Babu hannunmu a tashin farashin kayan abinci -- Dangote

Babbar Darakta a rukunin kamfanonin Dangote, Hajiya Fatima Aliko Dangote, ta bayyana cewa rukunin kamfanonin Dangote ba su da hannu a tashin farashin kayayyakin abinci da ake fuskanta a kasar nan.

Daily Nigeria Hausa ta rawaito cewa wata hira da Sashen Hausa na BBC, Hajiya Fatima ta ce kamfanin ya sayar da bangaren sarrafa abinci shekaru biyar da suka gabata ga Olam Group da ke sarrafa abinci da kasuwancin noma a Najeriya.

Ta ce Olam a yanzu shi ne ke samar da fulawa, taliya, semolina, kuma duk wata fulawa da ake samu a kasuwanni ba kamfanin Dangote ne ke samar da ita ba.

“A cikin yarjejeniyar cinikin, an amince da cewa za su ci gaba da yin amfani da sunanmu da tambarin muwajen yin kayayyakinsu, kuma nan da shekara mai zuwa za su daina.

“Mu yanzu sukari, gishiri, da kayan yaji na Dangote kawai muke samarwa. Har ila yau, muna fatan za mu fara noman shinkafa nan gaba ko kuma badi,” in ji ta.

Fatima ta kara da cewa ba su ji dadin yadda farashin kayayyakin ke hawa ba kuma kamfanin ba zai iya maganin hakan ba, inda ta nuna fatan abubuwa za su daidaita nan ba da jimawa ba.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki