Posts

Showing posts from December, 2022

Sojojin haya sun kama jirgi maƙare da fetur na sata a Neja-Delta

Image
Kamfanonin tsaro biyu da Najeriya ta bai wa kwangilar tsaron bututan man fetur sun kama jiragen ruwa da mota maƙare da man da hukumomi suka ce na sata ne a yankin Neja-Delta da ke kudancin ƙasar. Wata sanarwa da kamfanin mai na Najeriya, NNPC Limited, ya fitar a yau Asabar ta tabbatar mutum huɗu aka kama yayin samamen. Kamfanin ya samu rahoton sirri game da ayyukan mutanen tun a ranar 22 ga watan Disamba. Dakarun tsaro sun isa wurin kuma suka tarar da su suna jigilar man ta ɓarauniyar hanya tare da tace gas a wata matata da ke Agge. Tuni hukumomi suka ƙona jirgin da kayan da yake ɗauke da shi. NNPC Copyright: NNPC A tsakiyar shekarar 2022 ne gwamnatin Najeriya ta ƙulla yarjejeniya da kamfanonin Tantita Security Services da zimmar daƙile ayyukan ɓarayi da kuma masu fasa bututan mai a yankin na Neja-Delta. Satar mai na jawo wa Najeriya asarar biliyoyin kuɗin shiga kuma ya sa ba ta iya haƙowa da fitar da ganga miliyan 1.8 da ƙungiyar Opec ta masu arzikin man fetur ta ƙayyade mata a kowace

Bidiyo: Gasar sukuwar Dawaki ta Premier ta Birnin Kebbi. Rana ta daya zagaye na 2

Image
 

Bidiyo : Gasar sukuwar Dawaki ta Premier Birnin Kebbi. Rana ta daya zagaye na 3

Image
 

Fitaccen dan kwallon duniya, Pele ya mutu

Image
  Fitaccen ɗan ƙwallon nan na duniya ɗan ƙsar Brazil, Pele ya rasu yana da shekara 82. Pele ya rasu ne a ranar Alhamis 29 ga watan Disamban 2022 bayan ya sha fama da rashin lafiya. A kwanakin baya an yi ta yaɗa labarin ƙarya na rasuwarsa. Ya rasu ne sakamakon cutar kansar ƙaba da kuma cutar ƙoda Ana ganin Pele shi ne ɗan ƙwallon da ba a taɓa samun irin sa ba a duniya, kuma sau uku yana cin gasar kofin duniya wa ƙasarsa Brazil. Ya ci kofin duniya a shekarun 1958 da 1962 da kuma 1970. A shekarar 2000 ne kuma hukumar ƙwallon ƙafar duniya FIFA, ta ayyana shi a matsayin ɗan ƙwallon ƙarni. Shi ne ɗan ƙwallon da ya kafa tarihin zura ƙwallaye 1,281 a raga a cikin wasanni 1,363 cikin shekara 21 da ya yi yana buga tamaula. Cikin waɗannan har da ƙwallo 77 da ya ci wa ƙasarsa cikin wasanni 92 da ya buga wa Brazil ɗin. An yi wa Pele tiyata a kan yanke masa kansa a hanjinsa a watan Satumban 2021 a Asibitin Albert Einstein da ke Sao Paulo. An sake kwantar da shi a asibiti a watan Nuwamban 2022. Ƴarsa

Buhari Zai Sayo Motocin Sulke 400 Don Tsaron Su Abuja

Image
Shugaba Buhari ya amince da sayo motocin sulke guda 400 don amfani da su wajen tabbatar da tsaro a babban birnin tarayya da jihohin Nasarawa da kuma Neja. Sabon Kwamandan Rundunar Tsar Birgediya, Manjo-Janar Mohammed Usman ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a jawabin godiyarsa a bikin nada masa anininsa bayan karin girma da ya samu. Shugaban kasa tare da Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Faruk Yahaya da uwargidan kwamandan, Dokta Rekiya Usman, ne suka nada masa aninin. Jim kadan bayan kammala bikin a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, shugaban kasa ya bayyana shi a matsayin fitaccen jami’in da yake yi wa kasa hidima. Ya yaba wa Janar Usman bisa jajircewarsa da rikon amana da hakuri da kuma kwazo. Buhari, a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Garba Shehu ya fitar, ya yaba wa iyalan kwamandan bisa hakurin da suka yi na jure kalubalen da ya fuskanta wajen gudanar da aikinsa. A nasa jawabin, Manjo-Janar Usman, ya gode wa shugaban kasa bisa irin gagarumin goyon bayan da ya bai wa Rundunar

Ka da ka shekara goma da mata daya - Sheikh Daurawa

Image
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce shawarci maza cewa ka da su kuskura su shekara 10 da mace daya matukar suna da burin kara aure. Sheikh Daurawa, ya bayyana haka ne a zantawarsa da gidan rediyon Freedom da ke Kano haka ne, inda ya ce idan namiji ya kai wannan shekarun da mace daya, lokaci ya kure masa. “Kada ka wuce shekara 10 idan za ka kara aure ba ka kara ba. Idan ka wuce shekara 10 akalla kana da ‘ya ‘yar shekara takwas ko tara. “Da zarar ’yarka ta kai shekara 15 ba ka kara aure ba, to wacce zaka auro da wuya ta wuce shekara 20. Za ka ga tsakaninsu da ’yarka bai wuce ’yan tazarar shekaru ba. “Saboda haka matarka ta samu abokiyar rigima. Akwai wadda za ta iya tura ’yarta ta samu amarya su rika rigima ko ta yi ta dukan amaryar saboda ta fi karfinta. “…Saboda haka wanda zai yi aure ya shirya da wuri, kuma kada duk dadin miyar mace ka ce ba za ka kara aure ba,” in ji Shehun malamin. Karin aure ko yi wa uwar gida kishiya na tayar da kura

Gasar sukuwar Dawaki ta Birnin Kebbi ta 2022. Rana ta daya zagaye na biyu

Image

Almajiran Abduljabbar Kabara sun ce zasu daukaka kara

Image
  Almajiran Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da Kotun Musulunci ta yanke wa hukuncin rataya kan laifin batanci ga Manzon Allah (SAW) suna shirin daukaka kara. Almajiran fitaccen malamin mazaunin Kano, karkashin inuwar A’shabul Kahfi Warraqeem, Reshen Jihar Bauchi, sun yi zargin siyasa a hukuncin da aka yanke masa, saboda a cewarsu, malamnin nasu ya caccaki Gwamnan Jihar Kano, kan zargin almundahana. “Ba mu gamsu da hukuncin ba saboda muna zargin akwai hannun Gwamnan Jihar Kano da wasu malamai da suka dade suna zaman doya da manja da shi (Abduljabbar), wadanda suka yi masa kagen yin batanci domin su kawar da shi daga doron kasa ta hanyar amfani da karfin kotu,” in ji mai magana da yawunsu, Abdullahi Musa a Bauchi. Ya shaida wa manema labarai cewa, “Zargin batancin ba komai ba ne illa neman goga masa kashin kaji daga magauta, ciki har da Ganduje da wasu malamai da ke ganin daukakar da Abduljabbar ke samu a matsayin baraza a gare su.“Shi ya sa suka jefe shi da yin batanci domin su ja masa

Na Daina Jin Dadin Rayuwa, Burina In Cika Da Imani Kawai – Aminu Dantata

Image
  Hamshakin  attajirin nan na Jihar Kano, Aminu Alhassan Dantata, ya ce daina jin dadin rayuwa, kuma ba shi da wani buri sama da cikawa da imani. Attajirin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Mataimakin Dan Takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC, Kashim Shettima. Ya ce ton tasowarsa, ya samu damar haduwa da mutane da dama, kuma ya kulla abota da jama’a a duka jihohin kasar nan. Sai dai, ya ce a halin yanzu da walan gaske ya samu mutum 10 daga cikin abokan nasa da ke raye. “Na karade jihohin Nijeriya, kuma na yi harkoki da jama’a a daukacin jihohin, na yi abokai da dama sai dai abin bakin cikin shi ne, da wuya in ambato 10 daga ciki wadanda ke raye. “Gaskiya a yadda nake yanzu, lokaci kawai nake jira. Ina fata in bar wannan duniya da imani. “Ina fata ban saba wa kowa ba a rayuwa, idan kuwa hakan ta faru, ina fata za a yi mini afuwa, ni ma na yafe wa duk wani da ya saba mini. “A zuri’armu n i kadai na rage, inda nake rayuwa a tsakanin jikoki,” inji Dantata. Daga nan, ya yaba

’Yan Bindiga Sun Sace Manoma 100, Sun Sanya Haraji A Neja

Image
  ’Yan bindiga sun kashe mutum hudu tare da yin garkuwa da mutum fiye da 100 ciki har dakanan yara a Kananan Hukumomin Rafi da Mashegu na Jihar Neja. Daga cikin wadanda bata-garin suka kashe har da basaraken gargajiya da ’yan banga biyu da wani mutum daya a Karamar Hukumar Mashegu. Maharan sun kuma sanya harajin Naira miliyan uku-uku domin dakatar da garkuwa da mutane a yankunan kananan hukumomin Rafi da Shiroro inda suka yi awon gaba da mutum 61. Al’ummar yankunan Rafi da ’yan bindiga suka kai wa hari sun shiga yin kaura zuwa wasu wurare domin samun aminci. Rahotanni sun bayyana cewa a mako uku da suka gabata mahara sun far wa kauyuka 14 a kananan hukumomin, inda suka sace yawancin mutanen a gonakin wake,  marasa da dawa. Wani mazaunin yankin ya ce sun daina zuwa gonakinsu saboda tsoron kada a yi garkuwa da su, a yayin da ’yan bindiga ke sace masu amfanin gona. 'Yan Bindiga Garkuwa noma

Hisbah Ta Rufe Wuraren Shan Giya Sama Da 100 A Zariya

Image
Wata kungiyar addinin Musulunci mai zaman kanta mai suna Hisbah, ta jagorance garkame wuraren shan giya sama da 100 a Karamar Hukumar Sabon Gari da ke Jihar Kaduna. Dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Sabon Gari, Garba Datti Babawo ne ya tabbatar da hakan, yayin gabatar da hsaidar kammala karbar horo ga ’yan kungiyar su 750 da ya gudana a hedkwatar Karamar Hukumar ta Sabon Gari. Dan majalisar ya ce tun da Karamar Hukumar take ba ta taba samun sa’ida daga ayyukan badala ba sama da lokacin da aka kafa rundunar ta Hisbah. Daga nan sai Babawo ya ja kunnen dakarun da su tabbatar suna bin dokokin dokoki yayin gudanar da ayyukansu. Shi ma da yake nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar ta Sabon Gari, Injiniya Mohammed Usman, ya jaddada kudurin gwamnatinsa na kakkabe yankin daga ayyukan masha’a, ta yadda za a sami yanayin kasuwanci mai kyau tare da bunkasa zaman lafiya a tsakanin al’umma. Tun da farko sai da Kwamandan rundunar a yankin, Abubakar Auwal ya ce dakarun su 750 su