Posts

EFCC Ta Kwace Fasfon Sadiya Da Betta Edu

Image
Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ta kwace fasfo din tsohuwar Ministar aJin-kai, Betta Edu da magabaciyarta, Sadiya Umar-Farouq, kan binciken badakalar da ake yi a ma’aikatar. Wata majiya mai tushe daga EFCC ta ce an kwace fasfo din Edu da da Sadi ya  ne domin hana su fita daga Najeriya yayin da ake ci gaba da binciken. “Hukumar ta kwace fasfo din tsofaffin ministocin biyu, Sadiya Umar-Farouq da Betta Edu. “Mun kuma kwace fasfo din Halima Shehu har sai an kammala bincike. Hukumar ba ta son yin kasadar ganin ko daya daga cikinsu ya fice daga Najeriya alhalin ana bincike a kan su,” in ji majiyar. Dangane da binciken Edu da Sadiya Umar-Farouq, EFCC ta gayyaci shugabannin bankunan Zenith, Providus da Jaiz ofishinta a ranar Talata. Ita ma Halima Shehu, wacce aka dakatar daga hukumar kula da harkokin zuba jari ta kasa, EFCC na bincike a kan ta. Aminiya  ta ruwaito cewa Edu ta isa hedikwatar EFCC da misalin karfe 10 na safiyar ranar Talata domin amsa tambayoy

Labari Da Dumiduminsa: Shugaba Bola Ahmed Tinubu Ya Dakatar Da Ministar Harkokin Walwala Betta Edu

Image
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya dakatar da ministar jin ƙai, Betta Edu nan take. Kakakin shugaban Najeriyar, Ajuri Ngelale ne ya sanar da matakin dakatar da ministar cikin wata sanarwa da aka fitar a yau. Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin ne domin ba da dama ga hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gudanar da bincike a kanta. Tun farko al'ummar Najeriya sun yi ta matsa lamba inda suke kiraye-kiraye gwamnati ta dakatar da ita daga mukaminta domin a gudanar da cikakken bincike a kanta game da zarge-zargen da ake mata. Ana zargin ta da bayar da umarnin tura kuɗi kimanin naira miliyan 585 zuwa asusun bankin wata mata. (BBC HAUSA)

Najeriya da Saudi Arabiya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan aikin hajjin 2024

Image
A yau 7 ga watan Junairu 2024 ne Najeriya karkashin hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta amince da gudanar da aikin Hajjin bana ta hanyar rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna ta shekarar 2024 (1445AH) da ma'aikatar aikin hajji da umrah ta kasar Saudiyya. A sanarwar da mataimakiyar daraktar harkokin hulda da jama'a da dab'i ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, tace bikin rattaba hannun da aka yi a Jeddah ya samu halartar manyan wakilai daga Najeriya karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar da Malam Jalal Ahmad Arabi, mai rikon mukamin Shugabancin NAHCON.  Tawagar kasar Saudia ta samu jagorancin Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, Dr. Taufiq Al-Rabiah.     Kafin rattaba hannu kan yarjejeniyar, Ministocin biyu sun yi wata ‘yar gajeruwar tattaunawa inda Najeriya ta bukaci a kawo karshen matsalar karancin tantuna a Mina tare da neman karin wasu sharuddan da suka dace ga dilolin Najeriya a lokacin jigilar ka

Labari Da Dumiduminsa: Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kamfanonin Jiragen Da Zasu Yi Jigilar Maniyyata Hajin 2024

Image
Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da wasu manyan kamfanonin jiragen sama guda uku da za su yi jigilar maniyyata aikin hajjin 2024, wadanda suka hada da Air Peace., FlyNas da Max Air.  Har ila yau, an amince da wasu kamfanoni uku na jigilar kayayyaki da za su yi jigilar kayan alhazai WaÉ—annan su ne Cargo Zeal Technologies Ltd, Nahco Aviance da Qualla Investment Limited.   A sanarwar da mataimakiyar daraktar harkokin hulda da jama'a da dab'i ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, tace Yarjejeniyar ta karfafa yunÆ™urin gwamnati na tabbatar da ingantaccen aikin hajji ga maniyyatan Najeriya.  Don haka, a lokaci guda gwamnatin tarayya ta amince da rabon maniyyata daga jahohi daban-daban ga kowane kamfanonin jiragen sama da aka amince da su kamar haka:   i.Air Peace zai yi jigilar maniyyata daga: Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, FCT, Imo, Kwara, Ondo da Ribas. ii.Fl

Labari Da Dumiduminsa: Hukumar NAHCON Ta Kara Wa'adin Biyan Kudin Aikin Hajji Bana

Image
Dangane da koke-koken da malaman addini, hukumomin jin dadin alhazai Jiha, Gwamnonin Jihohi da sauran masu ruwa da tsaki suka gabatar dangane da rufe rajistar aikin hajjin 2024, Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta yi farin cikin sanar da amincewar gwamnatin tarayya. don tsawaita wa'adin.  A sanarwar da mataimakiyar daraktar harkokin yada labarai da dab'i ta Hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, tace daga yanzu an mayar ranar wa'adin zuwa  Janairu 31, 2024, yana ba da Æ™arin dama ga daidaikun mutane su samu damar zuwa aikin Hajji      Bukatar neman tsawaita lokacin daga al'ummomin addinai daban-daban na nuna muhimmancin tabbatar da yadda dimbin masu kishin addinin ke da sha'awar shiga aikin Hajji.   Don haka, NAHCON na da yakinin cewa kafin cikar wa’adin, tare da tallafin Hukumomin Alhazai na Jahohi ta zasu fitar da jimillar kudin aikin Hajjin 2024.  Don haka tsawaita wa’adin ya samar da kofa ga sabbin masu rajista don yin hakan kuma a karshen

Ayyukan Da Zan Yi Wa Al'umar Mazabata Cikin Shekarar 2024 - Abdulmumin Jibrin Kofa

Image
Bayan rantsar da ni a matsayin É—an Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaÉ“ar Kiru/Bebeji, na yi hoÉ“É“asar ganin na kawo ayyukan raya Æ™asa da ci gaban yankina. Kamar yadda buÆ™atun ainihin aikin da aka zaÉ“e ni don shi suke, na duÆ™ufa ba dare ba rana wajen yin bincike domin gabatar da Æ™udurorin da zan gabatar a zauren majalisa a ’yan watanni masu zuwa, waÉ—anda za su amfani ’yan mazaÉ“ata da ma Æ™asa baki É—aya. A sakamakon haka, na tattauna da shugabannin kwamitoci daban-daban a Majalisa, na kuma rubuta wasiÆ™un neman ayyuka masu yawa da za aiwatar a mazaÉ“ata a 2024, Æ™ari a kan wasu da zan yi da aljuhuna, kamar yadda na saba yi a baya. Yana da muhimmanci a fahimci cewa idan ban da aikin tituna (waÉ—anda na saka a kasafin kudin 2016, amma ba a aiwatar da su ba), na kawo ayyukan raya kasa masu tarin yawa a mazaÉ“ata, na samar da gurabun ayyukan yi ga mutanen mazaÉ“ata a hukumomi da ma’aikatun gwamnati masu yawa da kuma wasu hukumomin tsaro, duk waÉ—annan za a iya zuwa a tantance su.  Duka w

Hajj 2024 : Hukumar Alhazai Ta Bauchi Ta Siyar Da Kujerun Haji Guda 1700- Imam Abdurrahman

Image
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi ta sayar da kimanin guraban kujerun aikin hajji akalla *1700* daga cikin guda *3364* da Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta ware wa Jihar Bauchi. A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Muhammad Sani Yunusa ya sanyawa hannu, yace Sakataren zartarwa na hukumar jindadin alhazan ta jihar Bauchi Imam Abdurrahman Ibrahim Idris,shi ne bayyana hakan yayin  zantawarsa da manema labarai kan shirye shiryen aikin hajji daga Bauchi, inda yace wayarda alumma kan sabbin tsare tsaren aikin hajjin na shekarar 2024 daya gudana a jihar Bauchi yayi tasiri kwarai da gaske. Imam Abdurrahman ya alakanta nasarar gudanar da atisayen wayarda kan alummar ne da irin gudumawa da goyon bayan da tsarin ya samu daga sarakunan mu na jihar Bauchi da shugabannin kananan hukumomi da limamai da sauran masu ruwa da tsaki a aikin Hajji. Ya kara da cewa sabbin tsare-tsare na Saudiyya kan ayyukan Hajji na shekarar 2024 ne suka tilastawa kasashe fara  s

