Search This Blog

Monday, 26 December 2022

Shugabannin hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) sun kai ziyarar ta'aziyya ga Mangal








LABARI CIKIN HOTUNA

Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, kwamishinan kudi, Alhaji Nura Hassan Yakasai da kwamishinonin ayyuka da wasu ma’aikatan gudanarwa, sun kai ziyarar ta’aziyya ga Shugaban Kamfanin Mangal Group (Max Air) Alhaji Dahiru Barau Mangal a Katsina, bisa rasuwar marigayi Alhaji Bashiru Mangal

MAI MARTABA SARKIN KANO ALHAJI AMINU ADO BAYERO: Baƙon Shehu Maghili



Daga: Magaji Galadima

A ranar Litinin 12 ga watan Disamba 2022 gwamnatin ƙasar Aljeriya ta aiko da wani jirgi na musamman domin ya ɗauki mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zuwa ƙasar ta Aljeriya domin halartar taron duniya na musamman don tunawa da rayuwa da kuma aiyukan shahararren malamin addinin Musulunci sharifi kuma masanin falsafa  wato Shehun malami Muhammad Abdurrahman al-Maghili wanda yayi rayuwarsa tun a ƙarni na goma sha biyar. 

Jigin ya tashi daga Kano da karfe 9:45 na safe. A cikin waɗanda suka samu alfarmar raka Sarki wannan tafiya akwai Sarkin Dawakin Tsakar-gidan Kano Alhaji Ahmad Ado Bayero hakimin Kumbotso da Ambasada Ahmad Umar Ɗanmalikin Kano da Dakta Ibrahim Ɗahiru Bauchi wanda ya wakilci Sheikh Ɗahiru Bauchi da Malam Isa Sanusi Bayero da Dakta Lawi Atiku Sanka da kuma ni Magaji Galadima Kachallan Kano, sannan sai wasu malamai da sharifai na Kano da kuma fadawa hadiman Sarki. 

Jirgin ya ɗan yada zango a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar inda ya ɗauki Sultan na Agadas da Sarkin Sharifan ƙasar Nijar da sauran malamai da muƙaddamai da malaman jami’a. Sarkin Kano da ‘yan tawagarsa sun sauka a Aljiyas babban birnin Aljeriya da misalin karfe 5:00 na yamma inda manyan ministoci da jami’an gwamnati dana diflomasiyya da kuma manyan malamai suka taryi mai martaba Sarki da tawagarsa. Daga nan akayi jerin-gwano aka raka Sarki masaukinsa. 

A rana ta biyu wato Talata Sarki da ‘yan tawagarsa suka fita zuwa wajen taron ƙasa da ƙasa da aka shirya domin tunawa da shahararren malamin addinin musulunci masanin falsafa kuma sharifi wato Shehu Muhammad Abdurrahman al-Maghili wanda yayi rayuwarsa tun a ƙarni na sha biyar kuma har yazo Kano zamanin Sarki Muhammadu Rumfa. 

Al-Maghili ya zauna a Kano tsawon lokaci kuma ya bijiro da sababbin tsare-tsare masu muhimmanci a fadar Kano, kana kuma yayi rubuce-rubuce akan ibada da hukunci, sannan ya rubuta wani kundi da ya zama daftari na jagorar duk wani sarki na Kano dama nahiyar yammacin Sudan. 

Taron an shirya shi ne a babban ɗakin taro na ƙasar dake birnin Aljiyes.  A ranar buɗe taron Sarkin Kano da tawagarsa sun isa wajen da misalin karfe 9;00 na safe amma sai aka kaishi wani ɗaki ya zauna a kauwame har sai da ɗakin taron yayi cikar kwari sannan aka shigar dashi.

Toh dama an ɗauki makwanni ana ta yaɗawa a kafafen labarai cewa ƙasar ta Aljeriya zata karɓi bakuncin wani ƙasaitaccen Sarki mai alfarma da daraja daga garin Kano a Nijeriya, don haka mutanen ƙasar duk sun zaku suga wannan ƙasaitaccen Sarki. Saboda da haka yana shiga ɗakin taron sai duk aka tashi tsaye waje ya kaure da sowa da tafi, mata kuma na rabka guɗa, su kuma ‘yan badujala suka goce da wani irin take na musamman da ake kaɗawa mashahuran mutane in sun shigo wajen taro.

