Dokar Najeriya Ta Haramta Biyan Kuɗin Fansa — Ministan Tsaro

 


Ministan Tsaro Mohammed Badaru Abubakar ya ce Dokar Najeriya ta haramta biyan masu garkuwa da mutane kuɗin fansa.

Ministan wanda ya bayyana haka ne a taron Majalisar Zartarwa da aka gudanar a wannan Larabar, ya ce lokaci ya yi da za a daina biyan kuɗin fansar saboda haka ne kaɗai hanyar kawo ƙarshen masu garkuwa da mutane.

Ya ce Shugaban Kasa ya bai wa dukkan hafsoshin tsaro goyon bayan da ya kamata don ganin an kawo karshen garkuwa da mutane da ya yi ƙamari a ƙasar.

Tsohon Gwamnan na Jihar Jigawa, ya ce kasancewar dokar Najeriya ta haramta bayar da kuɗin fansa ya sanya bai kamata mutane su riƙa biyan kuɗin ba saboda ba shi da amfani.

“Babbar matsalar ita ce yadda mutane ke fitowa a kafafen yaɗa labarai suna neman taimako, har a zo a tara musu kuɗi domin biyan fansa. Hakan bai dace ba.

“Idan muka daina biyan kuɗin fansa, sannu a hankali ayyukan masu garkuwa da mutane zai zama tarihi,” in ji Badaru.

Dangane da yadda rashin tsaro ke ƙara ta’azzara a Abuja, babban birnin ƙasar da kuma garkuwa da mutane da ake yi a yankunan gefen birnin, Ministan ya ce ayyukan da ake yi na korar ’yan bindiga a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya shi ya sa suke ta ƙaura da guje-guje.

“Shugaban ƙasa ya ba mu umarni tare da duka hafsoshin tsaro, ya kuma ce lallai a je a tsayar da wannan abu da ke faruwa. Kuma mun sa ƙaimi don ganin mun kawo ƙarshensu,” in ji Badaru.

Ya ce ana ci gaba da fatattakar ’yan bindigar a jihohin Zamfara da Borno don ganin an daƙile ayyukansu.

A makon jiya ne tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Isa Pantami, ya samo wanda zai biya miliyan 50 daga Naira miliyan 100 na kudin fansar sauran ’yan mata ’yan gida daya da ’yan bindiga suka sace a Abuja.

Aminiya ta ruwaito yadda a daren Talatar makon jiya ’yan bindiga suka sace wani magidanci da ’ya’yansa mata shida a Karamar Hukumar Bwari ta Babban Birnin Tarayya.

Daga bisani suka sako shi sannan suka nemi ya biya Naira miliyan 60 zuwa ranar Juma’a kafin su sako ’ya’yan nasa.

Zuwa ranar Juma’ar Naira miliyan 30 iyalan suka iya tarawa, amma ’yan ta’addan suka ki amincewa, lamarin da ya sanya suka kashe babbar ’yarsa, Nabeeha, wadda ke ajin karshe a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Daga nan suka kara kudin fansa zuwa miliyan 100, tare da barazanar kashe sauran ’yan uwanta idan har ba a biya ba.

A kan haka ne tsohon minista Isa Pantami ya bayyana cewa ya tattauna da “aboki kuma dan uwa” wanda zai biya Naira miliyan 50 daga kudin fansar ragowar ’yan matan.

Ya rubuta cewa, “Duk da cewa ba na goyon bayan biyan kudin fansa ga ’yan bindiga, amma ya zama dole, tunda ta tabbata jiya mun rasa ’yarmu Nabeeha, kuma ana barazanar kashe sauran ’yan uwanta biyar, kamar yadda mahaifinsu ya shaida min.

“Na yi magana da da wani abokina kuma dan uwa wanda ya ce zai biya Naira miliyan 50 …. duk wanda ke da hali zai iya karawa domin mahaifin ya samu abin biya ya ceto rayuwar ’ya’yan namu.”

Ya kuma yi addu’ar zaman lafiya a kasar, ya kuma jajanta wa iyalan dalibar da aka kashe tare da yi addu’ar Allaha Ya saka wa wadanda suka rasu, Ya sanya su a  Aljanna.

(AMINIYA)

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki