KARIN BAYANI KAN AYYUKAN RAYA KASA DA HON ABDULMUMIN JIBRIN KOFA KE AIWATARWA A KIRU DA BEBEJI
Ga jerin dukkan ayyukan da dan majalisar ya aiwatar da kuma mazabun da suka amfana da su kamar haka:
AIKIN SAMAR DA SOLOLI DA AKA KAMMALA
Mazabar Kiru 175, mazabar Yalwa 25, mazabar Bargoni 20, mazabar Ba’awa 20, mazabar Badafi 20, mazabar Zuwo 20, mazabar Yako 20, mazabar Bebeji 175, mazabar Gwarmai, mazabar Ranka 10, mazabar Durmawa 20, mazabar Baguda 20, mazabar Tariwa 20, mazabar Gargai 20, mazabar Kuki 20.
JIMLA – 600
AIKIN SAMAR DA SOLOLI DA AKE CI GABA DA GABATARWA
Mazabar Kiru 30, mazabar Yalwa 40, mazabar Dangora 14, mazabar Maraku 14, mazabar Dashi 12, mazabar Tsaudawa 12, mazabar Galadimawa 12, mazabar Kogo 12, mazabar Bauda 12, mazabar Dansoshiya 12, mazabar Bebeji 40, mazabar Damau 20, mazabar Gwarmai 10, mazabar Ranka, mazabar Wak 20, mazabar Rantan 15, mazabar Anadariya 10, Gwarmai-Kofa 40, mazabar Rahama 18, garin Tiga 60, garin Jibga 6.
JIMLA - 419
Ansa solar guda 287 a mazabun kiru/Bbj Inda ko wanne babban akwatu ya sami guda daya.
Jimlar solar da aka saka da wadanda ake aikin sakawa yanzu haka sun zama 1,306
GININ AZUZUWAN DA AKA KAMMALA
Mazabar Zuwo – block daya mai azuzuwa 2, mazabar Tariwa - block daya mai azuzuwa 2, mazabar Kofa - block daya mai azuzuwa 2, mazabar Bebeji - block 3 mai azuzuwa 6.
GININ AZUZUWAN DA AKE CI GABA DA YI
Mazabar Bebeji – block 5 mai azuzuwa 10, mazabar Yalwa – block 5 mai azuzuwa 10, mazabar Kofa – block daya mai azuzuwa 2 (UBE Primary School Kofa), mazabar Tariwa – block daya mai azuzwa 2 (Ahababu).
RIJIYOYIN BOREHOLE MASU AMFANI DA HASKEN RANA
Mazabar Yako - 1, mazabar Kiru - 4, mazabar Yalwa - 1, mazabar Durmawa - 1, mazabar Bebeji - 4
JIMLA: 11
FAMFON TUKA-TUKA
Mazabar Damau - 1, mazabar Kogo – 1
GURIN NOMAN RANI:
Mazabar Kofa Green House guda 4 mai hade da borehole mai sola.
Wadannan ayyukan dai ba iya su ke nan ba a 2024; akwai wasu da dama da za su zo nan ba da jimawa ba kuma a hankali duk mazabu zasu amfana. Za mu yi iya bakin kokarinmu wajen tabbatar da cewa kasafin kudi na 2025 ya fi na 2024 samar wa da mazabarmu ayyukan raya kasa, musamman wajen gina tituna.
Sani Ibrahim Paki
Media Aide to Honourable Member
14-12-2024