Search This Blog
Monday, 20 February 2023
APC Ta Bukaci Buhari Ya Mutunta Umarnin Kotun Koli Kan Wa’adin Tsofaffin Kudi
Welcome to Alheekmah News Alheekmah News is a Nigerian digital news platform committed to delivering timely, accurate, and credible news to readers across Nigeria and beyond. We provide comprehensive coverage of national affairs, politics, governance, Hajj and Umrah, religion, education, business, security, health, and other issues that shape our society. Our mission is to inform, educate, and inspire through responsible journalism founded on accuracy, fairness, and integrity. We strive to provide factual reporting while promoting public awareness and constructive engagement. At Alheekmah News, we believe that reliable information empowers individuals and strengthens communities. We are dedicated to bringing you breaking news, in-depth reports, exclusive interviews, and insightful analysis you can trust. Stay informed. Stay connected. Stay ahead with Alheekmah News.
Friday, 17 February 2023
Yadda CBN Ya Lashe Amansa Kan Karbar Tsoffin N500 Da N1,000
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya jefa ’yan Najeriya cikin rudani bayan ya fitar da sanarwa masu cin karo da juna kan ci gaba a karbar tsoffin takardun N500 da N1,000 cikin dan kankanin lokaci.
CBN ya lashe amansa ne bayan manyan bankunan kasuwanci irinsu UBA da First Bank sun tura wa abokan huldarsu sakonni cewa za su ci gaba da karbar tsoffin takardun N500 da N1,000.
Bankunan sun yi haka ne bayan wata sanarwar da kakakin CBN, Osita Nwanisobi, da ke umartar su da karbar kudin matukar ba su wuce N500,000 ba.
Sakonsa ga bankunan ya ce,
“Kwastoma zai iya kai har N500,000 bankin kasuwanci, amma abin da ya haura hakan sai dai ya kai ofishin CBN.
“Don haka ana bukatar ku bi wannan umarnin,” in ji wasikar farko da babban bankin ya aike wa manajojin reshe da ayyukan bankunan kasuwancin.
Bayan fitowar wasikar, ’yan jarida sun tuntubi Mista Nwanisobi, game da ita, wanda ya tabbatar musu da sahihancinta.
“Duk wanda ke da tsoffin takardun kudin da suka haura N500,000 ya kai ofishin CBN mafi kusa
“Muna kuma sanar da ku cewa za mu bude rassanmu gobe Asabar 18 ga Fabrairu, 2023.”
Shi ma bankin UBA ya tura irin wannan sako ga kwastomominsa kamar haka: “Ba mu daina amsar tsoffin takardun N500 da N1,000 ba, matukar ba su haura N500,000 ba.
Bankunan sun tura sakonnin ne a ranar Juma’a.
Amma kafin a jima, bayan kafofin watsa labarai su wallafa labarin, sai CBN ya fitar da wata sabuwar sanarwa, yana karyata umarninsa na farko da ya baiwa bankuna su ci gaba da karbar tsofaffin N500 da N1000.
A sabuwar sanarwar, kakakin na CBN ya zargi kafofin watsa labarai da yada labarin karya — wato sanarwarsa ta farko wadda shi da kansa ya tabbatar musu da sahihancinta.
“ To a sani cewa, kamar yadda Shugaban Kasa ya ba da umarni, tsoffin takardun kudi da za a ci gaba da amfani da su, su ne N200 na tsawon kwana 60 zuwa ranar 10 ga watan Afrilu.”
A kan haka ne First Bank ya goge sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Wannan dambarwar ta zo ne washegarin jawabin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, inda ya ba da umarnin a ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira 200 tare da sabbin takardun Naira 200, 500 da kuma 1,000 har zuwa 10 ga watan Afrilu, ranar da tsohuwar 200 za ta daina aiki.
Buhari ya sanar da haka ne a jawabinsa ga ’yan Najeriya da ke ci gaba da surutu kan sauyin takardun kudin da CBN ya yi, da kuma karancin sabbin da ya jefa su cikin damuwa.
Hannu guda kuma gwamnatocin was jihohi sun maka Gwamnatin Tarayya a Kotun Koli suna neman ta soke dokar haramta amfani da tsoffin kudin.
Batun karancin sabbin takardun kudin dai ya jefa ’yan Najeriya cikin kunci, har da asarar rayuka.
A wasu jihohin Kudu abin ya kai ga tarzoma da kona bankuna.
