kasuwa irin su AA Rano da Dan Marina suna sayar da man a Naira 675, yayin da NNPC ke siyarwa a kan Naira 620.
A Maidugurin Jihar Borno kuwa, maniyartamu ta gano ana sayar da litar man har a kan Naira 720.
Gidajen man NNPC da wakilin majiyarmu ya ziyarta a Maidugurn sun kwashe kusan mako daya ba su sayar da man ba, har zuwa ranar Litinin da muke hada wannan rahoton.
A Jihar Kano, wakilin majiyarmu ya gano ana sayar da lita a tsakanin Naira 620 zuwa 690. AA Rano da ke Sharada da wasu wuraren suna sayar da man ne a kan Naira 675 lokacin da Aminiya ta kai ziyara.
Majiyarmu ta ruwaito yadda matasa suka gudanar da zangazangar tsadar rayuwa a wasu jihohin Nijeriya, inda matasan suka tare wasu tituna dauke da kwalaye suna kiran Shugaban Kasa Tinubu ya tausaya musu.
Laifin mutanen kasar ne — CBN
A makon jiya ce Majalisar Dattawa ta gayyaci Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) domin ya bayyana a gabanta sakamakon halin da tattalin arzikin kasar ke ciki da kuma faduwar darajar Naira da yadda mutane suka shiga kunci.
Kwamitin majalisar karkashin jagorancin Sanata Adetokunbo Abiru ya gana ne da Gwamnan na CBN a daidai lokacin da farashin Dala ya kai Naira 1,520 a kasuwar bayan fage.
Da yake bayyana dalilin matsalar, Gwamnan Bankin ya bayyana cewa, ba daga CBN matsalar take ba, inda ya nuna cewa, yadda mutanen kasar ke neman Dalar da kuma yadda suke matukar kaunar kayayyakin kasashen waje ne silar shiga wannan yanayi.
A cewarsa, babu wani siddabarun da Bankin CBN zai yi wajen daidaita Nairar, sai dai idan ’yan Nijeriya sun sauya wajen rage neman Dalar da kuma rage amfani da kayayyakin kasashen waje.
Sai dai ya ce, a nasu bangaren suna aiki ba dare, ba rana wajen shawo kan lamarin, inda ya ce matakan da suke dauka sun fara haifar da ’ya’ya masu ido, domin a cewarsa, daga cikin nasarorin da suka samu, akwai samun karin kusan Dala biliyan 1 a tattalin arzikin kasar.
Yadda za a shawo kan lamarin — Masani
Domin jin dalilin da ya sa Dala, wadda kudin wata kasar ce amma take sanadiyar jefa ’yan Nijeriya cikin kunci, majiyarmu ta tuntubi Dokta Abdurrazak Ibrahim Fagge, malami a Tsangayar Tsimi da Tanadi ta Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano, wanda ya ce dora duk wani abu na tattalin arzikin kasar nan da aka yi a kan Dalar Amurka shi ne musabbabin abin da ke wahalar da ’yan Nijeriya.
A cewarsa, “Da farko bari mu fara duba alakar ’yan Nijeriya da Dala.
“Kusan za a iya cewa ta samo asali ne daga yadda kasar ta dogara da man fetur a matsayin babbar hanyar da ke samar wa kasar kudaden kasashen waje, wanda kuma kamar kimanin kaso 70 na kudin shiga kasar nan ana samun su ne ta hanyar man fetur.
“Haka kuma, kamar yadda shi man fetur ake yi masa farashi da Dala, haka su ma kudin ake same su da Dalar.
“Wannan ba karamar alaka ce ta kud-da-kud tsakanin ’yan Nijeriya da Dalar Amurka ba.
“Dalili na biyu kuma, Nijeriya mun kasance gwamnatinmu gwamnati ce mai cin basuka har ma da na rashin hankali, wanda kuma mafi yawan basukan da ake ci daga kasashen ketare, ana ciyo su ne da Dala.
“Shi ma wannan sai ya kara wata alaka tsakanin Nijeriya da Dalar.
“Sannan wadannan dalilai guda biyu sai suka janyo cewar, hatta kasafin kudinmu na kasa, idan muka tashi yi a kan yi wa Naira farashi ne da Dalar.
Misali, a wannan kasafin kudin Gwamnatin Tarayya da farko ta yi wa duk Dalar Amurka daya a matsayin Naira dari bakwai da hamsin.
“Daga baya Majalisar ta kara zuwa Naira dari takwas da hamsin. Wadannan dalilai su ne suke kusan kara alaka tsakanin ‘yan Nijeriya da kuma Dalar Amurka.”
A cewarsa, wannan alakar ita ta janyo Dalar Amurkan ke wahalar da ’yan Nijeriya, musamman saboda bukatar da ’yan Nijeriyar ke da ita na Dalar Amurka.
“Na farko akwai bukatar masana’antu, wadanda ke sayan wasu sinadarai da wasu kayayyakin hadi da injina da ake amfani da su a masana’antun, wanda suke sayan su da Dalar Amurka.
“Haka kuma dalilin cin bashi da muka yi da Dalar nan to dole ne muna biyan uwar bashi ga kuma kudin ruwa da aka ciyo duk ana yin wannan da Dalar Amurka.
“Saboda haka, akwai bukatar a nemo Dalar a zo a biya wannan bashi da kudin ruwa na bashi, wanda idan muka duba tsawon shekera 10 da ta gabata daga zangon farko na 2014 zuwa zangon karshe na 2023, Nijeriya ta kashe kimanin Dala biliyan sha uku wajen biyan kudin ruwan bashi da kuma biyan tsofaffin basukan da wa’adinsu ya cika.
Wannan ba karamar bukata ba ce saboda haka duk lokacin da ake bukatarsu yana taimakawa wajen daga farashin Dalar a kan kudinmu na gida wato Naira.
Haka kuma, saboda rikon sakainar kashi da gwamnati ke yi a harkar abin da ya shafi lafiya da harkar ilimi to ’yan Nijeriya na bukatar Dala domin su fita waje wajen kai ’ya’yansu makaranta da neman lafiya ga iyalansu, wanda shi ma ake yin sa da Dala.
“A baya-bayan nan ma abin da ya sa bukatar Dalar ta karu shi ne ta ajiye kudi a gida.
“Wannan ya samo asali ne daga rikon sakainar kashi da gwamnati ke yi wa kudin kasar, inda ta bar darajar Naira na ta faduwa a kasuwa, ita ma kuma da kanta gwamnatin tana karya Nairar.
“Wannan ya sa ’yan Nijeriya suka shiga shakku na ajiye Naira saboda gudun asara. Mutum zai ajiye Naira miliyan daya, amma idan aka yi kwanaki sai ya ga darajarta ba ta fi Naira dubu dari tara da wani abin ba.
“Wannan tsoron da aka sa wa ’yan Nijeriya da dama ba su iya ajiye kudinsu a Naira, sai su je su sayi Dalar Amurka ko kuma wasu kudaden kasashen waje.
“Wannan sai ya kara bukatar Dalar a wurin mutane. Su ma ma’aikatan gwamnatin da ’yan siyasa idan suka yi wata almundahanar kudi, ba za su kai banki ba, ba za kuma su dauko Naira niki-niki su kai gida su ajiye biliyoyi, saboda haka sai a sayi Dalar Amurka, sai kudin su dawo ’yan kadan, a sa a jaka, a kai gida, a ajiye.
“Wannan bukatar ce a yanzu ta saka ’yan Nijeriya a matsala kuma ta taimaka wajen faduwar darajar Nairar.
“Ita kanta Gwamnatin Nijeriya da a yanzu ta dauki cewa idan tana da bukata ta kudi, idan ta ga zuwa ciyo bashin bata lokaci ne, to kawai sai ta karya Naira kai tsaye sai ta sami kudi.
“Hatta kasafin kudi na bana da aka kai wa Majalisa saboda ’yan majalisar suna so su sanya nasu ayyukan a cikin kasafin kudin sai suka karya Nairar a wannan kasafin kudin, inda an sa ta a Naira dari bakwai da hamsin su kuma suka canza zuwa Naira dari takwas da saba’in da biyar, wanda wannan karyawar da suka yi, ya samar musu da gurbi na Naira tiriliyan daya da biliyan dari biyu, wanda su ma suka kawo nasu ayyukan suka zuba a cikin kasafin kudin.”