Shugaban Majalisar Dokoki Ta Katsina Ya Raba Tallafin Naira Miliyan 35

Image
Kakakin Majalissar Dokoki ta Jihar Katsina, Nasir Yahaya, ya bayar da tallafin Naira Million Talatin da HuÉ—u da Dubu ÆŠari Tara da Hamsin. (34,950,000) ga Mutum Dubu Ukku (3000) a filin wasan Ƙwallon Kafa dake Daura Hadimin tsohon Shugaban Najeriya, Buhari Sallau, ya rawaito a shafinsa na Facebook cewa, an bayar da Tallafin ga Marayu, Limamai, Zawarawa, Masu Ƙananan Sana'oi, Exco, Mata, Matasa, Students, yan Media, Dagattai, MabuÆ™ata, yan siyasa, Ƙungiyar Teloli, Ƙungiyar Masu Shayi da Masu chajin waya, da sauran su. Inda ko wanne daga cikinsu zai amfana da Tallafin, Naira Dubu Goma (10,000) Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda PhD, yayi Jin-Jina gami da fatan Alkhairi ga Kakakin Majalissar akan wannan abin Alkhairi da yayi, sannan yayi roÆ™o gami da Jan hankali ga wanda suka amfana da wannan Tallafin da suyi amfani dashi ta hanyar daya dace, domin su bunÆ™asa Kasuwar su.  Haka kuma Mataimakin Shugaban Jam'iyyar APC na Jihar, Alh. Bala Abu Musawa, ya taya mutanen D

Shugaban NAHCON Ya Ziyarci Ofishin Jakadancin Saudiyya na Abuja.

Image
Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya wato NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi, ya kai ziyarar ban-girma zuwa ofishin Huldar Jakadanci na Saudiyya inda ya gana da Jakadan Saudiyya dake Abuja, Ambasada Faisal Ibrahim Al-Ghamidy, a ranar Laraba   A sanarwar da Hukumar ta fitar ta ce, Shugaban ya kai ziyarar ce da nufin bunkasa dangantaka da habakar da hadin-gwiwa tsakanin bangarorin biyu.   Malam Arabi ya jaddada jin dadinsa ganin yadda Jakadan Kasar Saudiyya Ambassada Faisal ke bada cikakken goyon-baya ga Hukumar da tareraya irinta Huldar Jakadanci karkashin  Ofishin Jakadancin Saudiyyar. Sanarwar tace ziyarar, ta bayyana karara yadda dadaddiyar alaqa ta jituwa ke tsakanin NAHCON da Ofishin Jakadancin Saudiyyar, abinda ke nuni da fahimtar-juna da hadin kai dake wanzuwa a tsakanin Kasashen biyu. A Yayin ganawar, bangarorin biyu  sun zanta batutuwa masu ma’anar gaske, abunda ke tabbatar da muhimmancin tarayyarsu wajen kara inganta gudanar da Al-amurran Aikin Hajji A Najeriya Sh

Kotun Koli Ta Tsayar Da Ranar Da Za Ta Saurari Karar Zaben Gwamnan Kano

Image
Kotun koli ta sanya ranar Alhamis 21 ga watan Disamba domin cigaba da sauraron karar zaben gwamnan Kano tsakanin gwamna Abba Kabiru Yusuf na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP da Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC.  KANO FOCUS ta rawaito cewa a cikin sanarwar da magatakardar kotun daukaka kara ta aikewa lauyoyin bangarorin biyu, kotun za ta saurari karar da NNPP ta shigar da kararrakin wasu jam’iyyu.  Gwamna Yusuf na kalubalantar hukuncin da wasu bangarori uku na kotun daukaka kara suka yanke wanda ya soke nasarar da ya samu tare da tabbatar da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke. Kotun sauraron kararrakin zabe karkashin jagorancin mai shari’a Osedebay ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano a watan Maris.  Kotun daukaka kara ta yi watsi da karar da Gwamna Yusuf ya shigar bisa matsayinsa na zama mamba a jam’iyyarsa sannan ta zargi kotun da yin watsi da hujjar da ta yanke. Kotun ta kori Gw