AMINIYA
Welcome to Alheekmah News Alheekmah News is a Nigerian digital news platform committed to delivering timely, accurate, and credible news to readers across Nigeria and beyond. We provide comprehensive coverage of national affairs, politics, governance, Hajj and Umrah, religion, education, business, security, health, and other issues that shape our society. Our mission is to inform, educate, and inspire through responsible journalism founded on accuracy, fairness, and integrity. We strive to provide factual reporting while promoting public awareness and constructive engagement. At Alheekmah News, we believe that reliable information empowers individuals and strengthens communities. We are dedicated to bringing you breaking news, in-depth reports, exclusive interviews, and insightful analysis you can trust. Stay informed. Stay connected. Stay ahead with Alheekmah News.
Babban bankin Najeriya (CBN) ya musanta rahotannin da ake ta yadawa cewa ya ba bankunan ajiya izinin karbar tsoffin takardun kudi na N500 da N1,000.
Welcome to Alheekmah News Alheekmah News is a Nigerian digital news platform committed to delivering timely, accurate, and credible news to readers across Nigeria and beyond. We provide comprehensive coverage of national affairs, politics, governance, Hajj and Umrah, religion, education, business, security, health, and other issues that shape our society. Our mission is to inform, educate, and inspire through responsible journalism founded on accuracy, fairness, and integrity. We strive to provide factual reporting while promoting public awareness and constructive engagement. At Alheekmah News, we believe that reliable information empowers individuals and strengthens communities. We are dedicated to bringing you breaking news, in-depth reports, exclusive interviews, and insightful analysis you can trust. Stay informed. Stay connected. Stay ahead with Alheekmah News.
LABARI DA DUMI-DUMI: Emiefele ya umurci bankunan da su karbi tsofaffin takardun kudi na N500, N1,000
Welcome to Alheekmah News Alheekmah News is a Nigerian digital news platform committed to delivering timely, accurate, and credible news to readers across Nigeria and beyond. We provide comprehensive coverage of national affairs, politics, governance, Hajj and Umrah, religion, education, business, security, health, and other issues that shape our society. Our mission is to inform, educate, and inspire through responsible journalism founded on accuracy, fairness, and integrity. We strive to provide factual reporting while promoting public awareness and constructive engagement. At Alheekmah News, we believe that reliable information empowers individuals and strengthens communities. We are dedicated to bringing you breaking news, in-depth reports, exclusive interviews, and insightful analysis you can trust. Stay informed. Stay connected. Stay ahead with Alheekmah News.
Thursday, 16 February 2023
Buhari Ya Ce A Ci Gaba Da Amfani Da Tsoffin Takardun N200
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarni a ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira 200.
Buhari ya ba da umarnin a ci gaba da amfani da tsoffin N200 ne ga Babban Bankin Najeriya (CBN) a yayin jawabinsa ga ‘yan Najeriya a safiyar Alhamis.
Ya kara wa’adin amfani da tsoffin takardun N200 ne da kwana 60 zuwa ranar 20 ga watan Afrilu, 2023.
Hakan na zuwa ne washegarin da Kotun Koli ta dage sauraron karar da wasu gwamnatocin jihohi suka shigar na kalubalantar dokar haramta amfani da tsoffin N1,000 da N500 da kuna N200 da CBN ta canja.
Welcome to Alheekmah News Alheekmah News is a Nigerian digital news platform committed to delivering timely, accurate, and credible news to readers across Nigeria and beyond. We provide comprehensive coverage of national affairs, politics, governance, Hajj and Umrah, religion, education, business, security, health, and other issues that shape our society. Our mission is to inform, educate, and inspire through responsible journalism founded on accuracy, fairness, and integrity. We strive to provide factual reporting while promoting public awareness and constructive engagement. At Alheekmah News, we believe that reliable information empowers individuals and strengthens communities. We are dedicated to bringing you breaking news, in-depth reports, exclusive interviews, and insightful analysis you can trust. Stay informed. Stay connected. Stay ahead with Alheekmah News.
Wednesday, 15 February 2023
Yanzu-Yanzu! Buhari Ya Gana Da Bola Tinubu A Fadar Shugaban Kasa
Welcome to Alheekmah News Alheekmah News is a Nigerian digital news platform committed to delivering timely, accurate, and credible news to readers across Nigeria and beyond. We provide comprehensive coverage of national affairs, politics, governance, Hajj and Umrah, religion, education, business, security, health, and other issues that shape our society. Our mission is to inform, educate, and inspire through responsible journalism founded on accuracy, fairness, and integrity. We strive to provide factual reporting while promoting public awareness and constructive engagement. At Alheekmah News, we believe that reliable information empowers individuals and strengthens communities. We are dedicated to bringing you breaking news, in-depth reports, exclusive interviews, and insightful analysis you can trust. Stay informed. Stay connected. Stay ahead with Alheekmah News.
DA DUMI-DUMI: Sake fasalin Naira: Kotun Koli ta Dage Sauraron karar da Kaduna, Kogi da Zamfara suka shigar
Kotun kolin Najeriya ta dage ci gaba da shari’ar kan manufar musanya naira na babban bankin Najeriya CBN zuwa ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu domin sauraron kararrakin da jihohi 10 suka hada.
Kotun
kolin da ta saurari karar a ranar Larabar da ta gabata ta cika makil da wasu
manyan lauyoyi da sauran gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi, Nasir El-Rufai da
Yahaya Bello, bi da bi.
A
zaman da ya gabata, Kotun ta dakatar da aiwatar da wa'adin ranar 10 ga watan
Fabrairu na CBN daga yin kwangilar tsohuwar takardar kudi ta N200, N500 da
N1,000.
Jihohin
Zamfara da Kogi da kuma Kaduna ne suka shigar da karar gwamnatin tarayya da
kuma babban bankin kasa CBN.
Sauran
jihohin da suka hada da Neja, Kano, Ondo, Ekiti, su ma sun nemi a shigar da su
gaban CBN da gwamnatin tarayya.
An
fara zaman kotun inda mai shari’a John Okoro ya jagoranci kwamitin mutum
bakwai.
Ya
ce bai kamata kotu ta yi watsi da shari’ar da kuma manufarta ba domin ya shafi
’yan Najeriya da ke addabar jama’a.
Jihar
Legas, ta hannun babban mai shari’a, Moyosore Onigbanjo, ita ma ta nemi a
shigar da ita kara.
Jihar
Bayelsa, karkashin jagorancin Damian Dodo, ita ma ta nemi a shigar da ita kara
a matsayin wanda ake kara. Hakazalika, Jihar Edo ta nemi a shigar da ita a
matsayin wanda ake kara.
Welcome to Alheekmah News Alheekmah News is a Nigerian digital news platform committed to delivering timely, accurate, and credible news to readers across Nigeria and beyond. We provide comprehensive coverage of national affairs, politics, governance, Hajj and Umrah, religion, education, business, security, health, and other issues that shape our society. Our mission is to inform, educate, and inspire through responsible journalism founded on accuracy, fairness, and integrity. We strive to provide factual reporting while promoting public awareness and constructive engagement. At Alheekmah News, we believe that reliable information empowers individuals and strengthens communities. We are dedicated to bringing you breaking news, in-depth reports, exclusive interviews, and insightful analysis you can trust. Stay informed. Stay connected. Stay ahead with Alheekmah News.
Tuesday, 14 February 2023
Wa'adin Dena Karbar Tsofaffin Kudi Ya Cika - CBN
Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya jadadda cewar ranar 10 ga watan Fabrairu ne wa’adin amfani tsofaffin takardun Naira ya cika.
Emefiele ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da jami’an diflomasiyya a Ma’aikatar Harkokin Waje da ke Abuja a ranar Talata.
“Lamarin ya lafa sosai tun bayan lokacin da aka fara biyan kudi a kan kanta wanda hakan ya rage dogayen layuka a ATM.
“Don haka babu bukatar la’akari da wani sauyi daga wa’adin ranar 10 ga Fabrairu,” in ji shi.
‘Yan Najeriya sun shiga rudani yayin da bankunan kasuwanci suka daina karbar tsoffin takardun tun daga ranar Litinin.
Da yake karin haske, Emefiele ya ce, “Wasu daga cikin shugabanninmu suna siyan sabbin takardun kudi suna ajiyewa saboda wata manufa saboda haka ba zan iya yin karin haske kan hakan ba.”
Emefiele ya ce babban bankin ya san irin wahalhalun da ‘yan Najeriya ke sha sakamakon canjin kudin, amma ya ce tsarin zai iya kawar da kashi 4 cikin 100 na hauhawar farashin kayayyaki.
Ya kuma yi bayanin cewa kamata ya yi a ce adadin kudin da ke zagawa a hannun al’umma ya kai kusan Naira biliyan 700.
Ana iya tuna cewa, a bayan nan ne dai gwamnatocin jihohin Kaduna, Zamfara da Kogi suka maka CBN da Gwamnatin Tarayya a gaban Kotun Koli suna kalubalantar sabon tsarin amfani da sabbin takardun kudi.
AMINIYA
Welcome to Alheekmah News Alheekmah News is a Nigerian digital news platform committed to delivering timely, accurate, and credible news to readers across Nigeria and beyond. We provide comprehensive coverage of national affairs, politics, governance, Hajj and Umrah, religion, education, business, security, health, and other issues that shape our society. Our mission is to inform, educate, and inspire through responsible journalism founded on accuracy, fairness, and integrity. We strive to provide factual reporting while promoting public awareness and constructive engagement. At Alheekmah News, we believe that reliable information empowers individuals and strengthens communities. We are dedicated to bringing you breaking news, in-depth reports, exclusive interviews, and insightful analysis you can trust. Stay informed. Stay connected. Stay ahead with Alheekmah News.
Monday, 13 February 2023
Kotun 'Ma'aikata Ta Umarci Ganduje Da Ya Amince Da Muhuyi A Matsayin Shugaban Hukumar Karbar Korafi Ta Kano
A ranar Litinin din da ta gabata ne Kotun ma’aikata ta kasa da ke zamanta a Kano, ta umarci gwamnatin jihar Kano da ta ci gaba da kasancewa a kan “status quo ante bellum” a karar da korarren shugaban hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Kano PCAC, Muhuyi Magaji Rimingado ya shigar, har sai an ci gaba da sauraron karar.
Status quo ante bellum yana nufin halin da ake ciki kamar yadda
ya kasance kafin jayayya.
An shigar da karar gwamnatin jihar Kano da majalisar dokokin
jihar da kuma babban lauyan jihar Kano a matsayin wadanda ake tuhuma na 1 da na
2 da na 3.
gaban mai shari’a E.D. Esele,
Mista Rimingado yana kalubalantar
sahihancin matakin da gwamnati ta dauka na korar shi ba tare da bin ka'ida ba.
A bisa wannan umarnin, wasikar korar da aka
mika wa Mista Rimingado ba ta da wani tasiri kuma hukuncin da kotun masana’antu
ta kasa, Abuja ta yanke a baya yana nan daram sai dai idan kotu ta yanke hukunci bayan yanke hukunci.
A ranar 14 ga Disamba, 2022, kotun ma’aikata ta kasa ta ayyana Mista Rimingado a matsayin shugaban hukumar, sannan ta kuma umarci Ganduje ya biya shi bashin albashin N5,791, 891.22.
Sai dai a wata takardar sallamar mai dauke da kwanan watan 24 ga watan Janairu mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Usman Alhaji, gwamnatin jihar ta kori Mista Rimingado a matsayin shugaban hukumar, saboda kudirin majalisar dokokin jihar a ranar 26 ga watan Yuli.
DAILY NIGERIAN
Welcome to Alheekmah News Alheekmah News is a Nigerian digital news platform committed to delivering timely, accurate, and credible news to readers across Nigeria and beyond. We provide comprehensive coverage of national affairs, politics, governance, Hajj and Umrah, religion, education, business, security, health, and other issues that shape our society. Our mission is to inform, educate, and inspire through responsible journalism founded on accuracy, fairness, and integrity. We strive to provide factual reporting while promoting public awareness and constructive engagement. At Alheekmah News, we believe that reliable information empowers individuals and strengthens communities. We are dedicated to bringing you breaking news, in-depth reports, exclusive interviews, and insightful analysis you can trust. Stay informed. Stay connected. Stay ahead with Alheekmah News.
Duk wanda ya kwarmata masu É“oye sabbin kuÉ—aÉ—e zai samu tukuici – EFCC

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa
Head of Service Urges Civil Servants to Uphold Ethical Conduct
The Head of Service, Kano State, has called on civil servants to strictly adhere to the Civil Service ethical code and show grea...
-
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya ce Bankuna za su ci gaba da karbar tsoffin takardun kudi na Naira ko da baya...
-
Matar hamshakin dan kasuwa na Kano, Alhaji Aminu Alasan Dantata, Hajiya Rabi ta rasu Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa, Hajiya ...
-
Zababben Gwamnan Jihar Kano Ya Sanar Da Kwamitin Karbar Mulki …… Dr. Baffa Bichi, Abdullahi Musa ya nada a matsayin Shugaba da Sakatare Baya...