Hanyoyi huɗu da Facebook ya sauya duniya

 


Dubi hoton da ke sama. Wannan shi ne yadda Facebook, ko kuma The Facebook kamar yadda aka sani a lokacin, ya ke lokacin da Mark Zuckerberg da wasu aminansa suka ƙaddamar da shi daga matsuguninsu na dalibai shekara 20 da suka gabata.

Tun daga wannan lokacin, shahararren shafin sada zumuntar na duniya ya sake fasali da yawa.

Amma manufarsa ba ta sauya ba: haɗa mutane a Intanet. Da Kuma samun maƙudan kuɗade daga talla.

Yayin da dandalin ke cika shekara 20, ga hanyoyi huɗu da Facebook ya canza duniya.

1. Facebook ya canza harkar sada zumunta

Sauran shafukan sada zumunta, irin su MySpace, sun fara aiki kafin Facebook - amma nan take shafin Mark Zuckerberg ya tashi bayan an ƙaddamar da shi a 2004, wanda ke tabbatar da yadda dandali irin wannan zai iya ɗaukan hankali cikin sauri.

MySpace Tom

ASALIN HOTON,MYSPACE

Bayanan hoto,

Tom shine abokin kowa na farko akan MySpace, wanda Tom Anderson ya ƙaddamar shekara guda kafin Facebook

A cikin ƙasa da shekara ɗaya masu amfani da shi sun kai miliyan daya, kuma a cikin shekara huɗu ya wuce MySpace - sakamakon fitar da sabbin abubuwa kamar 'tagging' mutane a hotuna.

Fita yawo da kyamarar zamani, sannan 'tagging' abokanka a cikin hotuna da yawa ya zama babban jigon rayuwar samari a ƙarshen shekarun 1990.

Ya zuwa shekarar 2012, masu amfani da shafin sun wuce biliyan daya kowanne wata, kuma, baya ga ɗan tuntuɓen da aka samu a ƙarshen shekarar 2021 - lokacin da masu amfani da shafin na yau-da-kullum suka ragu a karon farko zuwa biliyan 1.92, dandalin ya ci gaba da bunƙasa.

Ta hanyar faɗaɗa zuwa ƙasashen da ke da matsalar sadarwa da kuma ba da intanet kyauta, kamfanin ya ci gaba da riƙe tare da haɓaka yawan masu amfani da shafin Facebook. A ƙarshen 2023, Facebook ya ba da rahoton cewa masu amfani da shafin sun kai biliyan biyu a kullum.

Maganar gaskiya, Facebook ba shi da farin jini a tsakanin matasa kamar yadda ya ke a baya. Duk da haka, ya kasance mafi shaharar hanyar sadarwar zamantakewa a duniya, kuma ya haifar da sabon zamani na ayyukan zamantakewa a Intanet.

Wasu suna ganin Facebook da abokan hamayyarsa a matsayin abubuwan da ke ƙarfafa zamantakewa, wasu kuma suna ganin su a matsayin masu ruruta halayen lalata.

2. Facebook ya rage yadda mutane ke ɓoye sirrinsu

Facebook ya nuna yadda tattara bayanan abubuwan da muke so da waɗanda ba mu so ya zama abu mai matuƙar riba.

...

ASALIN HOTON,FACEBOOK

A kwanakin nan, kamfanin da ya mallaki Facebook, Meta, wani katafaren kamfanin talla ne wanda, tare da ire-irensu Google, ke ɗaukar kaso mafi tsoka na kudin talla a duniya.

Meta ya bayar da rahoton kusan dala biliyan 34 na kuɗaɗen shiga a cikin a tsakiyar 2023, musamman daga bai wa masu talla ayyukan talla da ke harin masu amfani da shafin kai-tsaye; An bayyana cewa an samu riba ta kudi dalar Amurka biliyan 11.5.

Sai dai kuma Facebook ya nuna inda tarin bayanai zai iya tabarbarewa.

An ci tarar Meta sau da yawa saboda kuskuren sarrafa bayanan sirri.

Al’amarin da ya fi fitowa fili shi ne badaƙalar Cambridge Analytica a shekarar 2014, wanda ya kai ga Facebook ya biya dala miliyan 725 don sasanta shari’a saboda wani gagarumin satar bayanai da ya gudana.

A cikin 2022, Facebook ya kuma biya tarayyar Turai tarar Yuro miliyan 265 saboda damar da ya bayar na fitar da bayanan sirri daga shafin.

Kuma a shekarar da ta gabata, Hukumar Kare Bayanai ta Ireland ta ci kamfanin tarar Yuro biliyan 1.2, saboda sauya wurin bayanan masu amfani da shafin a ƙasashen Turai zuwa wurin da ya zarce zarafinsu. A halin yanzu dai Facebook na ɗaukaka ƙara kan tarar.

3. Facebook ya shigo da harkar siyasa intanet

Ta hanyar bayar da tallace-tallace zuwa masu amfani kai-tsaye, Facebook ya zama babban dandalin yaƙin neman zaɓe a duniya.

Trump a shafukan sada zumunta

ASALIN HOTON,REUTERS

Misali, a cikin watanni biyar gabanin zaɓen shugaban ƙasar Amurka na shekarar 2020, tawagar shugaba mai ci a lokacin Donald Trump ta kashe sama da dala miliyan 40 wajen tallace-tallace a Facebook, kamar yadda binciken Statista ya nuna.

Facebook ya kasance yana da hannu wajen sauya siyasar can ƙasa- ta hanyar bayar da dama ga ƙungiyoyin masu amfani da dandalin su taru, su gudanar da yakin neman zaɓe da kuma tsara ayyuka.

Rahotanni sun ce Facebook da Twitter sun taka muhimmiyar rawa a lokacin juyin-juya-halin ƙasashe Larabawa wajen taimakawa lokacin shirya zanga-zanga da yaɗa labaran abubuwan da ke faruwa a ƙasa.

An soki amfani da ake yi da Facebook domin gudanar da harkokin siyasa saboda irin abubuwan da kan iya biyo baya, ciki har da tasirin da ya ke da shi kan haƙƙin bil'adama. A cikin 2018, Facebook ya amince da rahoton Majalisar Dinkin Duniya wanda ya ce ya gaza hana mutanen da ke amfani da dandalin wajen "rura wutar tashe-tashen hankula" kan 'yan Rohingya a Myanmar.

4. Facebook ya ƙara wa Meta ƙarfi.

Da babbar nasarar da Facebook ya samu, Mark Zuckerberg ya gina dandalin sada zumunta da kuma daular fasaha wadda ba a taba ganin irin ta ba ta fuskar yawan masu amfani da kuma tasiri.

.

ASALIN HOTON,REUTERS

Kamfanoni masu tasowa, da suka haɗa da WhatsApp da Instagram da Oculus, duk an saye su ne a ƙarƙashin inuwar kamfanin Facebook, wanda ya canza suna zuwa Meta a cikin 2021.

Meta yanzu ya ce fiye da mutane biliyan uku suna amfani da aƙalla ɗaya daga cikin manhajojinsa a kowace rana.

Kuma lokacin da ya kasa siyan abokan hamayyarsa, ana zargin Meta da kwaikwayarsu - domin ya ci gaba da mamaye ko ina.

Siffar Labaru masu ɓacewa a Facebook da Instagram yayi kama da wani mahimmin fasalin da aka samu a Snapchat; Instagram Reels shi ne amsar kamfanin ga ƙalubalen da manhajar TikTok na raba bidiyo ya haifar; Kuma Threads shi ne ƙoƙarin Meta na kwaikwayon X, wanda aka fi sani da Twitter.

Dabarun sun zama mafi mahimmanci fiye da kowane lokaci, sakamakon ƙaruwar gasa da kuma ƙarin matsin lamba daga hukumomi masu sanya ido.

A cikin 2022, an tilasta wa Meta ya siyar da Giphy mai yin GIF duk da cewa zai yi hasara, saboda fargabar wuce gona da iri a sakamkon mamaye kasuwa.

Shekara 20 masu zuwa?

Ci gaban da Facebook ke samu na nuni da ƙoƙarin da Mark Zuckerberg ke yi na tabbatar da tasirin shafin.

Amma kiyaye kambinsa a matsayin mashahurin dandalin sada zumunta zai zama babban ƙalubale a cikin shekaru 20 masu zuwa.

Meta yanzu yana matuƙar yunƙuri don gina kasuwancinsa wurin haɗa ƙirƙirarriyar duniya ta Metaverse, wadda ake iya cewa ya sha gaban manyan abokan hamayyarsa kamar Apple.

Ƙirƙirarriyar basir ta AI shi ma abu ne da Meta ya mayar da hankali a kansa.

Don haka, yayin da kamfanin ya ci gaba da nisa daga tushen sa na Facebook, zai bayar da sha'awa a ga abin da zai faru a nan gaba da wannan shahararriyar manhajar.

(bbc hausa)

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki