Gwamna Yusuf ya yabawa Tinubu da Shettima bisa rashin yin katsalandan a hukuncin Kotun Koli

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a matsayin jajirtattun jagororin da suka bijirewa gagarumin matsin lamba na yin tasiri ga hukuncin kotun koli kan zaben gwamna.

A sanarwar da Darakta Janar kan kafafen yada labarai da sadarwa na Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, yace Gwamna Yusuf ya bayyana jin dadinsa da yadda Tinubu da Shettima suka jajirce wajen fuskantar matsin lamba na yin katsalandan ga hukuncin kotun kolin, duk kuwa da kakkausar murya daga bangarori daban-daban.

Dangane da yunkurin da ake zargin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje na yin amfani da fadar shugaban kasa wajen murde hukuncin da kotun koli ta yanke na goyon bayan dan takarar sa na gwamna a jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, Gwamnan ya bayyana rashin tsoma bakin da Tinubu da Shettima suka yi a matsayin wata shaida da ke nuna cewa Najeriya na da kyakkyawan tsarin dimokwaradiyya.

Bugu da kari, Yusuf ya mika goron gayyata ga abokin takararsa, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, dan takarar gwamna na jam'iyyar APC da ya sha kaye a kotun koli, inda ya jaddada bukatar a mayar da hankali wajen gina Kano a yanzu da aka kammala takarar siyasa.

Ya bukaci daidaikun mutane daga kowane bangare na siyasa da su hada kai da gwamnatinsa domin ciyar da Kano gaba.

“A matsayina na mai bin tafarkin dimokaradiyya na gaskiya kuma mai son ci gaba, ina kira ga ‘yan adawa na da magoya bayansu da su ba ni hadin kai wajen ci gaban jihar mu ta Kano domin ci gaban al’ummarta,” in ji Gwamna Yusuf.

Ya kuma yabawa al’ummar Kano bisa goyon bayan da suka bayar da kuma juriyar da suka nuna, da kuma Alkalan Kotun Koli bisa yadda suke tabbatar da gaskiya a bangaren shari’a.

Bugu da kari, ya mika godiyarsa ga Allah da ya ba shi goyon baya.

Gwamnan ya kuma nuna jin dadinsa ga shugabannin NNPP a dukkan matakai, musamman yadda Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya ya yi masa jagora da goyon bayansa a lokacin da ake fuskantar kalubale.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki