KANSEIC Ta Ce 'Yan Takarar Ciyaman Zasu Biya Kudin Fom 10M, Na Kansiloli Kuma 5M
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano, KANSIEC, ta sanar da cewa masu neman shugabancin karamar hukuma da kansiloli zasu biya Naira Miliyan 10 da Miliyan 5 a matsayin kudin takara, inda tace ba za a dawowa da kowa kudin ba.
Shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya bayyana hakan yayin gabatar da ka’idoji da jadawalin gudanar da zaben kananan hukumomi a shelkwatar hukumar a yau Alhamis.
Yayi bayanin cewa masu takarar shugabancin karamar hukuma dole ne su biya Naira Miliyan 10 a yayin da masu neman kujerar Kansila za su biya Naira Miliyan 5.
Acewarsa, ka’idojin da aka fitar yana dauke da abubuwan da aka hana da wadanda aka amince a yi a zaben dake tafe sannan ya gargadi kan ‘yan takara game da karya ka’idojin.
Daga cikin ka’idojin sun hada da cewa dole ne duk mai neman shugabancin karamar hukuma ya kai shekaru 30 zuwa sama.
Sannan mai neman takarar Kansila dole ne ya kai shekaru 25 zuwa sama kuma ya kasance yana da shedar katin jam’iyya.
“Masu neman shugabancin karamar hukuma dole ne su kasance ba a taba samunsu da laifi ba, dole ne su zama suna da lafiya kuma sun mallaki shedar kammala Sakandire.
” Dukkan ‘yan takara dole ne su zama basa ta’ammali da miyagun kwayoyi kuma basa cikin kungiyoyin asiri”, inji shi.
Malumfashi ya kuma ce za a fara gangamin yakin neman zabe a ranar 6 ga watan Satumba tare da rufewa a ranar 31 ga watan Oktoba, inda ya bukaci jam’iyyun siyasa su gudanar da gangamin yakin neman zabe cikin kwanciyar hankali.
Sannan shugaban hukumar ya ce baza su lamunci duk wani nau’i na cin hanci da rashawa ba.
(Daily Nigeria Hausa)