Har Yanzu 29 Ga Watan Afurilu Ce Ranar Karshe Ta Rufe Yin Bizar Hajin 2024 - Laminu Rabi'u Danbaffa
Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan a yau yayin liyafar cin nasara a kotun koli da jami’an hukumar alhazai 44 suka shirya cewa masarautar Saudiyya ta tsaya tsayin daka kan dokokin aikin Hajji na shekarar 2024. A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya bukaci jami’an cibiyar Hajji da su rika fadakar da al’umma wannan wa’adin don tabbatar da cewa ba a bar wani mahajjaci a baya ba. Da yake jawabi kan liyafar da aka karrama Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusif, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya bayyana cewa, wannan shi ne mataki na farko, kuma ana sa ran za a samu ci gaba. Ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da Ya yi wa Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusif jagora ya kuma kare shi a dukkan al’amuransa. A nasa jawabin shugaban kungiyar Jami'an Alhazai na kananan hukumomi na Jahar Kano wanda kuma ya kasance jami’in Alhaz...