Search This Blog

Wednesday, 20 May 2026

Gwamnat Jihar Kano Ta Sanar da Hutun Babbar Sallar Ga Dukkan Makarantun Gwamnati da Masu Zaman Kansu


Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta sanar da hutun Sallar Idin Kabir ga dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar, Musbahu Aminu Yakasai ya fitar, an umarci dukkan makarantun kwana da su tafi hutun Sallah daga ranar Asabar, 23 ga Mayu, 2026, sannan su koma makaranta ranar Lahadi, 31 ga Mayu, 2026.

Haka kuma, makarantun jeka-ka-dawo za su fara hutun Sallah daga ranar Juma’a, 22 ga Mayu, 2026, sannan su koma makaranta ranar Litinin, 1 ga Yuni, 2026.

An shawarci iyaye da masu kula da daliban makarantun kwana da su je su karɓi ’ya’yansu a ranar rufe makaranta da aka amince da ita, wato Asabar, 23 ga Mayu, 2026, tare da tabbatar da dawo da su a kan lokaci ranar komawa makaranta.

Kwamishinan Ilimi, Gwani Dakta Ali Haruna Abubakar Makoda, ya yi fatan alheri ga dalibai, malamai, iyaye da daukacin al’ummar bangaren ilimi, tare da yi musu fatan gudanar da bukukuwan Sallar Idin Kabir cikin zaman lafiya da annashuwa.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Muhuyi’s 60 Days: Kano Intensifies the Fight Against Drug Abuse

Sixty days into his leadership of the newly established Kano State Multi-Agency Task Force on Drug Abuse and Illicit Trafficking...