NAHCON Ta Bayyana Manyan Nasarori Da Ta Cimma a Ayyukan Hajji a Zamanin Gwamnatin Renewed Hope

Shugaban Hukumar Kula da Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana muhimman nasarorin da hukumar ta samu a karkashin gwamnatin Renewed Hope ta shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, tare da tabbatar da cewa jin daɗin maniyyata na ci gaba da kasancewa a sahun gaba.

Farfesa Usman ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma a Katsina, inda ya yi cikakken bayani kan gyare-gyare da matakan da aka ɗauka wajen inganta gudanar da aikin Hajji a Najeriya.

A cewarsa, duk da ƙalubalen tattalin arziki da ake fuskanta, hukumar tare da goyon bayan shugaban ƙasa, ta aiwatar da muhimman matakai da suka tabbatar da nasarar aikin Hajjin 2024 tare da kawo sauƙi ga maniyyatan Najeriya.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa shugaban ƙasa ya amince da naira biliyan 90 domin rage tasirin hauhawar darajar kuɗin waje a kuɗaɗen aikin Hajjin 2024, da kuma ƙarin naira biliyan 24 domin biyan bashin da ya rage daga kamfanonin jiragen sama na 2023. Wannan mataki, a cewarsa, ya ceci kamfanonin jiragen sama na cikin gida daga rugujewa kuma ya tabbatar da gudanar da jigilar maniyyata cikin nasara.

Haka kuma, ya bayyana cewa shugaban ƙasa ya umurci dukkan kamfanonin jiragen sama da ke da hannu a aikin Hajji da su karɓi kuɗi a naira, wanda hakan ya kare maniyyata daga ƙarin radadin hauhawar darajar kuɗin waje.

Dangane da gyare-gyare, Farfesa Usman ya ce hukumar ta dakatar da tsarin katin kuɗin (credit card) na babban bankin ƙasa (CBN) wajen bayar da kuɗin tafiya (BTA), wanda ya jefa maniyyata da dama cikin wahala, sannan aka faɗaɗa tsarin Hajj Saving Scheme domin baiwa masu niyyar zuwa Hajji damar tara kuɗaɗensu a hankali.

A kan gaskiya da nuna riƙon amana, hukumar ta mayar da naira biliyan 5.3 ga hukumomin kula da alhazai na jihohi bisa sabis ɗin da ba a samu ba a lokacin Hajjin 2023.

Game da jin daɗi da tsare-tsare, shugaban hukumar ya bayyana cewa NAHCON ta samu nasarar samar da VIP Tent ‘A+’, ta daidaita kwangiloli daidai da adadin maniyyata, tare da tabbatar da cewa kusan kashi 98% na magunguna an samar da su, yayin da aka tura jami’an lafiya cikakke zuwa ƙasar Saudiyya.

Farfesa Usman ya jaddada cewa maniyyata na Najeriya sun sami gagarumar ragi a kuɗaɗen da suka kashe a wannan shekarar. Ya ce akwai ragin Riyal 720 a sabis na Mashair, Riyal 200 a masaukin Madina, Riyal 303 a sufuri, da kuma rage farashin jiragen sama a dukkan yankuna.
“Wadannan nasarorin,” in ji shi, “na nuna hangen nesa na shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma goyon bayan shugabanni kamar Gwamna Dikko Umar Radda. Tare da ci gaba da haɗin kai, NAHCON za ta ci gaba da inganta waɗannan nasarori tare da tabbatar da ƙarin jin daɗin maniyyata.”

Masu lura da jawabin sun ce wannan rahoto na shugaban NAHCON ya tabbatar da jajircewar hukumar wajen gudanar da aikin Hajji bisa ƙa’idojin duniya tare da rage wa maniyyatan Najeriya nauyin kuɗi.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki