Posts

Showing posts from 2023

Hajj 2024 : Hukumar Alhazai Ta Bauchi Ta Siyar Da Kujerun Haji Guda 1700- Imam Abdurrahman

Image
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi ta sayar da kimanin guraban kujerun aikin hajji akalla *1700* daga cikin guda *3364* da Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta ware wa Jihar Bauchi. A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Muhammad Sani Yunusa ya sanyawa hannu, yace Sakataren zartarwa na hukumar jindadin alhazan ta jihar Bauchi Imam Abdurrahman Ibrahim Idris,shi ne bayyana hakan yayin  zantawarsa da manema labarai kan shirye shiryen aikin hajji daga Bauchi, inda yace wayarda alumma kan sabbin tsare tsaren aikin hajjin na shekarar 2024 daya gudana a jihar Bauchi yayi tasiri kwarai da gaske. Imam Abdurrahman ya alakanta nasarar gudanar da atisayen wayarda kan alummar ne da irin gudumawa da goyon bayan da tsarin ya samu daga sarakunan mu na jihar Bauchi da shugabannin kananan hukumomi da limamai da sauran masu ruwa da tsaki a aikin Hajji. Ya kara da cewa sabbin tsare-tsare na Saudiyya kan ayyukan Hajji na shekarar 2024 ne suka tilastawa kasashe fara  ...

Shugaban Majalisar Dokoki Ta Katsina Ya Raba Tallafin Naira Miliyan 35

Image
Kakakin Majalissar Dokoki ta Jihar Katsina, Nasir Yahaya, ya bayar da tallafin Naira Million Talatin da HuÉ—u da Dubu ÆŠari Tara da Hamsin. (34,950,000) ga Mutum Dubu Ukku (3000) a filin wasan Ƙwallon Kafa dake Daura Hadimin tsohon Shugaban Najeriya, Buhari Sallau, ya rawaito a shafinsa na Facebook cewa, an bayar da Tallafin ga Marayu, Limamai, Zawarawa, Masu Ƙananan Sana'oi, Exco, Mata, Matasa, Students, yan Media, Dagattai, MabuÆ™ata, yan siyasa, Ƙungiyar Teloli, Ƙungiyar Masu Shayi da Masu chajin waya, da sauran su. Inda ko wanne daga cikinsu zai amfana da Tallafin, Naira Dubu Goma (10,000) Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda PhD, yayi Jin-Jina gami da fatan Alkhairi ga Kakakin Majalissar akan wannan abin Alkhairi da yayi, sannan yayi roÆ™o gami da Jan hankali ga wanda suka amfana da wannan Tallafin da suyi amfani dashi ta hanyar daya dace, domin su bunÆ™asa Kasuwar su.  Haka kuma Mataimakin Shugaban Jam'iyyar APC na Jihar, Alh. Bala Abu Musawa, ya taya mutanen D...

Shugaban NAHCON Ya Ziyarci Ofishin Jakadancin Saudiyya na Abuja.

Image
Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya wato NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi, ya kai ziyarar ban-girma zuwa ofishin Huldar Jakadanci na Saudiyya inda ya gana da Jakadan Saudiyya dake Abuja, Ambasada Faisal Ibrahim Al-Ghamidy, a ranar Laraba   A sanarwar da Hukumar ta fitar ta ce, Shugaban ya kai ziyarar ce da nufin bunkasa dangantaka da habakar da hadin-gwiwa tsakanin bangarorin biyu.   Malam Arabi ya jaddada jin dadinsa ganin yadda Jakadan Kasar Saudiyya Ambassada Faisal ke bada cikakken goyon-baya ga Hukumar da tareraya irinta Huldar Jakadanci karkashin  Ofishin Jakadancin Saudiyyar. Sanarwar tace ziyarar, ta bayyana karara yadda dadaddiyar alaqa ta jituwa ke tsakanin NAHCON da Ofishin Jakadancin Saudiyyar, abinda ke nuni da fahimtar-juna da hadin kai dake wanzuwa a tsakanin Kasashen biyu. A Yayin ganawar, bangarorin biyu  sun zanta batutuwa masu ma’anar gaske, abunda ke tabbatar da muhimmancin tarayyarsu wajen kara inganta gudanar da Al-amurran A...

Kotun Koli Ta Tsayar Da Ranar Da Za Ta Saurari Karar Zaben Gwamnan Kano

Image
Kotun koli ta sanya ranar Alhamis 21 ga watan Disamba domin cigaba da sauraron karar zaben gwamnan Kano tsakanin gwamna Abba Kabiru Yusuf na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP da Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC.  KANO FOCUS ta rawaito cewa a cikin sanarwar da magatakardar kotun daukaka kara ta aikewa lauyoyin bangarorin biyu, kotun za ta saurari karar da NNPP ta shigar da kararrakin wasu jam’iyyu.  Gwamna Yusuf na kalubalantar hukuncin da wasu bangarori uku na kotun daukaka kara suka yanke wanda ya soke nasarar da ya samu tare da tabbatar da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke. Kotun sauraron kararrakin zabe karkashin jagorancin mai shari’a Osedebay ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano a watan Maris.  Kotun daukaka kara ta yi watsi da karar da Gwamna Yusuf ya shigar bisa matsayinsa na zama mamba a jam’iyyarsa sannan ta zargi kotun da yin watsi da hujjar da ta yanke. Ko...

Kofa Ya Raba Tallafin Kudi Ga Mata Guda Dari Biyar A Mazabarsa

Image
A ci gaba da tagomashin arzikin da yake yi wa mutanen mazaÉ“arsa, Abdulmumin Jibrin Kofa, É—an Majalisar Wakilai na Kiru da Bebeji daga jihar Kano, a ranar Lahadi ya sake gwangwaje mata 500 da tallafin kuÉ—i. A sanarwar da h adimin É—an majalisar kan yaÉ—a labarai, Sani Ibrahim Paki  ya fitar, yace an  yi taron rabon tallafin ne a mahaifar É—an majalisar da ke Kofa a Ƙaramar Hukumar Bebeji, Kano, kuma wannan shi ne karo na bakwai da yake raba irin wannan tallafin a ’yan makonnin nan.  Idan za a iya tunawa, a baya É—an majalisar ya raba tallafin ga shugabannin al’umma, mata da matasa, É—alibai, ’yan social media, malamai da masu rike da sarautun gargajiya.  Wannan ne dai rabon tallafi karo na bakwai tun bayan farawa, kuma karo na biyu ga mata. Bugu da Æ™ari, É—an majalisar ya karÉ“i baÆ™uncin fitacciyar ’yar asalin Bebejin nan, kuma jigo a jam’iyyar NNPP, Hajiya Azumi Babeji, wacce ita ma ta halarci bikin sannan ta gabatar masa da takardar nadi...

Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Yi Ga NAHCON Da Ta Samar Canjin Dala Kan Farashin Gwamnati Ga Maniyyata

Image
Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa, ya bukaci Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta kara zage damtse wajen ganin an samu dala a farashin gwamnati  ga wadanda zasu halarci aikin hajjin bana. A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya bayyana hakan ne a wata ganawa da kungiyar Arewa New Agenda a wata ziyarar wayar da kai da hukumar alhazai ta kasa suka kai Kano, wanda aka gudanar  a ofishinsa. Ya kara da cewa karin kudin aikin Hajjin bana da kuma karancin lokacin biyan kudi na daga cikin matsalolin dake kawo tsaiko wajen biyan kudaden ajiya. Da yake mayar da jawabi kan wadannan matsalolin, shugaban tawagar kungiyar Arewa New Agenda daga Hukumar Alhazai ta kasa, Dakta Muhd Lawan Salisu, ya tabbatar wa darakta Janar din cewa, sun dukufa wajen hada kai da hukumomin da abin ya shafa, ciki har da Sarkin Musulmi, domin mika kokon bara ga...

Gwamnatin Kano Ta Tabbatar da Gano Illar Bata Tarbiyya Yara Mata A Shirin Tallafawa Ilimi Na AGILE

Image
Biyo bayan zarge-zargen bata tarbiyya da ake yiwa shirin tallafawa ilimin yaya mata na AGILE, ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta gudanar da taron karawa juna sani na yini biyu kan shirin. Premier Radio ta rawaito a shafinta na Facebook cewa, Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, wanda ya yi magana a yayin taron na masu ruwa da tsakin da ke nazarin horar da dabarun rayuwa a karkashin shirin, ya ce ma’aikatar ta fitar da wani sabon salo na abubuwan da shirin ya kunsa. Ya ce malamai sun yi korafin cewa a cikin shirin akwai wasu abubuwa da basu amince da su ba inda suka duba korafin nasu kuma suka gano matsalar dake cikin sa yayin da aka cire duk wani da ya saba da al’ada da koyarwar addnini muslunci. A nashi bangaren, co’odinetan shirin na AGILE a nan Kano, Alhaji Nasiru Abdullahi-Kwalli, ya ce ma

NAHCON Ta Dakatar Da Rabon Kujeru Ga Kanfanonin Jirgin Yawo

Image
Hukumar Aikin Hajji ta kasa (NAHCON) a dakatar da rabon kujeru aikin Hajjin 2024 ga kamfanonin jirgin yawo 40 da suka yi nasarar samun aikin jigilar maniyyata. NAHCON ta dakatar da rabon kujerun ne saboda korafe-korafen da zargin rashin adalci da wasu kamfanonin da ba su yi nasara ba ke yi. Mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta ce hukumar na sane da irin wadanna zarge-zarge daga wasu kamfanonin da ba su yi nasara a tantancewar da aka yi ba. Don haka aka dakatar da akai na tsawon awa 48 masu zuwa, domin daukar matakin da ya dace, tabbatar da tsafta a aikin da kuma kare martabar kukumar. (AMINIYA)

Na shiga matsananciyar damuwa da hare-haren 'yan bindiga a 'yan kwanakin nan - Gwamnan Zamfara

Image
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook Inda yace "A madadin gwamnatin Jihar Zamfara, ina miÆ™a saÆ™on ta'aziyya da jaje ga al'ummar Æ™aramar hukumar Zurmi, musamman iyalai da ‘yan uwan waÉ—anda suka rasa rayukansu a harin ta'addanci da 'yan bindiga suka kai garin"  Ina son tabbatarwa da al'umma cewa gwamnatina za ta bayar da tallafi da agajin gaggawa ga mutanen da abin ya shafa. Sannan ina mai tabbatar da cewa muna nan jajirce akan tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'ummar Zamfara baki É—aya. Ina sane da sadaukarwar da jami’an tsaro suke yi a Æ™oÆ™arin da suke na kare rayukan al’umma, gwamnatina za ta ba su duk wasu kayan aiki da kuma tallafin da suka dace domin yaÆ™ar ‘yan bindiga, ba za mu huta ba har sai Zamfara ta samu cikakken tsaro insha Allahu.   WaÉ—annan sabbin hare hare sun biyo bayan nasarar da jami'an tsaro suka samu ne, na kashe shugabannin 'yan ta'addan. Ciki har da nasarar ...

Shugaban Hukumar NAHCON Ya Karbi Rahoto Kan Masaukin Alhazai Tare Da Alkawarin Sake Inganta Ayyuka

Image
Mai rikon mukamin Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Malam Jalal Ahmed Arabi, OON, fwc, ya ce ba da fifiko tare da inganta jin dadin mahajjata da ayyukansu shi ne babban aikin da Hukumar za ta gudanar a lokacin aikin Hajjin shekarar 2024. A sanarwar da Mataimakin daraktan yada yada labarai da dab'i na hukumar, Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, yace Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar rahoton kwamitin duba sharuÉ—É—an masauki da ciyarwa yau a dakin taro na hukumar Ya ce samar da ingantacciyar hidima aiki ne mai matukar muhimmanci da hukumar za ta bi domin cika aikinta tare da dorewar amana da amincewar jama’a da kuma alhazai. A cewarsa, gabatar da rahoton da shawarwari a cikinsa “zai taimaka matuka wajen farfado da kwarin gwiwa da amincewar mutane da alhazai musamman a gare mu. “Ina so in gode muku bisa sadaukarwar da kuka yi. Wannan rahoto da shawarwarin ba shakka za su ba da gudummawa don haÉ“aka hanyoyin ci gaba da aiwatar da abu...

Labari Da Dumiduminsa: 'Yan Majlisar Jahar Rivers 27 Masu Biyayya Ga Wike Sun Bar PDP Zuwa Jam'iyyar APC

Image
Akalla ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas 27 cikin 32 ne suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC, sakamakon rikicin da ya barke tsakanin gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara da ministan babban birnin tarayya (FCT). Nyesom Wike ya zurfafa. Wani dan majalisar, Enemi George, ya tabbatar wa gidan talabijin na Channels cewa ‘yan majalisar 27 na karkashin jagorancin Martin Amaewhule ne. 'Yan majalisar sun yanke Wannan hukuncin ne a yayin zamansu na safiyar ranar Litinin (DailyNews24)

Gwamnan Katsina Ya Ceto Wanda Yan Ta'adda Suka Sace

Image
Gwamnan Katsina, Dikko Raddah, ya jagoranci fatattar ’yan bidiga a kauyen Zakka a Karamar Hukumar Safana ta jihar. Gwamnan ya jagornaci jami’an tsaro hadin gwiwa wajen ceto wani matashi da ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi. Dikko Radda ya jagoranci kai daukin ne a lokacin da ya je karamar hukumar kaddamar da shirin tallafi na mataimakin shugaban majalisar jihar, Abduljalal Runka. Sakataren yada labaran gwamna, Kaula Mohammed, ya ce kafin kaddamar da tallafin ne jami’an tsaro suka samu kiran gagawa cewa ’yan ta’adda sun kai hari kauyen Zakka. Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito Kaula na cewa, nan take gwamnan ya dakatar da shirin, shige gaba aka fattaki ’yan bindigar, aka ceto matashin. Daga nan gwamnan ya ba da umarnin kai mutumin asibiti domin kula da shi, saboda harbin sa da aka yi a kafa.

Sanatoci Sun Sallama Albashinsu Na Disamba Ga Mutanen Tudun Biri

Image
Sanatocin Najeriya gaba dayansu sun sadaukar da albashinsu na watan Disamba ga mutanen da harin bom da jirgin soji ya samu a wurin taron Mauludi a Jihar Kaduna. Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya sanar cewa sanatocin su 109 sun amince a ba da albashin nasu a matsayin gudunmuwar ga mutanen Tudun Biri. Sanata Barau wanda ya yi bayani a yayin ziyararsu fadar gwamnatin Kaduna domin jajanta wa Gwamna Uba Sani kan tsautsayi, ya bayyana cewa albasjin ya kama Naira miliyan 109. Ya ce hakika sun yi bakin ciki bisa tsautsayin da ya auka wa al’ummar garin na Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi, kuma majalisar ta sha alwashin yin bincike domin gano musabbabin abin da ya faru. Gwamna Uba Sani a jawabinsa ya mika godidyarsa ga dukkan ’yan majalisar da suka jajanta masa, inda ya bukaci su tabbatar da Hakimin Yan Tudun Biri ya fito kunya ta hanyar yi musu adalci. Ya kumu nuna rashin jin dadinsa bisa yadda wasu ke neman sanya rigar addini ko kabilanci a kan ab...

Hajj 2014 : Hukumar NAHCON Ta Kafa Kwamitin Bitar Ka'idojin Samar Da Abinci Da Gidaje.

Image
Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta kaddamar da wani kwamiti da zai yi nazari kan wasu sharuddan da suka shafi masauki da abinci don samar da ingantacciyar hidima a lokacin aikin Hajjin 2024. A sanarwar da Mataimakin daraktan yada labarai da dab'i na Hukumar Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, yace da yake jawabi a wurin taron, mai rikon Shugabancin Hukumar,  Malam Jalal Ahmad Arabi OON, fwc, ya bayyana cewa sake duba ka’idojin da ake da su za su taimaka wajen inganta ayyukan masu ba da hidima wanda hakan zai amfanar da Alhazan Najeriya. A cewarsa, kundin tsarin gudanarwar kwamitin ba sabon sabon abu ba ne, amma wata hanya ce kawai ta yin la'akari da tsarin da ake da shi don samar da kyakkyawan sakamako. “Abin da muke yi yanzu ba wai sabon abu  ba ne kawai don inganta yadda muke yin abubuwa. Kamar yadda yake faruwa a wasu sassa na duniya, muna bukatar mu kasance da Æ™wazo. Kamar yadda al'ada ce ta duniya, dole ne mu inganta ta hanyoyinmu, don dacewa da mafi kyaw...

Yanzu-Yanzu: Ganduje ya sake nada Aminu Hikima sabon mukami a matakin kasa

Image
A cikin sanarwar da Aminu Dahiru Ahmed ya fitar a shafinsa na Facebook, ya ce, wannan  shi ne karo na hudu da Baba Ganduje ya nada ni. A lokacinsa na farko a matsayin gwamnan jihar Kano, ya nada ni babban mai taimaka masa na musammam kan harkokin daukar hoto. Haka kuma a wa’adinsa na biyu ya sake nada ni a Wannan matsayi.   Lokacin da ya bar ofis bayan shekaru takwas, ya nada ni mai daukar hotonsa na kashin kai. Nadin na baya-bayan nan shi ne na hudu.   Aminu Dahiru yace Baba Ganduje ya yi min abin da uba kawai zai yi wa dansa. Ya dauki nauyin karatuna da sauran abubuwa da yawa. "Wacce irin ni'imomin Ubangijinku kuke karyatawa"? A matsayina na mai daukar hotonsa, ina da abubuwa da yawa da zan ce game da Baba Ganduje. Mai daukar hoto yana aiki tare da maigidansa. Ni ma na yi aiki tare da Baba Ganduje tsawon wadannan shekaru. Ina shaidawa tsohon gwamnan yana da riko da addini, mai tausasawa, mai kirki, mai yarda da mutuntawa har da wadanda ke karkashinsa. Kasanc...

Yanzu-Yanzu: Zulum ya amince da nadin Mohammed Dawule a matsayin mai rikon Hukumar Alhazai ta Jahar Borno

Image
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da nadin Mohammed Dawule Maino a matsayin mukaddashin sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jihar Borno. An bayyana nadin ne a ranar Lahadin da ta gabata a wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Borno, Hon. Bukar Tijjani. Sakataren gwamnatin jihar ya kara da cewa nadin wanda ya fara aiki nan take, ya dogara ne akan cancanta da kuma bayanan shekarun baya a aikin gwamnati. Har zuwa lokacin da Dawule ya nada shi mamba ne a sabuwar Hukumar Ilimi ta Larabci da Sangaya ta Jihar Borno (BOSASEB. Kafin nan, Dawule ya yi aiki a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Borno tsakanin 2015 zuwa 2022. Ya kuma yi aiki a Makarantar Sakandare ta islamiyya da ke Maiduguri da Kwalejin Gwamnati da ke Maiduguri da kuma Makarantar Alkur’ani ta Model da ke Konduga. An haifi Mista Dawule mai shekaru 50 a duniya a karamar hukumar Kaga da ke arewacin jihar Borno. Gwamna Zulum ya taya Mohammed Dawule Maino murna sannan ya ce yana fatan ci gaba da yi masa hid...

Hajj2024: NAHCON Ta Ja Hankalin Hukumar Kula Da Filayen Jiragen Kan Samar Da Kayayyakin Da Suka Wajaba

Image
Hukumar Alhazai ta kasa ta hori hukumar dake lura da filayen jiragen sama ta kasa, da ta gaggauta samar da dukkanin kayayyakin da suka waja a bangare tashin alhazai da nufin gudanar da jigilar alhazan na wannan shekarar cikin nasara A sanarwar da mataimakin Daraktan yada labarai da dab’I na hukumar , Mousa UIbandawaki ya sanyawa hannu, yace Mai rikon mukamin shugabancin hukumar, Malam Jalal Ahmed Arabi, shi ne yayi wannan kiran lokacin da wakilin hukumar na bangaren aikin Haji suka kai masa ziyarar ban girma a Abuja Ya bayyana cewa samar da kayayyakin da suka wajaba a bangaren tashin alhazan dake fadin kasar nan zai taimaka matuka gaya wajen samun nasarar aikin jigilar alhazan ‘’Ku manyan abokan hula ne wajen gudanar da aikin Haji. Koda yake akwai wasu abubuwa da ake la’akari dasu yayin tashin alhazai kuma muna sa ran zaku sanar mana yanayin da filiyen jiragen saman da ake amfani dasu waje n tashin alhazai suke ciki’’ Ya bayyana cewa kwamitin ya kamata yay duba da lokaci d...

Bayan Shekara Uku, an sake bude Kasuwar Bacci a Kaduna

Image
Bayan shafe tsawon shekara uku ana gyaran Kasuwar Barci da ke Tudun Wada a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, gwamnatin jihar ta sake bude kasuwar. Ana iya tuna cewa, tsohon gwamnan jihar, Nasiru El-Rufa’i ne ya rushe kasuwar domin zamanantar da ita. Sai dai wannan yunÆ™uri ya fuskanci kalubale, inda ‘yan kasuwar da dama da suka rasa shaguna da jari ke korafin kudin hayar shago da suka ce ya gagare su. Kan haka ne Shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Kabiru Yakubu Jarimi, ya shawarci tsofaffin ’yan kasuwar da su nemi ba’asin shagunansu. Shugaban wanda ya samu wakilcin Sakataren karamar hukumar, Abdulrahman Yahaya, ya shawarci ‘yan kasuwar da su yi watsi da shawarwarin masu hana su komawa kasuwar. Ya ce dole ne su koma su nemi hakkin shagunansu tun da sun kasance suna da shaguna a baya a cikin kasuwar. Aminiya

Abin Da Ya Kawo Cikas A Sulhun ECOWAS Da Sojin Nijar — Yusuf Tuggar

Image
Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, ya ce sun yi tayin tattaunawa domin kawo Æ™arshen tankiyar da ke tsakanin Ƙungiyar Raya Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) da sojojin da suka kifar da Shugaban Nijar Mohammed Bazoum, amma hakan bai yiwu ba, don kuwa shugabannin sojojin sun Æ™i amincewa da yunÆ™urin. Ambasada Tuggar ya faÉ—i hakan ne a wata hirarsa da BBC, yana mai cewa duk wata magana da ta shafi a saki Shugaba Bazoum, sojin ba su amince da ita ba. ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 2 a Imo Abdul Amart ya siya wa iyalan Aminu S. Bono gida “Sun ce kar ma a yi wannan maganar, kar ma a sa shi cikin sharuÉ—É—an yin sulhu,” in ji Yusuf Tuggar. Ya bayyana cewa babu ta yadda za a iya samun sulhu a wannan yanayi. “Za su ci gaba da rike shi kenan ya yi zaman dindindin a kulle?” Ministan ya ce sojojin da suka yi juyin mulki ne suka janyo wa Nijar takunkumin da ECOWAS ta Æ™aÆ™aba mata, da kuma shiga halin da take ciki. Ya ce abin da suke buÆ™ata shi ne a saki Shugaba Bazou...

Kofa ya shirya taron addu'a na musammam ga Tinubu, Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf

Image
...Ya ce har yanzu Æ™ofar NNPP a buÉ—e take don yin Æ™awance da APC da sauran jam’iyyu Abdulmumin Jibrin Kofa, É—an Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaÉ“ar Kiru da Bebeji, Kano, a yau ya tara malamai 1,000 a garinsa na Kofa a Bebeji, Kano, domin addu’a ta musamman ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da kasar baki daya, Jagoran jam’iyyar NNPP da ÆŠarikar Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, PhD, FNSE da kuma neman nasara ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a Kotun Ƙoli, da kuma addu’ar neman taimakon Allah ga É—an majalisar.  A sanarwar da hadimin dan majalisar kan harkokin yada yada labarai, Sani Ibrahim Paki ya sanyawa hannu, yace yayin taron, malaman sun sauke AlÆ™ur’ani sau 1,101, sannan suka yi addu’o’i na musamman. A taÆ™aitaccen jawabin da ya gabatar a wajen taron, Hon. Jibrin ya ce alaÆ™arsa da Shugaba Tinubu ba É“oyayya ba ce. Ya kuma ce Kwankwaso ne maigidanshi, sannan zai ci gaba da iya Æ™oÆ™arinsa wajen ganin an samu kyakkyawar alaÆ™a a tsakanin Tinubun da Kwankwaso. ...

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada Abdullahi Musa matsayin shugaban ma'aikata

Image
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Alhaji Abdullahi Musa a matsayin sabon shugaban ma'aikatan gwamnati. A sanarwar da babban sakataren yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, yace nadin ya biyo bayan murabus din da tsohon shugaban ma’aikata, Alhaji Usman Bala Mni ya yi na radin kansa wanda gwamnatin yanzu ta rike tun daga kafuwarta a watan Mayu, 2023. Kwararren ma’aikacin gwamnati wanda ya yi aiki a ma’aikatu da ma’aikatu da hukumomi daban-daban a Kano sama da shekaru talatin, sabon shugaban ma’aikata ya fito ne daga karamar hukumar Kiru. Abdullahi Musa ya rike mukamin babban sakatare na gidan gwamnatin Kano, daraktan harkokin kansiloli, Admin da Janar aiyuka na ofishin majalisar ministoci, ma’aikatar ayyuka na musamman, da kuma Servicom Directorate. Ya kammala karatunsa na Digiri a fannin Dangantaka tsakanin kasa da kasa daga babbar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya kuma ta samu digirin digirgir a fannin manufofin ...

Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Bukaci Jami’anta Na Kananan hukumomi Da Su Gaggauta Siyar Da Kujerun Aikin Hajji

Image
Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa, ya jaddada bukatar daukar matakin gaggawa na jami’an Hukumar alhazai na kananan hukumomi domin ganin an siyar da kujerun aikin Hajji a kan lokaci. A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Darakta Janar din yayi jawabin ga mahalarta taron a ranar Alhamis a taron bita na yini daya da hukumar ta shirya a sansanin ‘yan yawon bude ido na jiha, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya bukaci jami’an su kara zage damtse wajen siyar da dukkanin kujerun aikin Hajji da aka ware daga kananan hukumomi daban-daban. Da yake karin haske game da lamarin, ya jaddada wajabcin karbar kudaden ajiya 4.500,000 daga maniyyatan da suka nufa a karshen wata mai zuwa, musamman nan da ranar 25 ga Disamba, 2023. Bugu da kari, Alhaji Laminu Danbappa ya bayyana muhimman bayanai, inda ya bayyana cewa Saudiyya na shirin kammala bayar da bizar kwana 5...

NAHCON Ta Kaddamar Da Kwamitin Da Dai Zai Sake Duba Ayyukan Kwamitin Tawagar Likitoci Masu Kula Da Lafiyar Alhazai

Image
Hukumar alhazai ta kasa NAHCON a kokarinta na inganta gaskiya da kuma sake fasalin ayyukan tawagar likitoci masu kula da lafiyar alhazai ta kasa ta kaddamar da wani kwamiti mai mambobi 15 domin duba yadda tawagar zata gudanar da aikin Hajjin 2024. ; A sanarwar da Mataimakin daraktan yada yada labarai na hukumar, Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, yace da yake jawabi yayin taron da aka gudanar a dakin taro na hukumar, Mai rikon Shugabancin Hukumar, Malam Jalal Ahmad Arabi, OON, fwc ya ce wasu daga cikin hanyoyin da tsarin sun zama na zamani da kuma wadanda ba su da tushe. “Tawagar Likitoci ta kasa na da matukar muhimmanci wajen gudanar da ayyukan Hajji. Yana da matukar tayar da hankali cewa wasu daga cikin tsarinsa da tsarinsa suna buÆ™atar yin la'akari da su, idan dole ne mu sami kyakkyawan sakamako. Muna buÆ™atar shigar da sabbin ra'ayoyi ta yadda ake aiwatar da ayyukanta yayin da wasu daga cikin tsarinsa da  suka zama tsofaffi" ; “Kamar yadda yake tare da duk Æ™...

Najeriya Za Ta Fara Fitar Da Tataccen Mai Kasar Waje A 2024 —NNPCL

Image
Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) Mele Kyari ya ce Najeriya za ta zama kasa mai fitar da tataccen man fetur da dangoginsa zuwa kasashen waje a shekarar 2024 mai kamawa. Mele Kyari ya kuma ba wa ’yan Najeriya tabbacin cewa cikin watanni uku masu zuwa ba za a samu karancin man fetur ba, kamar yadda ake gani a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara. “Ina tabbatar wa shugabannin majalisa ba za a fuskanci karancin mai ba. “Za ku ji ana ta yada labarin layuka a gidajen mai, amma ba gaskiya ba ne,” in ji Mele Kyari. Hukuncin da muka zartar na korar Gwamnan Kano na nan daram – Kotu Magoya bayan NNPP sun yi zanga-zanga kan hukuncin kotu a Kano Ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci shugabannin majalisar dattawa. Ya kara da cewa NNPC zai gyara matatar mai ta garin Fatakwal a wata mai kamawa, sannnan matatar mai ta Warri ta biyo baya a farkon 2024. Haka zalika, ya yi hasashen NNPCL zai samu ribar da ta kai triliyan biyu a shekarar 2023 da ke dab da karewa. Kyari ya shai...

Yanzu-Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Zaben Gwamna Abdullahi Sule Na Jahar Nassarawa

Image
Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da zaben gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule.  Kotun daukaka kara ta kuma yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Nasarawa ta yanke a ranar 2 ga watan Oktoba da ta kori Sule na jam’iyyar APC tare da bayyana David Ombugadu, dan takarar jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.  Da yake yanke hukunci, kwamitin mutum uku ya ce kotun ta yi kuskure wajen yanke hukuncin cewa Gwamna Sule bai samu rinjayen kuri’un da aka kada a zaben ba.  Cikakken labarin zai zo muku nan gaba 

Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Kano Ta Jaddada Bukatar Biyan Kudin Aikin Hajji A Kan Lokaci

Image
Daraktan janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano Alh Laminu Rabi’u Danbappa ya jaddada muhimmancin hada kai da Limamai Juma’a. Wannan hadin gwiwar na da nufin fadakar da alhazai kan wajibcin gaggauta biyan kudaden ajiya na Hajji don tabbatar da cimma manufofin da aka sanya a gaba.  A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace taron da aka gudanar yau a dakin taro na sansanin yawon bude ido na jiha Alh Laminu Rabi'u Danbappa ya bayyana kudirinsa na yin aiki kafada da kafada da limaman Juma'a na dukkan kananan hukumomin.  Hanyar haÉ—in kan za ta taimaka wajen isar da sako  ga mahajjata masu niyya, tare da buÆ™ace su da su cika  ajiyar kuÉ—in aikin Hajji cikin gaggawa.  Babban daraktan ya jaddada muhimmancin hadin kai da hadin kai wajen samun nasarar aikin Hajji ba tare da wata matsala ba.  Ya kuma bukaci limaman Juma’a da su kara himma tare da al’ummominsu domin yada muhimman ...

Sojoji Sun Kutsa Ofishin EFCC Dake Kuduna Domin Kubutar Da Abokan Aikinsu

Image
Hukumar da ke yaƙi da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa ta EFCC ta bayyana takaicinta kan yadda ta ce wasu jami'an sojin saman ƙasar suka kutsa ofishinta da ke Kaduna domin ƙwato 'yan uwansu da hukumar ta tare bisa zargin 'karya dokar aikin tsaro'. Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun jami'ain hulɗa da jama'a na hukumar, Dele Oyewale, ta ce a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba jami'an EFCC sun kama wasu mutum biyar da hukumar ke zargi da aikata laifukan da suka shafi zambar kuɗi ta intanet a unguwar Barnawa da ke birnin Kaduna Hukumar ta ce ta kama mutanen ne ba tare da wani tashin hankali ba, daga nan ne kuma wasu mutum shida - da suka haɗar da sojoji huɗu da ɗaliban cibiyar fasahar aikin sojin sama biyu - waɗanda ke wurin a lokaci da aka kama waɗanda ake zargin, suka yi wa ofishin EFCC da ke Kaduna ƙawanya da nufin tilasta sakin mutanen. ''Daga nan ne kuma aka kama su tare da tsare su a ofishin hukumar,...

Hukuncin Kotu: Sakon Dr Nasiru Yusuf Gawuna Ga Al'umar Kano

Image
Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki daya tabbatar da nasararmu a yau a kotun daukaka kara ta zaben gwamna. Ina so in gode wa kotun daukaka kara saboda hukuncin da ta yanke wanda ya tabbatar da nasarar da muka samu a kotun sauraron kararrakin zabe. Tabbatar da gaskiyar da kotun daukaka kara ta yi tabbas zai karfafa dimokradiyya. Ina so in yi amfani da damar in yaba wa alkalan kotunan zabe da na kotun daukaka kara da suka tsaya kan gaskiya don ganin an yi adalci. Dukkan hukunce-hukuncen biyu sun sake tabbatar da cewa bangaren shari'a shine fata na karshe na talaka. Wannan nasara ce ga daukacin al’ummar jihar nan da mazauna jihar, don haka ina neman goyon bayan kowa ba tare da la’akari da jam’iyya ba don mu hada kai da ni da abokina Alh.Murtala Sule Garo don ci gaban Kano. Dole ne in gode wa jagoranmu mai kaunarmu, Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Dr.Abdullahi Umar Ganduje, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sen. Barau Jibrin da Ministoci biyu daga Jihar Kano bisa...

Yanzu-yanzu: Gwamnan Kano Abba Kabir Zai Daukaka Kara Zuwa Kotun Koli

Image
...... Ya Bayyana Hukuncin Daukaka, Rashin Adalci Bayan nazari na tsanaki da masu ruwa da tsaki, gwamnan jihar Kano da  NNPP sun yanke shawarar tunkarar kotun koli kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke jiya a Abuja. A sanarwar da babban sakataren yada yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, yace Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a daren Juma’a a wani jawabi na musamman da aka yi wa mutanen Kano a matsayin martani ga hukuncin kotun daukaka kara da aka bayyana a matsayin rashin adalci. “Ina so in sanar da mutanen Kano nagari kuma hakika ‘yan Najeriya cewa bisa ga amincewar masu ruwa da tsakinmu, mun umurci lauyoyin mu da su fara daukaka karar wannan hukunci a kotun kolin Najeriya, muna da kwarin gwiwar cewa babbar kotun koli ta Najeriya. Kotu da yardar Allah SWT za ta kawar da wadannan kura-kurai na shari’a da kotunan daukaka kara da kotunan daukaka kara ke yi, sannan ta sake tabbatar mana da aikin da mutanen jihar Kano nagari suka ba m...

Labari da dumiduminsa: Kungiyar Kwadago ta janye yajin aikin da ta fara gudanarwa

Image
Kungiyar Kwadagon ta kasa ta Janye yajin aikin ne bayan zaman tattaunawar da mai bawa Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu Cikakken labarin zai zo muku nan gaba 

Kotu Ta Dage Shari'ar Rarara Kan Sukar Buhari

Image
Wata Kotun Majistiri da ke zamanta a Lafiya, babban birnin Jihar Nassarawa, ta dage sauraron kara da aka shigar da mawakin siyasa, Dauda Kahutu wanda aka fi sani da Rarara, kan zarginsa da neman tunzura al’umma da kuma tayar da hankali. Karar wanda wani mazaunin garin Mararraba da ke makotaka da Abuja mai suna Muhammad Sani Zangina ya shigar, ya danganta shi ne da wani jawabin taron ’yan jarida da ya ce mawakin ya shirya a Abuja, inda ya bayyana nadamar goyon bayansa ga tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, tare da zarginsa da wargaza kasar kafin mika ta ga Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu. An sa zare tsakanin Rarara da mutanen Buhari Sabuwar wakar Rarara ta sake yamutsa hazo A takardar karar wadda wakilinmu ya samu gani, lauyan mai shigar da karar, Barista Muhammad Barde Abdullahi ya gabatar, ya ce zargin da ake yi wa Rararan da aikatawa, ya saba da doka ta 114 a Kundin Shari’a na penal code. Sai dai a yayin zaman fara sauraron shari’ar a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba,...

Kungiyar Kwadago Za Ta Fara Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani Daga Gobe Talata

Image
Kungiyar Kwadago ta Najeriya da kungiyar ‘yan kasuwa ta Najeriya sun umurci mambobin kungiyar da su shiga yajin aikin gama gari daga tsakar daren ranar 14 ga Nuwamba, 2023. Shugaban kungiyar ta TUC, Festus Osifo ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Litinin. Osifo ya ce yajin aikin zai ci gaba da kasancewa har sai “gwamnati a dukkan matakai sun farga da alhakin da ya rataya a wuyansu.” Har ila yau yajin aikin na zanga-zangar ne don nuna rashin amincewa da yadda aka yi wa shugaban NLC, Joe Ajaero, da wasu shugabannin majalisar suka yi a Owerri, jihar Imo, a ranar 1 ga watan Nuwamba, da kuma matsalolin da ke addabar ma’aikata a jihar Imo. ‘Yan sanda sun kama Ajaero ne gabanin wata zanga-zangar da aka yi a jihar Imo, kamar yadda shugaban yada labarai na NLC, Benson Upah ya bayyana. Ko da yake rundunar ‘yan sandan ta musanta kama Ajaero, inda ta bayyana cewa an tsare shi ne kawai don kare kai harin, gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya zargi sh...

Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Shirya Taron Addu'a Kan Nasarar Kotu, Ya Kuma Tallafa Wa Mutum 10,000

Image
Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Bebeji da Kiru, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya shirya taro na musamman wanda ya haÉ—a sama da mutum 10,000 domin yin addu’o’i a garinsa na Kofa da ke Karamar Hukumar Bebeji ta Jihar Kano a ranar Lahadi  ÆŠan majalisar mai hawa huÉ—u ya shirya taron ne domin ya gode wa Allah saboda nasarar da ya samu a Kotun Sauraron Ƙararrakin ZaÉ“e da ta ÆŠaukaka Ƙara da ke Abuja a kwanakin baya, da kuma raba wasu kayan tallafi ga ’yan mazabarsa. A yayin kasaitaccen taron dai, an bayar da tallafi ga ’yan mazabar su 10,000 maza da mata. Bugu da Æ™ari, an ba mutanen tallafin kuÉ—i da kayan sanaa da motoci da kayan abinci da sutturu da kuma sauran kayan amfanin yau da kullum. Kazalika, an yi addu’a ta musamman ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, domin neman Allah Ya ba shi nasara a Kotun ÆŠaukaka Ƙara da ta Ƙoli, da sauran ’yan majalisar Kano na NNPP da suka yi nasara a kotu, da ma fatan nasara ga waÉ—anda ba a kai ga ya...