NAHCON Ta Yi Jimamin Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ƙarƙashin jagorancina, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ta bi sahun sauran al’ummar Najeriya wajen jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Wannan rashin ya zo ne a daidai lokacin da ƙasa ke cikin alhini na rashin wani fitaccen attajiri kuma mai jinƙai, Alhaji Aminu Dantata.
Wannan al’amari wani tunatarwa ne gare mu duka kan cewa kowa yana da lokacin tafiyarsa, kuma yana ƙara bayyana wa matasa bukatar shiryawa don karɓar ragamar shugabanci na gaba da gina rayuwa bisa gaskiya, amana, hangen nesa da kyakkyawar manufa ga makomar Najeriya.
Dukkan su biyu, kowannensu da irin nasa salo, sun kasance tamkar madubin darussa da matasa za su duba su dauki darasi domin gina ingantacciyar ƙasa. Tsohon Shugaban Ƙasa Buhari ya shahara wajen tsantsar gaskiya, rikon amana da ladabi – wanda ya sanya ya zama abin ƙauna da koyi ga talakawa da dama.
Haka kuma, Alhaji Aminu Dantata ya shahara da hikimar kasuwanci da arziki wanda ya ke amfani da su wajen tallafawa ayyukan jinƙai da ci gaban al’umma. Ya gada kasuwanci daga mahaifinsa kuma ya gina bisa wannan harsashi, har ya bunƙasa sha’anin kasuwancin iyalansu da bayar da gudunmawa wajen ci gaban tattalin arziki da zamantakewar Najeriya.
Za a ci gaba da tuna da su bisa wasu manyan abubuwan alheri da suka aikata waɗanda ba za a iya ƙididdigewa ba da kuma gudunmawar da suka bayar wajen gina ƙasar nan.
Rasuwarsu a lokaci guda babban rashi ne ga ƙasa, amma kuma wani darasi ne ga matasan da ke tasowa a yau wajen tabbatar da ƙimomin da ke kawo haɗin kai, zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa.
Allah ya gafarta musu, ya sanya su cikin Aljannatul Firdaus, ya ƙarfafa danginsu da daukacin al’ummar Najeriya a wannan lokaci na jimami.