'Yan Bindiga Sun Sace Mutum Talatin Lokacin Sallah A Zamfara
Wani ganau ya ce ’yan bindigar sun mamaye masallacin ne da misalin karfe 5 na Asuba, a lokacin da ake shirin fara salla. Garba ya ce, “Za mu fara sallar asuba, kwatsam sai ’yan bindiga suka shigo masallaci suka umarci kowa ya fito ya bi su. “Kowa ya yi kokarin guduwa domin tsira amma suka tare ko’ina suka gargade mu cewa za su kashe duk wanda ya yi yunkurin guduwa. “Na samu na iya tsalle daga tagar kuma da sauri na shiga wani kango da ke kusa da masallacin na boye kaina,” in ji shi. Shaidan ya bayyana cewa ’yan bindigar sun bar baburansu a nesa da masallacin don kada a lura da motsinsu. Ya kara da cewa, “Daga baya sun tafi da mutanen zuwa inda baburansu suke, suka tafi da su.” A cewarsa, adadin mutanen da aka sace a masallacin zai iya wuce 30. Ya kara da cewa “masallacin ya cika a lokacin da suka kai hari kuma kadan ne daga cikin mu suka samu tsira.” Daya daga cikin shugabannin yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce jami’an tsaro na ci gaba da bin diddigin ’yan bindiga...