An ɗauki tsawon lokaci kafin a samu natsuwa lamurra su koma daidai sannan mai martaba Sarkin Kano figinai suka yi sayi ya zauna aka gyara aka kimtsa sannan aka fara gudanar da taro. 

Daga nan ne kuma sai aka fara jawabai, babban ministan harkokin addini na ƙasar shine ya wakilci shugaban ƙasa kuma yayi jawabin maraba ga mahalarta taron kana yayi godiya ta musamman ga Sarki Aminu Bayero a madadin shugaban ƙasa da al’ummar ƙasar baki ɗaya. Shima Sarkin na Kano  yayi jawabi inda ya nuna farin ciki da godiya ga gwamnati da jama’ar ƙasar baki ɗaya saboda kyakkawar taryar da aka yi masa, ya kuma isar da gaisuwar jama’ar masarautar Kano da Nijeriya baki ɗaya a garesu. 

Sarkin ya yaba da hangen nesan waɗanda suka assasa wannan taro na tunawa da Shehu Maghili wanda yace yafi cancanta a kira shi da Bakano maimakon dan Aljeriya saboda da dalilai da dama. Ya baiyanawa mahalarta taron cewa a yanzu haka a cikin birnin Kano akwai unguwar Sharifai waɗanda asali jama’ar da suka zo Kano tare da Shehu Maghili sune ke zaune…



Sunday, 25 December 2022

Mutane sama da 20 ne suka mutu saboda tsananin sanyi a Amurka

 


Fiye da Amurkawa 200,000 ne suka wayi gari ba tare da wutar lantarki ba a safiyar ranar Kirsimeti sakamakon guguwar sanyi da ta shafe kwanaki ana tafkawa a wasu jihohin gabashin Amurka, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 20


Matsanancin sanyi, dauke da guguwa mai cike da tarihi ya mamaye  jihohin Amurka 48 a wannan makon, abin da ya haifar da cikas ga matafiya da dakatar da zirga-zirgar dubban jirage, inda dubban gidaje ke cike da dusar kankara.

An tabbatar da mutuwar mutane 22 a jihohi takwas, ciki har da akalla mutane bakwai da suka mutu a yammacin New York, inda dusar kankara dauke iska mai tsanani suka mamaye garuruwa.

Shugaban gundumar Mark Poloncarz ya shaida wa manema labarai cewa, "Muna da mutane bakwai da aka tabbatar sun mutu sakamakon guguwar da ta afku a gundumar Erie.

Wasu ma'aurata a Buffalo, wanda ke kan iyaka daga Canada, sun shaidawa AFP cewa tsananin sanyi ba zai basu damar tafiyar tsawon minti 10 ba na ziyartar danginsu a bikin Kirsimeti.

Haka zalika matafiya sun kasance a makale a filayen jirgin saman a Atlanta, Chicago, Denver, Detroit, Minneapolis da New York.

Kankara da ta mamaye kan titi ta haifar da rufe wasu hanyoyin zirga-zirgar ababen hawa na wucin gadi da suka hada da ta Interstate 70.

Hukumomin kasar dai sun gargadi direbobi da kada su bi hanyoyin daidai lokacin da al’ummar kasar kan ganiyar zirga-zirga saboda bukukuwan Kirismeti.

Dalilin Da Zan Koma Daura Idan Na Bar Mulki —Buhari


Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ce zai koma Daura da zarar ya kammala wa’adin mulkisa don guje wa matsaloli.

Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Lahadi lokacin da ya karbi bakuncin mazauna Babban Birnin Tarayya don ta su murnar bikin Kirsimeti.

Kazalika, Buhari ya gode wa ’yan Najeriya da suka yarda tare da amince masa ya shugabance su.

Ya ce duk da ci gaba da aka samu a fasaha da kimiyya, hankalinsa zai fi kwanciya idan ya koma garinsa.

Buhari dai ya jima da cewa da zarar ya kammala wa’adin mulkinsa zai bar Abuja gaba daya, don kauce wa shiga sabgogin gwamnatin da za ta gaje shi.

'Ya'yana biyu ne suka rasu saboda cutar Sikila - Buhari


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce 'yayansa biyu ne suka rasu sakamakon cutar Sikila.

Buhari ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a wajen wani gagarumin taro da 'yan uwa da abokan arziki suka shirya masa kan bikin cikarsa shekara 80 da haihuwa a fadarsa.

Yayin da yake jawabi game da rayuwarsa shugaba Buhari ya ce 'ya'yansa biyu ne - da ya haifa tare da matarsa ta farko mai suna Safinatu - suka rasu sakamakon cutar Sikila.

Ya ƙara da cewa hakan ya tilasta masa yin gwajin ƙwayoyin halitta a lokacin da ya tashi auren matarsa ta yanzu Aisha Buhari.

Ya ce ya dage cewa dole sai matar da zai aura ta kasance tana da ƙwayoyin halitta na AA, don kauce wa ɗaukar cutar Sikila ga 'yayan da zai haifa kasancewar shi yana da ƙwayoyin halitta na AS.

Buhari ya auri Safinatu a shekarar 1971. sun kuma haifi 'ya'ya biyar tare da ita.

EFCC Ta Yi Gwanjon Kadarorin Su Diezani A Kasuwa


Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta sanar da yin gwanjon wasu kadarorin da ta kwace daga hannun ’yan siyasa da ’yan kasuwa ga ’yan Najeriya masu bukatar saya.

Hukumar ta ce kadarorin dai na jibge ne a Jihohin Legas da Ribas da Abuja da Anambra da Gombe da Ebonyi da Kaduna da Delta da Edo daKwara da Kuros Riba da Osun da kuma Oyo.

Aminiya ta gano cewa daga cikin kadarorin har da na tsohuwar Ministar Man Fetur ta Najeriya, Diezani Allison-Madueke, wadanda hukumar ta ce an mallake su ta haramtacciyar hanya.

A wata sanarwar da hukumar ta wallafa ranar Asabar, EFCC ta ce daidaikun mutane da kuma kamfanoni da kungiyoyin da ke son sayen kayan da aka yi gwanjon dole ne su kasance ba a taba daure su ba a baya.

Kadarorin da aka yi gwanjon nasu sun hada da wani gida a rukunin gidaje na Heritage Court a Jihar Ribas da wani mai daki uku a rukunin gidaje da ke rukunin gidaje na Foreshore a unguwar Ekoyin Jihar Legas fa sauran su.

’Yan Najeriya Na Kushe Ni Duk Kokarina —Buhari

 

’Yan Najeriya Na Kushe Ni Duk Kokarina —Buhari


Shugaba Buhari ya ce ba zai yi kewar shugabancin Najeriya ba saboda kushe shi da ’yan kasar ke yi duk kokarinsa.

Buhari ya bayyana hakan ne a liyafar da ’yan uwa da abokan arziki suka sirya masa don taya shi murnar cikarsa shekaru 80 da haihuwa a Abuja, inda ya ce ’yan Najeriya na raina duk fadi tashin da yake kan kasar, don haka ba zai yi kewar mulkar ta ba idan wa’adin mulkinsa ya cika.

“Abubuwan da zan yi kewar su a matsayina na shugaban kasa a gwamnatance ba su da yawa, saboda raina kokarina da ’yan Najeriya ke yi a kodayaushe.

“Ina iya bakin kokarina, amma wasu na ganin za su iya tsoratar da ni don su samu yadda suke so,” in ji shi.

Da yake amsa tambayar ’yan jarida kan jita-jtar da ake yadawa cewa ba shi ne Buharin da ’yan kasar suka sani a baya ba, Buhari ya ce yana sane da hakan, sai dai sanin cewa ’yan Najeriya mutane ne masu son raha ya sa bai damu ba.

Ya ce wannan batu ba abin dariya ba ne saboda wasu ne ke kokarin amfani da hakan don kau da hankalin ’yan Najeriya daga kan abubuwan da suke da muhimmaci.

#hajj2023 Hukumar alhazai ta Kano, ta yi kira ga duk mai niyyar zuwa Hajin bana, da ya gaggauta biya


 

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Gov. Yusuf Commissions 10km Roads in Sumaila, Wudil to Boost Connectivity, Security

Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, has commissioned 10 kilometres of newly completed roads in Sumaila and Wudil Local...