Wasu Daga Yan Asalin Kiru Da Bebeji Da Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Samawa Ayyukan Gwamnati
Idan za a iya tunawa, Hon Abdulmumin Jibrin Kofa, ya yi shekaru huɗu (2011-2015) a wa’adin mulkinsa na farko, sai kuma ƙasa da shekaru biyu (2015-2016) da kuma (2018-2019) a wa’adi na biyu, sai kuma watanni shida kacal (2019-Jan 2020) a wa’adinsa na uku. Yanzu kuma a wa’adinsa na huɗu da yake kai, shekara ɗaya ke nan da ɗoriya (2023-2024).
A sanarwar da hadimin Dan Majalisar kan Harkokin yada labarai, Sani Ibrahim Paki ya sanyawa hannu, yace amma duk da haka, ya yi namijin ƙoƙari wajen samar wa matasa masu matsayin karatun digiri, HND, difloma da ma sakandare ayyukan yi a matakin gwamnatin tarayya.
Tuni wasu daga cikin waɗannan mutanen suka fara yin girma a wuraren ayyukan nasu kuma sun samu rufin asiri suna ci gaba da ɗaukar nauyin iyalai da ’yan uwansu da jamaa da kuma mazabu da yankunan da suka fito. Muna taya su murna.
Yanzu haka kuma ɗan majalisar na iya baƙin ƙoƙarinsa wajen samar wa ƙarin masu matakan karatu daban-daban ayyukan yi a gwamnatin tarayya. Insha Allahu offers zasu fara fitowa bada dadewa ba kuma zaa sanar da jamaa.
Ga jerin sunayen wasu daga cikin mutanen da dan majalisa Hon Kofa ya samar wa ayyukan a matakin tarayya a baya.