Mataimakin Shugaban Kasa Ya Kaddamar Da Sababbin Shugabannin NAHCON
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya kaddamar da sababbin Jami'an hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) tare da yin kira ga da su bullo da sabbin abubuwa a harkokin aikin hajji a Najeriya.
A sanarwar da mai taimakawa Mataimakin Shugaban kasar kan harkokin yada labarai Stanley Nkwocha ya sanyawa hannu, yace da yake jawabi yayin kaddamar da sababbin 'yan hukumar a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Laraba, mataimakin shugaban kasar ya bukaci mambobin su hada kai tare da kawo sabbin ra’ayoyi kan ayyukan hukumar. A cewar Sanata Shettima, yin aiki a hukumar NAHCON na da matukar muhimmanci ganin cewa “Hajji na daya daga cikin rukunan Musulunci guda biyar”. “A gare ku, bayan nadaku da aka yi, abu ne mai nasara domin idan kun yi wa alhazai hidima da kyau, Allah Ta’ala zai biya ku a ranar lahira. Don haka, aikinku ya fi kusanci da na addini fiye da aikin gudanarwa,” in ji Shettima.
Da yake karin haske game da batun kafa sabuwar hukumar da aikin da ke gabansu, Sanata Shettima ya ce, “Shugaban yana sane ya zabo mutanen da ke da al’adu daban-daban da kuma wadanda ba a taba gurbata su a baya ba domin su kawo sabbin dabaru da sabbin abubuwa a harkokin aikin Hajji a Najeriya da kuma yadda za a yi aikin Hajji a Najeriya. haka kuma a yi tambayoyi game da tsarin gudanarwa na hukumar tare da fitar da mafi kyawu daga ma'aikatan." “Kamar yadda aka saba, za ku fuskanci kalubale da dama amma ina rokon ku da ku hada karfi da karfe guda domin cimma nasarar da muke bukata.
Zan roke ku da kuyi tunani ku fito da ingantattun hanyoyin da za su gamsar da alhazan Najeriya. “Aiki ne mai wuyar gaske; wannan shi ne yanayin aikin hajji. Amma ina so ku kasance da shi a cikin zuciyarku cewa kuna bauta wa Allah da bil'adama," in ji shi. Mataimakin shugaban kasan ya bukaci sabbin jami’an da su inganta tsarin adashin gata mai dogon zango na aikin Hajji domin kara yawan maniyyatan da ke halartar ibadar ta shekara a fadin kasar nan. Yace: "Akwai Jihohin da suka samu nasara a cikin shirin adashin gata mai dogon zango na Ja'iz, kuma akwai bukatar a kara ba da shawarwari ta yadda wannan tsari ya kasance anyi koyi da shi a fadin kasar nan."
Ya kuma kalubalanci hukumar da ta “hadi da jami’an mu da abokan huldar mu don samar da dangantaka mai dorewa ta yadda za su samu jarin jari mai yawa a ayyuka a kasa mai tsarki.”
Tun da farko a nasa jawabin shugaban Hukumar kula da aikin Haji ta kasa, Malam Jalal Arabi ya godewa shugaban kasa da mataimakinsa bisa ganin sun cancanci yiwa kasa hidima ta hanyar hukumar NAHCON.
Ya ce bisa la’akari da muhimmancin aikin da ke gabansu, sabuwar hukumar za ta yi aiki a matsayin tawaga don inganta ayyukan Hajji a Najeriya, tare da bayar da tabbacin cewa maniyyatan za su samu darajar kudinsu.
Shugaban hukumar ta NAHCON ya ce tuni tawagar sa ta fara aiki da ziyarar da ta kai kasar Saudiyya domin duba wuraren da za a fara gudanar da ayyuka a nan gaba.
Sabon shugabancin hukumar da aka kafa ya hada da Aliu Abdulrazaq (Kwamishinan harkokin Ma'aikata da kudi), Prince Anofi Elegushi (Kwamishina, Ayyukan Haji), da Farfesa Abubakar A. Yagawal (Kwamishina, Tsare-tsare & Bincike). Wakilan shiyyar da masu ruwa da tsaki sun hada da Dr. Muhammad Umaru Ndagi — Arewa ta tsakiya; Abba Jato Kala - Arewa maso Gabas; Sheikh Muhammad Bin Othman - Arewa maso Yamma; Tajudeen Oladejo Abefe - Kudu maso Yamma; Aishat Obi Ahmed - Kudu maso Gabas; Zainab Musa - Kudu maso Kudu; Farfesa Musa Inuwa Fodio — Jama’atul Nasril Islam, da Farfesa AdedimiziMahfouz Adebola - Majalisar Koli kan Harkokin Musulunci.
Har ila yau, wadanda suka halarci taron sun hada da ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate; Ministocin sufurin jiragen sama, Mista Festus Keyamo, SAN, da na cikin gida, Mista Olubunmi Tunji-Ojo.