Yadda Farfesa Abdullahi Sale Ya Kawo Sauyi A Harkokin Aikin Hajjin Najeriya - Daga Nura Ahmad Dakata

A wani gagarumin yunkurin kawo sauyi, harkar aikin Hajji na fuskantar  sauye-sauye a karkashin jagorancin Farfesa Abdullahi Sale Usman, shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON).




A cikin kankanin lokaci da aka nada Farfesa Usman, ya kafa sabon ma’auni na kirkire-kirkire, inganta aiki, da rikon amana a tafiyar da ayyukan Hajji da Umrah a Najeriya.




Sake Tsara Ayyuka:

Daya daga cikin manyan gyare-gyaren da Farfesa Usman ya bullo da shi, shi ne kokarin kawo sauyi kan tantance maniyyata aikin Hajji ta amfani da na’ura. Mahajjata nan gaba kadan za su iya yin rajista ba tare da wata matsala ba ta hanyar da aka samar na yanar gizo, tare da rage cikas da tabbatar da gaskiya.




Haka nan,  tsarin yana nuna hakikanin matsayin biyan kudin da maniyyaci da neman biza, da shirye-shiryen tafiya, yana Æ™arfafa mahajjata da mahimman bayanai kamar a tafin hannunsu.

 

Matakan Rage Farashi:

Bisa la'akari da nauyin kuÉ—i da ke kan masu zuwa aikin hajji, Farfesa Usman ya ba da fifiko kan  tattaunawa da kamfanonin jiragen sama da masu yi wa alhazai hidima da hukumomin Saudiyya don tabbatar da ganin an samu ragi a farashin. Wannan yunÆ™urin zai rage tsadar kudin kujerar aikin Hajji ba tare da lalata ingancin ayyukan da ake gudanarwa ba ga alhazai.




Inganta Jin Dadin Alhazai: Jin dadin alhazan Najeriya ya kasance jigon gyare-gyaren Farfesa Usman.

Hukumar NAHCON, a karkashin jagorancinsa, ta aiwatar da tsauraran matakai don inganta matsayin masauki, harkokin sufuri, da ayyukan kiwon lafiya. Mahajjata yanzu zasu ji daÉ—in samun ingantattun asibitoci, kwararrun ma'aikatan kiwon lafiya, da gaggauta kai agajin gaggawa idan an bukaci haka yayin aikin hajji.




Yin Aiki Da Masu Ruwa Da Tsaki: Farfesa Usman ya kuma samar da hadin gwiwar da ba a taba ganin irin sa ba da masu ruwa da tsaki, da suka hada da hukumomin jin dadin alhazai na jiha, da masu kamfanonin jirgin yawo, da sauran abokan hulda masu zaman kansu.

Tsarin hanyar tuntubar da Farfesa Sale ya samar, ta tabbatar da cewa dukkan bangarorin sun ba da gudummuwarsu wajen ganin an inganta ayyukan Hajjin Najeriya.




Kaifafa Basirar Ma’aikata: Bisa la’akari da bukatar kwararrun ma’aikata, hukumar a karkashin jagorancin Farfesa Abdullahi Sale, nan ba da jimawa ba za ta kaddamar da shirye-shirye kaifafa basirar jami’an kula da alhazai da masu gudanar da masu kamfanonin jigilar alhazai.

Taron karawa juna sani da na bayar da horo,  suna baiwa masu ruwa da tsaki ilimi da basirar da ake bukata don isar da ayyuka kamar yadda yake a matakin duniya.




Samun Dorewar Wannan Ci gaba: Domin bin tsarin da duniya ke kai a halin yanzu, Farfesa Usman ya bullo da tsare-tsare masu dorewa da nufin rage kudin muhalli da na ayyukan Hajji.

Waɗannan sun haɗa da zaɓun sufuri masu dacewa da muhalli da shirin sarrafa shara tare da haɗin gwiwar hukumomin Saudiyya.




Kokarinsa Wajen Tabbatar Da Kididdiga Da Tsantsaini Yayin Mayar Da Kudade Ga Alhazai : Baya ga gyara day a kawo kan harkokin aiki, Farfesa Usmanya dauki kwakkwaran mataki don tabbatar da tsantsaini da kididdiga wajen mayar da kudade ga alhazan da suka je hajin 2023. Ya samar da wata sabuwar hanyar ta na’urar zamani wacce ke bada dama ga alhaji ya mika bukatarsa ta a biya shi kudinsa,yayin hakan ya sanya mutane sun samu aminci kan yadda ake gudanar da aikin mayar da kudaden da masu hakki




Samun Yabo A Fadin Kasa: Sauye-sauyen da Farfesa Abdullahi Sale ya kawo a hukumar NAHCON, ya samu yabo sosai daga malaman addini, Kamfanonin Jirgin yawo, da kuma mahajjata. Mutane da yawa sun bayyana shugabancin Farfesa Usman a matsayin babban alkhairi, wanda ke nuna sabon zamani na inganci da kwarewa a harkar aikin Hajji.




Abun Da Za  A Fuskanta Nan Gaba: Yayin da aka samu nasarori da yawa, Farfesa Usman ya tsaya tsayin daka kan jajircewarsa na ci gaba da inganta ayyuka. Burinsa na gaba ya haÉ—a da Æ™arin sabbin hanyoyin aiki na zamni, faÉ—aÉ—a haÉ—in gwiwa, da ingantattun ayyuka don tabbatar da cewa Najeriya ta ci gaba da riÆ™e matsayinta na jagora a ayyukan Hajji na duniya.




Kokarin da Farfesa Abdullahi Sale Usman ya yi na kawo sauyi a fannin kula da harkokin ayyukan Hajji a Najeriya ya zama shaida ga karfin jagoranci mai hangen nesa, wanda ya bar tsarin da ba za a taba mantawa da shi ba a harkar aikin Hajji da kuma kafa fage mai inganci ga alhazai masu zuwa.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki