Hajjin 2024: Wajibi ne ga maniyyata su biya kuɗin Hajji nan da makonni 2- Shugaban hukumar alhazan Kebbi

Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Kebbi, Alh Faruku Aliyu Yaro Enabo ya ja hankalin maniyyata a jihar da su hanzarta biyan kuɗin aikin Hajjin 2014 kafin nan da makonni biyu.

Jaridar Hajj Reporters Hausa, ta rawaito cewa Enabo ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi a yau Talata da Shuwagabannin Ƙananan Hukumomi 21 dake Jahar Kebbi a Babban Birnin Jahar, Birnin Kebbi.

A cewar shi , biyan kudin kafin wa’adin makonni biyun shi zai tabbatar da cewa maniyyatan sun ɗauki ƙuduri na aikin Hajji.

Ya ƙara da cewa Hukumar Alhazzai ta Ƙasar Saudiyya itace ta zo da sabbin tsare-tsare ta yadda dukkanin maniyyata za su samu biza kamin wata uku da tashi zuwa Ƙasa mai tsarki.

Bayan gabatar da shuwagabannin Hukumar, Daraktoti da Masu Bawa Gwamna Shawara, Alh Faruku Enabo ya ja hankalinsu da su bawa maraɗa kunya, ya ƙara da cewa duk wanda aka samu da laifi babu makawa za’a ɗauki matakin ladabtarwa.

(Hajj Reporters Hausa)

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki