Ayyukan Da Zan Yi Wa Al'umar Mazabata Cikin Shekarar 2024 - Abdulmumin Jibrin Kofa
Bayan rantsar da ni a matsayin ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji, na yi hoɓɓasar ganin na kawo ayyukan raya ƙasa da ci gaban yankina. Kamar yadda buƙatun ainihin aikin da aka zaɓe ni don shi suke, na duƙufa ba dare ba rana wajen yin bincike domin gabatar da ƙudurorin da zan gabatar a zauren majalisa a ’yan watanni masu zuwa, waɗanda za su amfani ’yan mazaɓata da ma ƙasa baki ɗaya.
A sakamakon haka, na tattauna da shugabannin kwamitoci daban-daban a Majalisa, na kuma rubuta wasiƙun neman ayyuka masu yawa da za aiwatar a mazaɓata a 2024, ƙari a kan wasu da zan yi da aljuhuna, kamar yadda na saba yi a baya. Yana da muhimmanci a fahimci cewa idan ban da aikin tituna (waɗanda na saka a kasafin kudin 2016, amma ba a aiwatar da su ba), na kawo ayyukan raya kasa masu tarin yawa a mazaɓata, na samar da gurabun ayyukan yi ga mutanen mazaɓata a hukumomi da ma’aikatun gwamnati masu yawa da kuma wasu hukumomin tsaro, duk waɗannan za a iya zuwa a tantance su.
Duka waɗannan ayyukan na nan a cikin wani kundin littafi Mai suna “Seeing is believing” (Gani ya kori ji) da ke ɗauke da hotuna da wuraren da aka yi su, wanda muka wallafa a 2017, kuma ya ƙunshi ayyukanmu da dama daga 2011-2015 kawai. Sai dai littafin bai ƙunshi ɗaruruwan ayyukan alherin da tallafin da muka bayar na gwamnati da na ƙashin kanmu ba daga 2016 zuwa yau. Amma nan ba da jimawa ba za mu sabunta shi domin ya ƙunshi abubuwan da muka yi daga baya, domin ya zama hujja kuma ya zama kyakkyawan tarihi ga ’yan baya.
Kamar yadda kuka sani, wannan ne karo na huɗu da nake lashe zaɓen kujerar ɗan Majalisar Wakilai, amma gaba ɗaya shekaru kamar shida kawai na yi cikin 12 da ya kamata na yi a kan kujerar saboda dalilan da kowa ya riga ya san su. Na yi shekaru huɗu a majalisa daga 2011-2015, sai shekara ɗaya da rabi daga 2015-2019, sai wata shida daga 2019-2023, daga 2023 zuwa yau kuma na yi wani wata shidan a kai.
Ina so na gode muku saboda yadda kuka amince da ni da kuma halaccin da kuka nuna min na zaɓe na har sau huɗu. Ina mai ba ku tabbacin cewa sai na ba mara ɗa kunya wajen kawo ayyukan alheri ga mazaɓarmu da kuma kayar da sanaaoi, bayar da jari da tallafi ga ’yan mazaɓarmu Insha Allah.
AYYUKAN DA SHIRYE-SHIRYEN DA ZA MU AIWATAR A 2024 TA HANYAR TALLAFIN GWAMNATI
1- Samar da fitilun kan titi masu amfani da hasken rana a yankunan Kiru/Bebeji
2- Ginawa da kuma gyara azuzuwan makaranta a yankunan Kiru/Bebeji
3- Ginawa da kuma gyara wasu hanyoyi a yankunan Kiru/Bebeji
4- Gyarawa da ɗaga likafa da kuma samar da kayan aiki a wasu asibitoci da cibiyoyin lafiya a yankunan Kiru/Bebeji
5- Samarwa tare da saka na’urorin rarraba hasken lantarki a yankunan
Kiru/Bebeji
6- Samar da cibiyoyin koyar da fasahar sadarwa a Kiru/Bebeji
7- Samar da cibiyar zana jarabawa a Kiru/Bebeji
8- Samar da wasu gine-gine a Makarantar Kiwon Lafiya da ke Bebeji
9- Raba tallafin kayan karatu ga ɗaliban firamare da na sakandare a Kiru/Bebeji
10- Samar tallafin karatu na Gwamnatin Tarayya ga ɗaliban Kiru/Bebeji
11- Raba tallafin jari ga mata da matasa a yankunan Kiru/Bebeji
12- Bayar da tallafin rage raɗaɗi ga masu buƙata ta musamman a Kiru/Bebeji
13- Bayar da horo, koyar da sana’o’i da raba jarin fara sana’a ga ’yan kasuwar Kiru/Bebeji
14- Ɗaukar mata da matasan Kiru/Bebeji ayyuka a hukumomin tsaro da gwamnati a hukumomi da ma’aikatun gwamnati
15- Samar da kananan famfunan ban-ruwa ga manoman rani na Kiru/Bebeji
AYYUKA DA SHIRYE-SHIRYEN DA ZAN AIWATAR DAGA ALJIHUNA
1- Ginawa da kuma gyara wasu masallatai a yankunan Kiru/Bebeji
2- Gyara fadojin wasu masu riƙe da sarauntun gargajiya a Kiru/Bebeji
3- Ginawa da kuma yin kwaskwarima ga wasu ofisoshin jami’an tsaro da kuma samar musu da kayan aiki a yankunan Kiru/Bebeji domin inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
4- Gina cibiyar koyar da na’ura mai ƙwaƙwalwa da kuma ta koyar da sana’o’i a Kiru/Bebeji
5- Samar da kayayyakin koyon sana’o’i
6- Samar da jari da tallafin kuɗi ga masu kananan sana’o’i a Kiru/Bebeji
7- Bayar da tallafin kayayyakin da masu juna-biyu ke buƙata da kuma kuɗi ga mata masu juna-biyu
8- Zuwa ziyarar duba marasa lafiya
9- Bayar da tallafin ƙaro karatu da tallafin kuɗi ga dalibai.
10- Ci gaba da bayar da tallafin kuɗi domin rage raɗaɗi ga mutanen Kiru/Bebeji
11- Bayar da tallafin kayan karatu ga ɗaliban firamare da sakandare na Kiru/Bebeji
Muna yi muku fatan alheri da kuma Barka da shiga sabuwar shekarar Miladiyya
Hon Abdulmumin Jibrin Kofa PhD
(Jarman Bebeji)
1-1-2024