Posts

Showing posts from December, 2023

Hajj 2024 : Hukumar Alhazai Ta Bauchi Ta Siyar Da Kujerun Haji Guda 1700- Imam Abdurrahman

Image
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi ta sayar da kimanin guraban kujerun aikin hajji akalla *1700* daga cikin guda *3364* da Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta ware wa Jihar Bauchi. A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Muhammad Sani Yunusa ya sanyawa hannu, yace Sakataren zartarwa na hukumar jindadin alhazan ta jihar Bauchi Imam Abdurrahman Ibrahim Idris,shi ne bayyana hakan yayin  zantawarsa da manema labarai kan shirye shiryen aikin hajji daga Bauchi, inda yace wayarda alumma kan sabbin tsare tsaren aikin hajjin na shekarar 2024 daya gudana a jihar Bauchi yayi tasiri kwarai da gaske. Imam Abdurrahman ya alakanta nasarar gudanar da atisayen wayarda kan alummar ne da irin gudumawa da goyon bayan da tsarin ya samu daga sarakunan mu na jihar Bauchi da shugabannin kananan hukumomi da limamai da sauran masu ruwa da tsaki a aikin Hajji. Ya kara da cewa sabbin tsare-tsare na Saudiyya kan ayyukan Hajji na shekarar 2024 ne suka tilastawa kasashe fara  s

Shugaban Majalisar Dokoki Ta Katsina Ya Raba Tallafin Naira Miliyan 35

Image
Kakakin Majalissar Dokoki ta Jihar Katsina, Nasir Yahaya, ya bayar da tallafin Naira Million Talatin da HuÉ—u da Dubu ÆŠari Tara da Hamsin. (34,950,000) ga Mutum Dubu Ukku (3000) a filin wasan Ƙwallon Kafa dake Daura Hadimin tsohon Shugaban Najeriya, Buhari Sallau, ya rawaito a shafinsa na Facebook cewa, an bayar da Tallafin ga Marayu, Limamai, Zawarawa, Masu Ƙananan Sana'oi, Exco, Mata, Matasa, Students, yan Media, Dagattai, MabuÆ™ata, yan siyasa, Ƙungiyar Teloli, Ƙungiyar Masu Shayi da Masu chajin waya, da sauran su. Inda ko wanne daga cikinsu zai amfana da Tallafin, Naira Dubu Goma (10,000) Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda PhD, yayi Jin-Jina gami da fatan Alkhairi ga Kakakin Majalissar akan wannan abin Alkhairi da yayi, sannan yayi roÆ™o gami da Jan hankali ga wanda suka amfana da wannan Tallafin da suyi amfani dashi ta hanyar daya dace, domin su bunÆ™asa Kasuwar su.  Haka kuma Mataimakin Shugaban Jam'iyyar APC na Jihar, Alh. Bala Abu Musawa, ya taya mutanen D

Shugaban NAHCON Ya Ziyarci Ofishin Jakadancin Saudiyya na Abuja.

Image
Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya wato NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi, ya kai ziyarar ban-girma zuwa ofishin Huldar Jakadanci na Saudiyya inda ya gana da Jakadan Saudiyya dake Abuja, Ambasada Faisal Ibrahim Al-Ghamidy, a ranar Laraba   A sanarwar da Hukumar ta fitar ta ce, Shugaban ya kai ziyarar ce da nufin bunkasa dangantaka da habakar da hadin-gwiwa tsakanin bangarorin biyu.   Malam Arabi ya jaddada jin dadinsa ganin yadda Jakadan Kasar Saudiyya Ambassada Faisal ke bada cikakken goyon-baya ga Hukumar da tareraya irinta Huldar Jakadanci karkashin  Ofishin Jakadancin Saudiyyar. Sanarwar tace ziyarar, ta bayyana karara yadda dadaddiyar alaqa ta jituwa ke tsakanin NAHCON da Ofishin Jakadancin Saudiyyar, abinda ke nuni da fahimtar-juna da hadin kai dake wanzuwa a tsakanin Kasashen biyu. A Yayin ganawar, bangarorin biyu  sun zanta batutuwa masu ma’anar gaske, abunda ke tabbatar da muhimmancin tarayyarsu wajen kara inganta gudanar da Al-amurran Aikin Hajji A Najeriya Sh

Kotun Koli Ta Tsayar Da Ranar Da Za Ta Saurari Karar Zaben Gwamnan Kano

Image
Kotun koli ta sanya ranar Alhamis 21 ga watan Disamba domin cigaba da sauraron karar zaben gwamnan Kano tsakanin gwamna Abba Kabiru Yusuf na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP da Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC.  KANO FOCUS ta rawaito cewa a cikin sanarwar da magatakardar kotun daukaka kara ta aikewa lauyoyin bangarorin biyu, kotun za ta saurari karar da NNPP ta shigar da kararrakin wasu jam’iyyu.  Gwamna Yusuf na kalubalantar hukuncin da wasu bangarori uku na kotun daukaka kara suka yanke wanda ya soke nasarar da ya samu tare da tabbatar da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke. Kotun sauraron kararrakin zabe karkashin jagorancin mai shari’a Osedebay ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano a watan Maris.  Kotun daukaka kara ta yi watsi da karar da Gwamna Yusuf ya shigar bisa matsayinsa na zama mamba a jam’iyyarsa sannan ta zargi kotun da yin watsi da hujjar da ta yanke. Kotun ta kori Gw

Kofa Ya Raba Tallafin Kudi Ga Mata Guda Dari Biyar A Mazabarsa

Image
A ci gaba da tagomashin arzikin da yake yi wa mutanen mazaÉ“arsa, Abdulmumin Jibrin Kofa, É—an Majalisar Wakilai na Kiru da Bebeji daga jihar Kano, a ranar Lahadi ya sake gwangwaje mata 500 da tallafin kuÉ—i. A sanarwar da h adimin É—an majalisar kan yaÉ—a labarai, Sani Ibrahim Paki  ya fitar, yace an  yi taron rabon tallafin ne a mahaifar É—an majalisar da ke Kofa a Ƙaramar Hukumar Bebeji, Kano, kuma wannan shi ne karo na bakwai da yake raba irin wannan tallafin a ’yan makonnin nan.  Idan za a iya tunawa, a baya É—an majalisar ya raba tallafin ga shugabannin al’umma, mata da matasa, É—alibai, ’yan social media, malamai da masu rike da sarautun gargajiya.  Wannan ne dai rabon tallafi karo na bakwai tun bayan farawa, kuma karo na biyu ga mata. Bugu da Æ™ari, É—an majalisar ya karÉ“i baÆ™uncin fitacciyar ’yar asalin Bebejin nan, kuma jigo a jam’iyyar NNPP, Hajiya Azumi Babeji, wacce ita ma ta halarci bikin sannan ta gabatar masa da takardar nadin da Gwamnatin Jiha

Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Yi Ga NAHCON Da Ta Samar Canjin Dala Kan Farashin Gwamnati Ga Maniyyata

Image
Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa, ya bukaci Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta kara zage damtse wajen ganin an samu dala a farashin gwamnati  ga wadanda zasu halarci aikin hajjin bana. A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya bayyana hakan ne a wata ganawa da kungiyar Arewa New Agenda a wata ziyarar wayar da kai da hukumar alhazai ta kasa suka kai Kano, wanda aka gudanar  a ofishinsa. Ya kara da cewa karin kudin aikin Hajjin bana da kuma karancin lokacin biyan kudi na daga cikin matsalolin dake kawo tsaiko wajen biyan kudaden ajiya. Da yake mayar da jawabi kan wadannan matsalolin, shugaban tawagar kungiyar Arewa New Agenda daga Hukumar Alhazai ta kasa, Dakta Muhd Lawan Salisu, ya tabbatar wa darakta Janar din cewa, sun dukufa wajen hada kai da hukumomin da abin ya shafa, ciki har da Sarkin Musulmi, domin mika kokon bara ga

Gwamnatin Kano Ta Tabbatar da Gano Illar Bata Tarbiyya Yara Mata A Shirin Tallafawa Ilimi Na AGILE

Image
Biyo bayan zarge-zargen bata tarbiyya da ake yiwa shirin tallafawa ilimin yaya mata na AGILE, ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta gudanar da taron karawa juna sani na yini biyu kan shirin. Premier Radio ta rawaito a shafinta na Facebook cewa, Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, wanda ya yi magana a yayin taron na masu ruwa da tsakin da ke nazarin horar da dabarun rayuwa a karkashin shirin, ya ce ma’aikatar ta fitar da wani sabon salo na abubuwan da shirin ya kunsa. Ya ce malamai sun yi korafin cewa a cikin shirin akwai wasu abubuwa da basu amince da su ba inda suka duba korafin nasu kuma suka gano matsalar dake cikin sa yayin da aka cire duk wani da ya saba da al’ada da koyarwar addnini muslunci. A nashi bangaren, co’odinetan shirin na AGILE a nan Kano, Alhaji Nasiru Abdullahi-Kwalli, ya ce ma

NAHCON Ta Dakatar Da Rabon Kujeru Ga Kanfanonin Jirgin Yawo

Image
Hukumar Aikin Hajji ta kasa (NAHCON) a dakatar da rabon kujeru aikin Hajjin 2024 ga kamfanonin jirgin yawo 40 da suka yi nasarar samun aikin jigilar maniyyata. NAHCON ta dakatar da rabon kujerun ne saboda korafe-korafen da zargin rashin adalci da wasu kamfanonin da ba su yi nasara ba ke yi. Mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta ce hukumar na sane da irin wadanna zarge-zarge daga wasu kamfanonin da ba su yi nasara a tantancewar da aka yi ba. Don haka aka dakatar da akai na tsawon awa 48 masu zuwa, domin daukar matakin da ya dace, tabbatar da tsafta a aikin da kuma kare martabar kukumar. (AMINIYA)

Na shiga matsananciyar damuwa da hare-haren 'yan bindiga a 'yan kwanakin nan - Gwamnan Zamfara

Image
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook Inda yace "A madadin gwamnatin Jihar Zamfara, ina miÆ™a saÆ™on ta'aziyya da jaje ga al'ummar Æ™aramar hukumar Zurmi, musamman iyalai da ‘yan uwan waÉ—anda suka rasa rayukansu a harin ta'addanci da 'yan bindiga suka kai garin"  Ina son tabbatarwa da al'umma cewa gwamnatina za ta bayar da tallafi da agajin gaggawa ga mutanen da abin ya shafa. Sannan ina mai tabbatar da cewa muna nan jajirce akan tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'ummar Zamfara baki É—aya. Ina sane da sadaukarwar da jami’an tsaro suke yi a Æ™oÆ™arin da suke na kare rayukan al’umma, gwamnatina za ta ba su duk wasu kayan aiki da kuma tallafin da suka dace domin yaÆ™ar ‘yan bindiga, ba za mu huta ba har sai Zamfara ta samu cikakken tsaro insha Allahu.   WaÉ—annan sabbin hare hare sun biyo bayan nasarar da jami'an tsaro suka samu ne, na kashe shugabannin 'yan ta'addan. Ciki har da nasarar

Shugaban Hukumar NAHCON Ya Karbi Rahoto Kan Masaukin Alhazai Tare Da Alkawarin Sake Inganta Ayyuka

Image
Mai rikon mukamin Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Malam Jalal Ahmed Arabi, OON, fwc, ya ce ba da fifiko tare da inganta jin dadin mahajjata da ayyukansu shi ne babban aikin da Hukumar za ta gudanar a lokacin aikin Hajjin shekarar 2024. A sanarwar da Mataimakin daraktan yada yada labarai da dab'i na hukumar, Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, yace Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar rahoton kwamitin duba sharuÉ—É—an masauki da ciyarwa yau a dakin taro na hukumar Ya ce samar da ingantacciyar hidima aiki ne mai matukar muhimmanci da hukumar za ta bi domin cika aikinta tare da dorewar amana da amincewar jama’a da kuma alhazai. A cewarsa, gabatar da rahoton da shawarwari a cikinsa “zai taimaka matuka wajen farfado da kwarin gwiwa da amincewar mutane da alhazai musamman a gare mu. “Ina so in gode muku bisa sadaukarwar da kuka yi. Wannan rahoto da shawarwarin ba shakka za su ba da gudummawa don haÉ“aka hanyoyin ci gaba da aiwatar da abu

Labari Da Dumiduminsa: 'Yan Majlisar Jahar Rivers 27 Masu Biyayya Ga Wike Sun Bar PDP Zuwa Jam'iyyar APC

Image
Akalla ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas 27 cikin 32 ne suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC, sakamakon rikicin da ya barke tsakanin gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara da ministan babban birnin tarayya (FCT). Nyesom Wike ya zurfafa. Wani dan majalisar, Enemi George, ya tabbatar wa gidan talabijin na Channels cewa ‘yan majalisar 27 na karkashin jagorancin Martin Amaewhule ne. 'Yan majalisar sun yanke Wannan hukuncin ne a yayin zamansu na safiyar ranar Litinin (DailyNews24)

Gwamnan Katsina Ya Ceto Wanda Yan Ta'adda Suka Sace

Image
Gwamnan Katsina, Dikko Raddah, ya jagoranci fatattar ’yan bidiga a kauyen Zakka a Karamar Hukumar Safana ta jihar. Gwamnan ya jagornaci jami’an tsaro hadin gwiwa wajen ceto wani matashi da ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi. Dikko Radda ya jagoranci kai daukin ne a lokacin da ya je karamar hukumar kaddamar da shirin tallafi na mataimakin shugaban majalisar jihar, Abduljalal Runka. Sakataren yada labaran gwamna, Kaula Mohammed, ya ce kafin kaddamar da tallafin ne jami’an tsaro suka samu kiran gagawa cewa ’yan ta’adda sun kai hari kauyen Zakka. Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito Kaula na cewa, nan take gwamnan ya dakatar da shirin, shige gaba aka fattaki ’yan bindigar, aka ceto matashin. Daga nan gwamnan ya ba da umarnin kai mutumin asibiti domin kula da shi, saboda harbin sa da aka yi a kafa.

Sanatoci Sun Sallama Albashinsu Na Disamba Ga Mutanen Tudun Biri

Image
Sanatocin Najeriya gaba dayansu sun sadaukar da albashinsu na watan Disamba ga mutanen da harin bom da jirgin soji ya samu a wurin taron Mauludi a Jihar Kaduna. Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya sanar cewa sanatocin su 109 sun amince a ba da albashin nasu a matsayin gudunmuwar ga mutanen Tudun Biri. Sanata Barau wanda ya yi bayani a yayin ziyararsu fadar gwamnatin Kaduna domin jajanta wa Gwamna Uba Sani kan tsautsayi, ya bayyana cewa albasjin ya kama Naira miliyan 109. Ya ce hakika sun yi bakin ciki bisa tsautsayin da ya auka wa al’ummar garin na Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi, kuma majalisar ta sha alwashin yin bincike domin gano musabbabin abin da ya faru. Gwamna Uba Sani a jawabinsa ya mika godidyarsa ga dukkan ’yan majalisar da suka jajanta masa, inda ya bukaci su tabbatar da Hakimin Yan Tudun Biri ya fito kunya ta hanyar yi musu adalci. Ya kumu nuna rashin jin dadinsa bisa yadda wasu ke neman sanya rigar addini ko kabilanci a kan ab

Hajj 2014 : Hukumar NAHCON Ta Kafa Kwamitin Bitar Ka'idojin Samar Da Abinci Da Gidaje.

Image
Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta kaddamar da wani kwamiti da zai yi nazari kan wasu sharuddan da suka shafi masauki da abinci don samar da ingantacciyar hidima a lokacin aikin Hajjin 2024. A sanarwar da Mataimakin daraktan yada labarai da dab'i na Hukumar Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, yace da yake jawabi a wurin taron, mai rikon Shugabancin Hukumar,  Malam Jalal Ahmad Arabi OON, fwc, ya bayyana cewa sake duba ka’idojin da ake da su za su taimaka wajen inganta ayyukan masu ba da hidima wanda hakan zai amfanar da Alhazan Najeriya. A cewarsa, kundin tsarin gudanarwar kwamitin ba sabon sabon abu ba ne, amma wata hanya ce kawai ta yin la'akari da tsarin da ake da shi don samar da kyakkyawan sakamako. “Abin da muke yi yanzu ba wai sabon abu  ba ne kawai don inganta yadda muke yin abubuwa. Kamar yadda yake faruwa a wasu sassa na duniya, muna bukatar mu kasance da Æ™wazo. Kamar yadda al'ada ce ta duniya, dole ne mu inganta ta hanyoyinmu, don dacewa da mafi kyaw

Yanzu-Yanzu: Ganduje ya sake nada Aminu Hikima sabon mukami a matakin kasa

Image
A cikin sanarwar da Aminu Dahiru Ahmed ya fitar a shafinsa na Facebook, ya ce, wannan  shi ne karo na hudu da Baba Ganduje ya nada ni. A lokacinsa na farko a matsayin gwamnan jihar Kano, ya nada ni babban mai taimaka masa na musammam kan harkokin daukar hoto. Haka kuma a wa’adinsa na biyu ya sake nada ni a Wannan matsayi.   Lokacin da ya bar ofis bayan shekaru takwas, ya nada ni mai daukar hotonsa na kashin kai. Nadin na baya-bayan nan shi ne na hudu.   Aminu Dahiru yace Baba Ganduje ya yi min abin da uba kawai zai yi wa dansa. Ya dauki nauyin karatuna da sauran abubuwa da yawa. "Wacce irin ni'imomin Ubangijinku kuke karyatawa"? A matsayina na mai daukar hotonsa, ina da abubuwa da yawa da zan ce game da Baba Ganduje. Mai daukar hoto yana aiki tare da maigidansa. Ni ma na yi aiki tare da Baba Ganduje tsawon wadannan shekaru. Ina shaidawa tsohon gwamnan yana da riko da addini, mai tausasawa, mai kirki, mai yarda da mutuntawa har da wadanda ke karkashinsa. Kasanc

Yanzu-Yanzu: Zulum ya amince da nadin Mohammed Dawule a matsayin mai rikon Hukumar Alhazai ta Jahar Borno

Image
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da nadin Mohammed Dawule Maino a matsayin mukaddashin sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jihar Borno. An bayyana nadin ne a ranar Lahadin da ta gabata a wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Borno, Hon. Bukar Tijjani. Sakataren gwamnatin jihar ya kara da cewa nadin wanda ya fara aiki nan take, ya dogara ne akan cancanta da kuma bayanan shekarun baya a aikin gwamnati. Har zuwa lokacin da Dawule ya nada shi mamba ne a sabuwar Hukumar Ilimi ta Larabci da Sangaya ta Jihar Borno (BOSASEB. Kafin nan, Dawule ya yi aiki a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Borno tsakanin 2015 zuwa 2022. Ya kuma yi aiki a Makarantar Sakandare ta islamiyya da ke Maiduguri da Kwalejin Gwamnati da ke Maiduguri da kuma Makarantar Alkur’ani ta Model da ke Konduga. An haifi Mista Dawule mai shekaru 50 a duniya a karamar hukumar Kaga da ke arewacin jihar Borno. Gwamna Zulum ya taya Mohammed Dawule Maino murna sannan ya ce yana fatan ci gaba da yi masa hid