Shugaban NAHCON Ya Yabawa Kungiyar AHUON Tare Da Bada Shawarar Horar Da Wakilansu
Mai rikon Shugabancin Hukumar Alhazai ta Najeriya, Malam Jalal Ahmad Arabi, OON, fwc, l ya yaba da gagarumin kokarin da kungiyar masu gudanar da aikin Hajji da Umrah ta Najeriya (AHUON) ke yi na shirya aikin Hajjin bana na 2024 ba tare da matsala ba ta hanyar horar da mambobinta kan sabon tsarin shirin.
Shugaban ya bayyana haka ne a taron karawa juna sani da kungiyar AHUON ta shirya a Otel din Immaculate dake Abuja.
Shugaban wanda ya kasance babban bako a wajen taron, ya jaddada bukatar samar da kyakkyawar alaka tsakanin NAHCON da kungiyar domin ganin Alhazai sun samu sauki
A sanarwar da Mataimakin daraktan yada labarai na hukumar, Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, yace Shugaban wanda ya samu wakilcin Daraktan sa ido da bin ka’ida, Alhaji Alidu Shittu, ya yabawa kokarin mai shirya taron na bayar da horon da nufin karawa mambobinsu ilimin sabbin ci gaba a aikin Hajji tare da yin kira gare su da su shiga cikin sabuwar Cibiyar bayar da horo kan ayyukan Hajji da Hukumar ta kafa don yin karatu na fannin aikinsu
“Shugaban kungiya, ina so in yi kira gare ka da membobinka da ka amfana da shirin horon da Cibiyar Hajji ta Najeriya ta shirya domin wayar da kan mambobinku kan abubuwan da ke faruwa a harkar Hajji. Yana iya ba ku sha'awar sanin cewa manyan ma'aikatan Hukumar sun kammala karatunsu ne a Cibiyar da Takaddar Gudanar da Aikin Hajji & Umrah."
Ya kuma bayyana cewa nan ba da dadewa ba Hukumar za ta fara hada-hadar maniyyata aikin hajjin 2024, ta hanyar amfani da harsunan gida wajen isar da sakonni ga Mahajjatan mu. "
“Za a yi amfani da gidajen rediyo na cikin gida da ke fadin kasar nan a wannan fanni saboda lokaci ya kusa cika na wa’adin da ma’aikatar Hajji ta Saudiyya ta kayyade.
Ya kuma ba da tabbacin hukumar ba za ta bar wani abu ba don ganin an samu gagarumar nasara a aikin Hajjin 2024, ya kara da cewa ci gaba da hadin kai da goyon baya da addu’o’in AHUON zai taimaka a wannan fanni.
Ya kuma nuna jin dadinsa ga kungiyar dangane da lokacinsu da dukiyoyinsu da aka tura su gudanar da aikin Hajji da Umrah da kuma damar da aka ba shi a matsayin babban bako na musamman.