Har ila yau, Dokta Abdurrazak Ibrahim Fagge ya ce, maganar Gwamnan Babban Bankin Kasa Mista Cardoson cewa ba shi da wani siddabaru da zai yi wanda zai warware matsalar da muke fama da ita cikin kankanen lokaci kuskure ne.
“Hakan da ya yi ya fito da rashin kwarewarsa karara, domin akwai zargin ba shi da kwarewa a fannin tunda dama ba abin da ya karanta ke nan ba.
“Shi ya sa kullum muke kiraye-kiraye cewa, idan akwai matsala a kasa ko ta tattalin arzikin ko wacce ta shafi kudi kai tsaye, kamata ya yi a daidai wannan lokacin a kawo kwararre, a ba shi rikon Babban Bankin.
“Amma idan lokacin da babu wasu matsaloli ne kuma komai yana tafiya daidai za a iya kawo kowa ma. Za a iya ba shi kuma ka ga an samu tafiyar abubuwa daidai.
“Amma a yanzu ana bukatar wanda zai yi tunani ya kawo mafita. Dama ba cewa aka yi ka zo ka yi siddabaru, ka kawo mafita ba.
“A’a ka yi tunani, ka yi nazari na tattalin arziki da kuma hada-hadar kudi. Ka kuma samar wa da kasar mafita kamar yadda ake yi a duniya.
“Wannan shi ne abin da ya kamata a yi. Wannan ya nuna cewa, shi ba cikakken kwararre ba ne a wannan fanni.”
Shin Dala za ta sauko kuma farashin mai zai ragu?
Da majiyarmu ta tambaye shi ko akwai wata hanyar da za a mangace matsalar, sai ya ce, “A ka’ida mafita daga yanayin da ake ciki ita ce a hakura da ciyo basukan da suke yi domin shi ne babban sanadin jefa mu cikin wannan hali.
“Na biyu kuma dole ne a tashi tsaye a nema wa Naira kima yadda darajarta za ta dawo kamar yadda aka san ta.
“Wasu shekaru da suka gabata ana ganin Nairar ta fi Dalar Amurka daraja, tunda Dalar Amurka daya ba ta kai Naira daya ba.
“Dole ne a yanzu a tashi a fara sama wa Naira daraja da kima daidai gwargwadon yadda za a iya, ta yadda ba zai yi wa tattalin arzikin kasa ko masana’antunmu illa ba.
“Sannan kuma a samu jami’in da ake ganin zai iya samar da wannan tsari, a ba shi jagorancin gudanar da harkokin Babban Bankin Kasa domin a samu wannan gyaran.
“Haka kuma, yana da kyau kamar wata yarjejeniya da muka shiga tsakaninmu da kasar China tun a 2018 na yin amfani da kudin China idan ’yan kasuwarmu za su yi sayayya ya kasance Chinan za ta rika ba su kudin, idan suna bukata, suna bayar da kudi ga Babban Bankin Kasa, su samu wannan kudin, su saya, su tafi China, su siyo kayayyakin.
“Akwai bukatar a gudanar da tsarin bisa tsarin da aka tanada ba kamar yadda ake gudanar da shi a yanzu ba.
“Misali, a yanzu kudin Yuan biliyan tara da aka zuba tun a 2018 a Babban Bankin Kasa sun zuba ne a kan duk Yuan daya a matsayin Naira 64, amma yanzu abin ba haka yake ba, domin Babban Bankin Kasa yana sayar da Yuan a kan Naira dari da wani abu, wanda da an ci gaba da sayar da shi a kan Naira 64 kamar yadda aka sayar wa ’yan kasuwar da za su je China su sayi kayayyaki a baya, da watakila har yanzu kayayyakin da muke sayowa daga China farashinsu na 2021 da har yanzu yana nan bai sauya ba, to amma son zuciya ya sa shi kansa Babban Bankin Kasa ya sa yana kara farashin, wanda wannan ya janyo mana illoli masu yawa.
“To irin wannan tsarin da sai a shigo shi da manyan kasashen da muke kasuwanci da su, kamar su Amurka da su Rasha, kowace kasa za mu yi hulda da ita, mu yi kai tsaye da kudin kasar ba wai da Dalar Amurka ba.
“Wannan zai rage mana bukatar Dalar da muke da ita da kuma matsaloli da muke da su. Haka kuma zai taimaka wajen inganta Nairar da muke da ita,” inji shi.
A bangaren farashin man fetur kuwa, kamar yadda Dokta Fagge ya ce, farashinsa na kara hauhawa ne saboda yawancin jigilarsa da ake yi daga kasashen waje, wanda hakan ya sa shi ma yake da alaka da Dalar.
Amma a watan Agustan bara, Gwamnatin Tarayya ta ce tana sa ran matatun man fetur din kasar guda hudu za su koma aiki a karshen shekara bana, inda Minista a Ma’aikatar Man Fetur, Heineken Lokpobiri ya ce za a fara ne da matatar Fatakwal a watan Disamban bara.
Majiyarmu ta ruwaito cewa, an kunna wutar Matatar Man Fatakwal, wanda ke nuna dawowa aiki a matatar. Nijeriya ita ce ƙasar da ta fi haƙo man fetur a Afirka, amma kusan duk tataccen man fetur dinta tana shigo da shi ne daga ketare.
Idan dukkan matatun man Nijeriya za su dawo aiki, za su iya tace danyen mai ganga 4450,000 a kullum.
A daya bangaren kuma, majiyarmu ta ruwaito cewa, Matatar Man Dangote ce mafi girma a Afirka, wadda ita ma aka ce za ta taimaka wajen rage shigo da tataccen man daga kasashen ketare da kasar ke yi.
Ita ma Matatar Dangoten, idan ta fara aiki sosai, za ta iya tace ganga dubu 650 a kullum.
A wata tattaunawa da BBC ta yi da wani masani kan harkar man fetur, Dokta Ahmed Adamu, wanda ke aiki a Jami’ar NILE a Abuja ya ce, tashin farashin man Nijeriya ya ta’allaka ne da abu biyu: tashin farashin mai a kasuwannin duniya da kuma karyewar darajar Naira.
Ya ce, babban abin da ke tantance farashin man fetur shi ne ainihin farashin da ɗan kasuwa ya saro man, wanda da Dalar Amurka ake amfani.
A cewarsa, idan dan kasuwa ya saro man da Dalar Amurka, sai ya dawo Nijeriya kuma Dalar ta yi tashin gwauron zabo, dole ya kara farashin a Naira.
A cewarsa, sauran abubuwan da ake la’akari da su kafin tantance farashin litar mai su ne kudin jirgin ruwa da kudin fito da kuma kudin sufuri a cikin gida Nijeriya.
A game da ko za a iya samun sauki, sai ya ce, “zai iya sauka, domin kuwa abubuwan da suke sanya farashin man ya karu su ne kuma za su iya sanya shi ya ragu.
“Amma a bangaren farashin Dalar Amurka kuwa, wannan lamari ne da ya dogara ga tsaretsaren gwamnati.”
Da kyar muke daukar dawainiyar iyalanmu — Maza
Majiyarmu ta zanta da maza masu iyalai a kan yadda suke dawainiya da iyalansu, inda Malam Umar Alkasim, wanda ma’aikacin gwamnati ne ya shaida wa Aminiya cewa, albashinsa ba ya isar sa da iyalinsa, inda ya nemi gwamnatin da ta kawo wa kasar mafita.
“Albashina ba ya rike ni da ’ya’yana biyar da muke tare da su. A da, bayan ciyarwa da sauran bukatu har samu nake yi na adana wani abu daga cikin kudin albashina.
“Amma yanzu kasancewar komai ya ninka farashinsa a kasuwa, ga shi kuma ba kara albashin aka yi ba, kudin sam ba su isar mu, mu ci abinci ballantana mu yi wasu bukatu.”
Shi ma wani mai wankin mota a kan titin Gidan Zoo a Kano mai suna Salisu Shuaibu ya bayyana cewa, duba da yanayin da ake ciki ba ya samun wankin motar sosai kamar da yake yi, ballantana ya samu abin da zai kai wa iyali.
“Yanzu sai in wuni ban samu wanki mota uku ba. Ba kamar a baya ba da nake wanke mota kusan 10 a rana.
“To mutane suna cikin wani yanayin na neman abin da za su ci shi ne a gabansu ba batun wankin mota ba.
Shi ma wani dan kasuwa mai suna Abbas Muhammad (Bale) ya bayyana cewa, rayuwar al’ummar tana cikin halin ni-’yasu, “Mu yanzu da muke kasuwancin sayar da motoci, muna fuskantar matsala.
“Ya kasance a yau mai jarin Naira miliyan goma da yake sayan motoci 5 saboda tsadar rayuwa a yanzu mutum ba zai iya sayan mota uku ko hudu ba.
“Baya ga wannan kuma ga kudin hanya da ake biya wa kowace mota bayan an biya mata kudin kwastam.”
Mun gani a tukunyarmu — Matan aure
Majiyarmu ta zanta da wasu matan aure a kan irin sauyin da suke gani wajen cefane.
Wata mata mai suna Hauwa Abdullahi mai shekara 25, wadda take da yara tara ta ce, idan sun samu abincin dare, to babu na rana, idan kuma an samu na rana, na daren sai ya yi wahala, inda ta kara da cewa, suna kwana babu abinci.
Malama Hauwa cikin kuka ta kara da cewa, tana da jarirai ’yan biyu, wadanda a cewarta idan suna kuka kuma ba ta da abin da za ta ba su, sai dai ita ma ta fara kuka saboda takaici.
Ita kuwa Amina Muhammed wadda take da yara biyar ta ce, mijinta ya fi shekara goma yana kwance ba shi da lafiya.
Ta ce, haka ake kwana idan ba a samu ba, sannan yara su yi ta kuka har barci ya dauke su.
Ita kuwa Adama Dahiru wadda take da yara shida ta ce, lallaba rayuwar ake, inda ta ce suna dai cin abin da ya samu ne kawai.
Malama A’isha Musa mai yara takwas ta ce, sukan yi kwana biyu ba su daura sanwa ba, inda ta ce mijinta mai aikin leburanci ne, idan an samu, su ci, idan ba a samu ba, sai su hakura.
Komawa ga Allah ita ce mafita — Sarkin Musulmi
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya tunatar da ’yan Nijeriya cewa, hanya mafi dacewa domin samun sauki daga wahalhalun da ake fama da su a kasar ita ce komawa ga Allah da addu’a.
Sarkin Musulmi ya jaddada muhimmancin shugabanni su yi adalci, sannan ya bayyana cewa, wahalhalun da ake fama da su a kasar a halin yanzu sun samo asali ne daga kaucewar mutane daga tafarkin Allah, domin haka dole a koma ga Allah domin Shi ke da mafita.
Ya ci gaba da cewa, “Kowa ya san halin da Nijeriya ke ciki a halin yanzu, amma mafita ita ce mu koma, mu nemi dauki daga Allah, amma da addu’o’i na gaskiya ba don riya ba, domin Allah Ya ce, duk tsanani na tare da sauki.”
Sarkin yi a ci gaba da cewa, wahalhalun da ake fama da su a kasar a yanzu sun samo asali ne daga kaucewar mutane daga tafarkin Allah.
“Duk wanda ya bar yin da’a ga Allah to tabbas Allah Zai rabu da al’amarinsa, hakan ya tabbata a wurare da dama a cikin Alkur’ani Mai Girma,” in ji shi.
Sarkin Muslumi ya yi wannan kiran ne a Abuja ranar Juma’a a yayin taron bude Masallacin Juma’a, wanda hedikwatar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa’kamatis Sunnah (JIBWIS) ta gina.
Wakilin Sarkin Musulmi a bikin kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Alhaji Yayale Ahmed ya taya shugaban JIBWIS murnar samun nasarar kammala aikin masallacin da yin alkawarin ci gaba da bayar da gudunmawa domin ganin an kammala cibiyar addinin Musulunci da ke wurin.
“Dole ne mu tuna da muhimmancin shugabanci da hadin-kai da kyautata zaman tare tsakanin Musulmi da kuma tsakaninsu da Kiristoci a irin halin da kasar nan ke ciki,” in ji shi.
(AMINIYA)