Wasa Farin Girki, Shekarar 2025 Za Ta Kasance Mafi Alkhairi Ga Kanawa Karkashin Shugabancin Gwamna Abba Kabir Yusuf - Shugabar ARTV
Shugabar gidan talabijin na ARTV Kano Hajiya Hauwa Isah Ibrahim ta taya al’ummar Kano da jagoran Kwankwasiyya na duniya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo murnar shiga sabuwar shekara ta 2025.
Hajiya Hauwa ta kuma taya dukkanin ma’aikatanta na ARTV murnar shiga sabuwar shekarar tare da kira a garesu su kara jajircewa wajen aikinsu ,tana Mai basu tabbacin cigaba da basu hadin kan da ya dace .
A saƙonta, Hajiya Hauwa ta ce ta ɗaura gabarar sake bunƙasa harkokin tashar talabijin ɗin mallakin jihar Kano fiye da yadda ta yi cikin ƙanƙanin lokaci a shekarar 2024.
Shugabar ARTV din ,tayi fatan cewa shekarar 2025 zata zamo mafi Alkairi ga mutanan Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf.
Tace idan akayi la’akari da kasafin kudin da gwamna Yusuf ya sanyawa hannu da Karin da aka samu daga sama da naira biliyan 549 zuwa sama da naira biliyan 719 ,babu shakka gwamna Yusuf ya shirya kawo karshen matsalolin da ake samu na wahalhalu a Kano musamman taadar rayuwa da yunwa da Kuma talauci.
Ta jinjinawa gwamnan abisa yadda baya wasa da bangaren Ilimi da koshin lafiyar al’umar Kano,da kuma yadda yake tafiyar da tsare tsaren da ya dauko tun a yakin neman zabensa .
Hajiya Hauwa ta kuma bayyana yadda Gwamnatin Kano ta É—auki harkar yaÉ—a labarai da muhimmanci tare da tafiya daidai da zamani.
Ta yiwa al’ummar Kano albishir da samun sabbin shirye-shirye na musamman a tashar cikin wannan sabuwar shekara.
Ta nemi al’uma suci gaba da yiwa gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf fatan Alkairi da adu’a.