Posts

Hajj2023: Hukumar NAHCON Ta Bawa Kano Kujerun Hajji 2,902

Image
Rabon ya kasance kamar haka: Abia 53 Adamawa. 2669 Anambara. 39 Bauchi. 3, 132 Bayelsa. 35 Binuwai. 236 Borno. 2,735 Cross Rivers. 66 Delta 74 Nassarawa. 1,567 Nijar. 5,165 Ogun. 1,139 Ondo 436 Osun. 1,054 Oyo. 1 441 Yobe. 1,968 Ebony 117 Edo 274 Ekiti. 197 Enugu. 40 FCT 3,520     Gombe. 2,301 Imo. 30 Jigawa. 1,525 Kaduna. 5982 Kano. 5,902 Katsina. 4,913   Kebbi. 4871 Kwara. 3,219 Legas. 3,576 Plateau. 1,984 Rivers. 50 Sokoto. 5,504 Taraba. 1,590 Za a saki jihar Kogi ne bayan kammala nazarin ayyukanta yayin da aka dakatar da rabon jihar Akwa Ibom saboda rashin sabunta lasisin aiki. A halin da ake ciki, ana sa ran dukkan jihohin za su mika wa Hukumar biyan kashi 50% na kudin kujerun 2022 kafin ranar 10 ga watan Fabrairu.  Rashin yin hakan ka iya sanyawa a rage yawan adadin kujerun da aka bawa jahar      HANNU Mousa Ubandawaki Mataimakin Daraktan Labarai da wallafe-wallafe NAHCON, Abuja

Gwamnoni Sun Roki Buhari A Ci Gaba Da Amfani Da Tsoffin Kudi

Image
  Gwamnonin Jam’iyyar APC sun bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa baki a ci gaba da amfani da tsofaffi da kuma sabbin takardun kudi. Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ne ya bayyana hakan bayan ganawar sirri da suka yi da shugaban kasa a Abuja. Ya ce yayin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya karbi sama da Naira tiriliyan biyu na tsofaffin kudi, amma iya Naira biliyan 300 kacal ya iya bugawa wanda a cewarsa hakan ba zai wadatar da mutane ba. El-Rufai, wanda ya samu rakiyar takwaransa na Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce kamata ya yi CBN ya buga akalla rabin abin da suka tara. Ya ce gwamnonin jam’iyyar sun shaida wa shugaban kasa wawahalar da talakawa ke sha, da asar kayayyaki da ’yan kasuwa ke yi saboda rashin samun masu sayen kayansu. Ya ba da misali da yadda masu sayar da tumatur suka je Legas da kayansu amma suka lalace saboda mutane ba su da kudin saye. El-Rufai ya ce gwamnonin sun roki shugaban kasa da ya sake duba halin da ake ciki. Ya kara da cewar shugaban gama

Babu Kasar Da Ta Taba Sauya Kudi A Lokacin Zabe Sai Najeriya —El-Rufai

Image
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewar babu matsala a sauya fasalin takardun kudi, amma duk duniya babu kasar da ta taba sauyawa a lokacin zabe sai Najeriya. El-Rufai ya yi zargin akwai gwamnan da shi kadai ya karbi sabbin kudi har na Naira miliyan 500 a kasar nan Ya bayyana hakan ne cikin wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC, inda ya ce an yi tsarin ne don masu kudi, amma da yawansu tsarin ba zai shafe su ba; zai kare ne a kan talaka. “Babu laifi game da sauya kudi, kowace kasa na yi amma babu inda aka taba sauya kudi a lokacin zabe kuma aka bayar da wa’adi kadan, a ina aka taba yin haka a duniya? “’Yan siyasa da manyan ’yan kasuwa da aka yi tsarin dominsu, suna da hanyoyin da za su samu kudin ba tare da sun wahala ba, wasu daga cikinsu su ke juya bankunan, amma wane hali talakawa da kananan ’yan kasuwa za su shiga? “Duka gwamnonin APC sun gana a kan wannan matsalar, mun ga yadda mutane ke shan wahala, mun goyi bayan sauya kudi amma wa’adin da aka ware

Babu Wanda Nake Tsoro —El-Rufai Ga ‘’Yan Fadar Buhari’

Image
  Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya kalubalancin ’yan fadar shugaban kasa da yake zargi da zagon kasa ga takarar Bola Tinubu a zaben shugaban kasa da ke tafe.  Tun a ranar Laraba El-Rufai ya fara tayar da kura da zargin cewa akwai jami’an Fadar Shugaban Kasa da ke neman yi wa takarar Tinubu kafar ungulu. A wata hirarsa da Sashen BBC na Hausa, an ji shi yana cewa, “Na rantse babu mahalukin da nake tsoro a duk fadin kasar nan. “Don ana ganin girmn mutum ba soronsa ake ji ba; Amma idan muna girmama mutum, amma yana nuna shi ba babba ba ne, to wallahi za mu ake shi.” Ana ganin kalaman nasa kari ne a kan zargin wadanda yake zargi a fadar shugaban kasa, da ya cesuna neman tadiye inubu. BBC sun fitar da somin-tabin hirar ce kafin a fitar da shi gaba dayansa. A ranar Laraba, a waya hira da shirin Sunrise Daily na gidan alabijin na Channels ne El-Rufai ya yi zargin akwai magoya baan wadanda suka nemi takarar shugaban kasa a APC wanda Tibubu a lashe da ke fakewa da Shugaba Buhari domin cimma man

Cibiyar Koyar Da Ayyukan Hajji Ta NAHCON, Za Ta Fara Gudanar Da Harkokin Koyarwa

Image
Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Cibiyar Aikin Hajji  za ta fara gudanar da harkokin karatun ta na shekarar 2023/24 a ranar Talata 7 ga Fabrairu, 2023 rukunin farko na dalibai. Taron budewar wanda  Ministan ilimi, Adamu Adamu zai kaddamar da da shi, yayin da ministan babban birnin tarayya, Muhammad Musa Bello, zai kasance babban bako na musamman. A sanarwar da mataimakin daraktan harkokin yada labarai da hulda da jama’a na hukumar NAHCON, Mousa Ubandawaki, and yace Cibiyar za ta fara ne da shirin sati 4 na bayar da takardar shaida ga dalibanta na "Tsarin Gudanar da Ayyukan Hajji da Umrah". Shugaban hukumar, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya bayyana farin cikinsa da kafuwar wannan cibiya. “Muna gaggauta taya dukkan masu ruwa da tsakinmu murnar wannan nasarar da muka samu. Ba za mu iya yin da'awar cewa mun cimma wannan kawai ba. Don haka, mun fahimci gudummawar da hukumar da ta gabata ta bayar. Don haka ina kira ga masu ruwa da tsaki da su hada kai a matsay

Daga yanzu Bankuna Zasu Rinka Bayar da Sababbin Kudi A Kan Kanta

Image
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce daga yanzu Bankuna Zasu rinka bawa mutane kudi a kan Kanta, sabanin umarnin da ya bayar na baya kan cewa sai a Na'urar ATM kadai zasu sanya kudaden domin masu hulda dasu su cira. Hadimin Shugaban kan harkokin kafafen yada labarai na yanar Gizo, Bashir Ahmed ne ya wallafa wannan labari a shafinsa na Instagram  Za a iya tunawa cewa A ranar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya Ya gana da Shugaba Buhari ne ya fitar da sabuwar sanarwar da ta ce ko bayan Karewar Wa'adin kashe tsofaffin kudi, Bankuna Zasu ci gaba da karbarsu domin mikawa Babban Bankin 

Kotun Koli ta sake tabbatar da Hajiya Laila Buhari a matsayin 'Yar Takarar Sanatan PDP Ta Kano Tsakiya

Image
A ranar Alhamis ne kotun koli ta sake tabbatar da Hajiya Laila Buhari a matsayin ‘yar takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar PDP. SOLACEBASE ta ruwaito cewa a baya kotun daukaka kara ta tabbatar da Laila Buhari ta soke zaben Danburan Nuhu. Kotun kolin da ta yanke hukuncin da mai shari’a Muhammad Lawal Garba ya karanta, ta yi watsi da dukkan dalilan daukaka kara ta Danburam Nuhu. Jastis Garba na tare da Jastis Kudirat Kekere Ekun, da Jastis Saulawa da Jastis Ibrahim Jauro, da Jastis Emmanuel Agim Cikakken labarin zai zo muku nan gaba 

Atiku Abubakar Zai Kaddamar Da Makarantar Haddar Alkur'ani A Kano

Image
  Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, zai kaddamar da makarantar sakandaren kwana ta haddar Al-Kur’ani mai dalibai 500 a Jihar Kano. Atiku zai bude wannan makarantar haddar Al-Kur’ani ce a unguwar Gunduwawa da ke Karamar Hukumar Gezawa, a yayin ziyarar yakin neman zabensa a Jihar Kano, wadda za a gudanar ranar 9 ga watan Fabrairun da muke ciki. Wannan makarantar haddar Al-Kur’ani “Na da wurin kwanan dalibai mata 250, maza 250, kuma za su rika haddace Al-Kur’ani a cikin wata bakwai, kafin su tafi makarnatun gaba da sakandare,” inji kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku a Jihar Kano, Sule Ya’u Sule. Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau ne dai ya gina makarantar ta haddar Al-Kur’ani mai daukar dalibai 500 a matsayin aikinsa na raya alu’m Sule Ya’u Sule ya sanara ranar Laraba cewa, Atiku zai kaddamar da makarantar ce a ranar taron yakin neman zabensa, ko kuma washegari. A cewarsa, “Wazirin Adamawa zai zo Kano ranar 9 ga Fabrairu, don haka j

Hajj2023: Hukumar Alhazai Ta Kano Za Ta Fara Gudanar Da Bitar Alhazai Ga Maniyyata Aikin Hajin bana

Image
Sakataren Hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Muhammad Abba Danbatta, shi ne ya bayar da wannan umarni ga dukkan Shugabanni da Malaman Bita, na Bitar mako-mako dake fadin jahar Kano  A sanarwar da Mataimakin Sakataren kwamitin malaman Bitar na Jaha, Malam Dahiru Kabiru Guringawa ya fitar, ta ce akwai shugaban kwamitin Bitar, Sheikh Haroon Muhd Sani Ibn Sina yace, za a fara gudanar da bitar ce daga ranar Asabar 4 ga watan Fabarairu na 2023 da karfe 10 na safe  Za a fara gudanar da Bitar ce a dukkanin Cibiyoyin bitar dake fadin jahar Kano.  A saboda sai sanarwar ta yi kira ga dukkanin Jami'an Alhazai na kananan hukumomi dasu tabbata sun sanarwa da dukkanin maniyyatansu don su halarta 

Akwai Makiyan Tinubu A Fadar Shugaban Kasa – El-Rufa’i

Image
  Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya yi zargin cewa akwai makiyan dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu a Fadar Shugaban da suke kokarin ganin sun kai shi kasa. Ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, a cikin shirinsu na  Sunrise Daily  da safiyar Laraba. El-Rufa’i ya ce mutanen, wadanda bai bayyana sunansu ba, sun fusata ne tun lokacin da aka kayar da dan takararsu a zaben fid-da gwani na APC. Ya kuma ce mutanen na fakewa da bukatar ganin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi abin da ya dace. Ya ce, “Na tabbatar a cikin Fadar Shugaban Kasa akwai masu son mu fadi zaben nan, saboda bukatarsu ba ta biya ba, an kayar da dan takararsu a zaben fid-da gwani. “Wadannan mutanen na kokarin fakewa da bukatar Buhari ya yi abin da ya dace. Zan bayar da misalai biyu; wannan batun na biyan tallafin mai wanda ya ke sa Najeriya ta kashe makudan kudade abu ne da dukkanmu mun dade da amincewa a cire shi. “Sai da ma na tattauna da Shugaban Kasa a kan